Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuNijeriya ce kasa ta 36 a jerin kasashen da suka fi cin...

Nijeriya ce kasa ta 36 a jerin kasashen da suka fi cin hanci a duniya – Bincike

Kungiyar Transparency International (TI) ta sake sanya Nijeriya a matsayi na 36 cikin kasashen da suka fi cin hanci a duniya a shekarar 2025, a cewar rahoton Corruption Perceptions Index (CPI) da aka fitar ranar Talata.

Rahoton ya nuna cewa Nijeriya ta fadi daga matsayi na 140 a 2024 zuwa 142 cikin kasashe 182 da aka tantance, inda maki 0 ke nuna mafi muni wajen cin hanci, yayin da 100 ke nuni da mafi tsabta.

Nijeriya ta samu makin 26, inda ta yi kunnen doki da kasashe irin su Cameroon, Guatemala, Guinea, Kyrgyzstan da Papua New Guinea.

Duk da faduwar matsayin, Nijeriya ta ci gaba da kasancewa a matsayin kasa ta 36 mafi cin hanci, kamar yadda ta kasance a shekarar da ta gabata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata