Rahoton Pew Research Centre ya bayyana Musulunci a matsayin addini mafi saurin ƙaruwa a duniya tsakanin 2010 zuwa 2020, saboda yawan haihuwa da ƙarancin shekaru a tsakanin Musulmai.
Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya ce mace Musulma tana haifar yara 2.9 a rayuwarta, idan aka kwatanta da 2.2 ga wadanda ba Musulmai ba.
Yayin da Kiristanci ke da mabiya biliyan 2.3, adadin mabiya Musulunci na ƙara karatowa da rage gibin.
A cewar binciken, Kiristanci ya ragu da kashi 1.8%, yayin da yawancin sauyin addini daga sauran addinai ke komawa Musulunci.
Haɓakar ta fi a ƙasashen Musulmi, yayin da marasa addini suka fi yawa a ƙasar Sin.
