Karamin ministan ayyuka Bello Goronyo, ya bayyana cewa nasarorin da shugaba Bola Tinubu ya samu a cikin shekaru biyu kacal a kan karagar mulki sun zarce na tsawon shekaru goma.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Sokoto, Goronyo ya jaddada cewa, Tinubu ya jajirce kan sake fasalin Nijeriya domin biyan bukatun dukkan ‘yan kasar.
A cewarsa Shugaba Tinubu ya gargadi dukkan ministocinsa cewa suyi aiki tukuru da sadaukarwa domin kare makomar Nijeriya wanda hakan ya yi tasiri sosai wajen samun ci gaba fiye da na shekaru goma.

Cigaban mai Gina Rijiy ke nan Goronyo? Domin mu Talakawan Nigeria babu wani Cigaba da muka samu a mulkin APC illa Mugun Talauci, Uquba da kuma Azaba Wallahi. Kuma Wallahi kusani ba zamu Taba Yafe muku ba