Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuNijeriya na dab da zama ta uku mafi ƙarfin tattalin arziki a...

Nijeriya na dab da zama ta uku mafi ƙarfin tattalin arziki a Afrika – Hasashen hukumar NOA

By Salisu Ado Sulaiman

Hukumar wayar da kan al’umma ta Najeriya NOA ta yi hasashen cewa kasar na dab da wuce kasar Algeria wajen zama ta uku mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka a 2025 da muke ciki.

Hukumar ta NOA, wacce ministan yada labaran Najeriya Alhaji Muhammad Idris ke jagoranta, ta nuna cewa kasar ta samu bunkasar tattalin arziki da kaso 38 bisa ma’aunin GDP, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wani rahoton mako da hukumar ta wallafa, ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya ya kai Naira Tiriliyan 372.8 bisa ma’aunin GDP, daga shekarar 2019 zuwa 2024.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata