Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedNijar na shirin gina wata sabuwar matatar mai a jihar Dosso

Nijar na shirin gina wata sabuwar matatar mai a jihar Dosso

 

Wata tawagar hadin gwiwar wasu ma’aikatun Nijar karkashin jagorancin sabon ministan mai, ta kai ziyarar aiki domin gani da ido na wurin da za’a gina sabon kamfanin matatar mai a cikin jihar Dosso.

Ana sa ran sabuwar matatar man za ta rika tace ganga dubu 30 a ko wace rana a tashin farko kafin daga bisani a fadada zuwa dubu 100 a kowace ranar.

Ko baya ga matatar man ma akwai kuma babban cibiyar samar da wutar lantarki a jihohin Tillaberi Dosso da babban birnin Yamai domin rage dogaro da na ketare inji hukumomin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata