Mune muka yi Muslim/Muslim don haka dole mu fito mu caccaki gwamnati kan gazawarta – Sheikh Abubakar Salihu Zaria
Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Abubakar Salihu Zaria ya caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan matsalolin tattalin arziki da suka addabi kasar nan.
Bayanin malamin ya fito ne a wani faifan bidiyo da a kan shafin X da sauran kafafen sada zumunta a ranar Lahadi.
Sheikh Abubakar ya bayyana cewa shi da sauran musulmi sun goyi bayan Tinubu tare da yi masa kamfen a zaben 2023, suna ganin zai inganta al’amuran kasar, amma abin ya ci tura.
Ya bayyana cewa gazawar shugaban kasar na magance matsalolin kasar ya sa ake ta yi musu gori a cikin al’umma.
Yace duk da kokarin da suka yi na sanar da shugaban kasar matsalolin da kasar ke ciki, har da yin magana da shi da yaren sa, amma anyi watsi dashi.
Malamin ya koka da cewa, suna tsammanin tikitin tikitin musulmi da musulmi zai amfanar da addinin musulunci, amma a maimakon haka, shugaban ya yi watsi da matsalolinsu da na al’umma gaba daya.
Malamin ya koka da cewa, maimakon a ci gaba, Nijeriya na ci gaba da komawa baya, yana mai kira ga shugaban kasar da ya duba lamarin.

