Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuNajeriya ba za ta karɓi fursunonin Venezuela daga Amurka ba – Minista...

Najeriya ba za ta karɓi fursunonin Venezuela daga Amurka ba – Minista Tuggar

Ministan harkokin waje na Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta ƙi amincewa da matsin lambar da Amurka ke yi mata da wasu ƙasashen Afirka domin su karɓi ’yan Venezuela da za a koro su daga Amurka, ciki har da waɗanda aka fito da su daga gidajen yari.

Tuggar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV, inda ya ce karɓar waɗannan fursunonin zai yi wa Najeriya wuya saboda matsalolin cikin gida da ƙasar ke fuskanta.

Ya ce Najeriya ba za ta iya ɗaukar nauyin ’yan Venezuela ba, musamman ma waɗanda ke da laifuka.

Rohoton jaridar Premium Times ya ruwaito ministan na danganta harajin kashi 10% da gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump, ta kakaba wa kayan da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka a matsayin martani ga ƙin karɓar waɗannan fursunoni, ba wai saboda halartar taron BRICS da Tinubu ya yi ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata