Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuMuna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 - Kashim...

Muna kokarin bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya ce gwamnatin kasar na kan hanyar bunkasa tattalin arzikin Nijeriya zuwa dala tiriliyan 1 cikin shekaru goma masu zuwa.

Kashim Shettima ya ce don cimma wannan buri ana da bukatar haɗin gwiwa da ƙwararrun da za su iya jagorantar lamarin.

Ya yi wannan magana ne a birnin Legas a yayin taron da Africa and Middle Depositors Association (AMEDA) da Central Securities Clearing System (CSCS) Plc ne suka shirya.

A jawabinsa, Shettima ya jaddada kudirin gwamnatin na karfafa tsarin hada-hadar kudi a Nijeriya ta hanyar bin tsari da gyara dabarun bunkasa kasuwannin, da kuma hadakar gwamnati da masu masana’antu masu zaman kansu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata