Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da zargin mayar da Nijeriya ta zama kasa mai jam’iyya daya a karkashinsa.
A yayin da yake jawabi a zaman hadin guiwa na majalisar dokokin kasar kan bikin ranar dimokuradiyya da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja, Tinubu, ya ce ba zai shawarci jam’iyyun adawa da su magance rikicin gidajensu ba.
Tinubu ya kuma ce jam’iyyar APC ba za ta hana ‘yan adawa su shigo cikinta ba, yin hakan kamar gurbata siyasar ne.
