Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuNacin ciyo bashi da gwamnatin Tinubu ke yi hadari ne ga goben...

Nacin ciyo bashi da gwamnatin Tinubu ke yi hadari ne ga goben Nijeriya – Atiku Abubakar

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Tinubu da yawan karbar bashi, yana mai cewa hakan barazana ce ga makomar kasar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya bayyana sabuwar bukatar bashin dala biliyan 21.5, da Yuro biliyan 2.19, da Yeng biliyan 15 da kuma tallafin Yuro miliyan 65 a matsayin “cin amanar tattalin arziki.”

Ya ce bashin Najeriya na iya kaiwa Naira tiriliyan 183 daga Naira tiriliyan 144.7 da aka ruwaito a karshen 2024, yana mai zargin gwamnati da amfani da bashi wajen biyan bashi maimakon ci gaban kasa.

Atiku ya bukaci majalisa, kungiyoyin farar hula, kafofin watsa labarai da kasa da kasa su dakatar da shirin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata