Friday, April 10, 2026
HomeBabban LabarinmuNijeriya ta kara yawan fasfon da take iya bugawa a rana zuwa...

Nijeriya ta kara yawan fasfon da take iya bugawa a rana zuwa 5,000 – Tunji Ojo

Rahoton gidan talabijin na Channels ya Ambato ministan cikin gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Hukumar shige da fice ta Najeriya (NIS) yanzu tana iya samar da fasfo tsakanin 4,000 zuwa 5,000 cikin awa biyar karo na farko cikin shekaru 62.

Tunji-Ojo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, bayan ya duba sabuwar cibiyar samar da fasfo da aka gina a hedikwatar hukumar shige da fice ta Nijeriya da ke Abuja.

A cewar sa, sabuwar fasahar ta baiwa hukumar damar yin fiye da fasfo 1,000 a cikin awa guda, alhali a da hukumar tana iya yin tsakanin fasfo 250 zuwa 300, ne a rana kacal.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata