Kungiyar ƙwadago a Nijeriya NLC, ta umarci ma’aikata a jihohin da ba su aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi ba, su gudanar da bikin May Day na 2026 a kan tituna maimakon wuraren taro na gwamnati.
A cikin wata sanarwa da Sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja ya fitar, ya zargi wasu gwamnatocin jihohi da karya dokar sabon valbashi ta 2024, musamman wajen rashin biyan cikakken albashi, rashin gyara albashin manyan ma’aikata da kuma kin shigar da ma’aikatan kananan hukumomi, malamai da ma’aikatan lafiya cikin tsarin.
Kungiyar ta bayyana cewa irin wannan mataki na jihohi cin zarafi ne ga hakkin ma’aikata, tare da cewa dokar albashi da Shugaba Bola Tinubu ya rattaba wa hannu wacce ta sauya albashi daga naira 30,000 zuwa 70,000 ba ta samu cikakken aiwatarwa ba a wurare da dama.
NLC ta bukaci ma’aikata su taru daga karfe 7 na safe a ranar 1 ga watan Mayu su fito zanga-zanga cikin lumana a manyan biranen jihohi, inda za su kai korafe-korafensu ga gwamnati, tana mai cewa rashin yin hakan zai zama kamar cin amanar gwagwarmayar ma’aikata.
