Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiNiMet ta yi hasashen ruwan sama da ambaliya a sassa daban-daban na...

NiMet ta yi hasashen ruwan sama da ambaliya a sassa daban-daban na Nijeriya

Hukumar NiMet ta bayyana cewa daga Litinin zuwa Laraba, za a samu guguwa da ruwan sama mai karfi a sassa da dama na Najeriya tare da yiwuwar ambaliya, musamman a Arewacin ƙasar.

A safiyar Litinin, za a samu ruwan sama mai karfi a Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe da Katsina, yayin da sauran jihohin Arewa za su fuskanci rana da dan hadari. Da yamma kuma, ana hasashen ya nuna za’a samu ruwan sama a Kebbi, Adamawa da Taraba.

A Talata da Laraba, hukumar ta yi hasashen ruwan sama da guguwa za su yawaita a jihohin Arewa da Kudu, ciki har da Kano, Katsina, Sokoto, Adamawa da Akwa Ibom, yayin da NiMet ke gargadin ambaliya a wasu sassan kudancin kasar.

Hukumar ta bukaci al’umma da su dauki matakan kariya da kuma gujewa wuraren da ruwa ke taruwa kamar yadda jaridar Daily Trsut ta tattaro.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata