Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuMun nemi INEC ta yi wa Tafiyar Matasa rijista a matsayin jam'iyyar...

Mun nemi INEC ta yi wa Tafiyar Matasa rijista a matsayin jam’iyyar siyasa da sunan “Access Party” – Bulama Bukarti

Jagoran Tafiyar Matasa, Barista Audu Bulama Bukarti, ya bayyana cewa sun mika bukatar yi wa tafiyar matasa rajista a matsayin jam’iyyar siyasa da sunan “Access Party”.

Barr Bulama Bukarti ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce sun nemi rejista da sunan Access Party ne saboda sauƙin shi da kuma ma’anarsa na bawa nagartattun matasa sabbin jini dama su kawo sabbin manufofi a tsarin siyasa da mulkin Nijeriya.

 

Bulama ya ce manufarsu ita ce bai wa waɗanda suka dace da jagoranci al’umma damar shigowa su kawo gyara a ƙasarsu,saboda haka Access Party ita ce jam’iyar Tafiyar Matasa, kuma kirarinta a Arewa zai ci gaba da zama haka, a kudancin Nijeriya kuma a kirata “Na Our Waka. Na Our Mata”.

Ya kara da cewa akwai karin bayani game da halinda suke ciki da hukumar zabe ta kasa INEC amma zuwa nan gaba za su bayyana halin da ake ciki.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata