![]() |
| Hannatu Musawa |
Ministar Al’adu, Hannatu Musa Musawa ta bayyana cewa bata aikata wani abu da ya saba wa doka ba ta hanyar karɓar nadin minista yayin da take gudanar da wajibcin shekara ɗaya na yi wa kasa hidima wato (NYSC).
Hakan ya biyo bayan ganowar da Ƙungiyar rubuce rubuce kan dokokin kare hakkin Dan Adam (HURIWA) tayi na cewa Musawa tana yiwa ƙasa hidima a wani wuri a Abuja.
A wancan lokacin, Emeka Megwa, Daraktan yada laabarai da hulɗa da Jama’a na NYSC, ya bayyana cewa rike matsayin minista yayin gudanar da hidimar ƙasa yana nufin keta dokar hukumar kula da masu yi wa kasa hidima
A wata tattaunawa da Daily Trust, Megwa ya bayyana cewa duk wani ɗan bautar ƙasa da ya karɓi kowanne naɗin mukami na gwamnati kafin kamalla hidimar kasa ya sabawa dokar hukumar kula da masu yi wa kasa hidima ta NYSC.

