Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuMun karkata Naira Tiriliyan 4 na tallafin fetur zuwa ga ayyukan raya...

Mun karkata Naira Tiriliyan 4 na tallafin fetur zuwa ga ayyukan raya kasa – Shugaba Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da isasshen kudade ga muhimman bangarorin bunkasa tattalin arzikin kasa, domin kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wajen bude taron kasa kan asusun jama’a da tsarin kashe kudade, wanda kwamitocin kula da kudade da al’umma na Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka shirya.

Da take wakiltar shugaban kasa, karamar ministar kudi Doris Uzoka-Anite, ta ce cire tallafin man fetur, duk da cewa abi ne mai radadi amma ya bai wa gwamnati damar karkata kudaden zuwa inganta sufuri, kafa sabbin tsare-tsaren jin kai, da kuma gina muhimman ababen more rayuwa da za su amfani ‘yan Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata