Wednesday, April 8, 2026
HomeBabban LabarinmuNNPCL ta ninka yawan danyen mai da take ba matatar Dangote

NNPCL ta ninka yawan danyen mai da take ba matatar Dangote

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya sanar da ninka yawan danyen mai da yake kai wa Matatar Man Dangote zuwa jirage 10 a watan Maris, abin da masana ke ganin zai iya kawo sauƙin farashin man fetur a ƙasar.

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa matatar ta karɓi jirage 10 na danyen mai daga NNPC a watan Maris, sabanin kusan jirage biyar da ake samu a baya.

Jaridar Punch ta ambato ya ce daga cikin wannan adadi, jirage shida an biya su da naira, yayin da huɗu aka biya su da dala, a ƙarƙashin yarjejeniyar samar da danyen mai tsakanin ɓangarorin biyu.

Ƙarin samar da danyen man ya zo ne a lokacin da ake fama da tangarda a kasuwannin mai na duniya, sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, ciki har da rikicin da ya shafi Iran.

Masana harkar mai sun ce wannan mataki na iya taimakawa wajen rage farashin man fetur a Najeriya, amma sun jaddada cewa hakan zai tabbata ne kawai idan gwamnati ta rage farashin danyen mai da take sayar wa matatar Dangote.

Duk da haka, Aliko Dangote ya bayyana cewa har yanzu matatar ba ta kai cikakken ƙarfin aiki ba, domin tana buƙatar kusan jirage 19 na danyen mai a kowane wata domin yin aiki yadda ya kamata.

Ya kuma ƙara da cewa matatar na ci gaba da shigo da danyen mai daga ƙasashen waje kamar United States da wasu ƙasashen Afirka, saboda ƙarancin wadatar mai daga cikin gida.

Dangote ya yi korafi kan yadda wasu kamfanonin mai na ƙasashen waje ke fifita sayar da danyen mai ga ‘yan kasuwa na waje maimakon kai tsaye ga matatar, lamarin da ke sa su sake sayen man nasu a farashi mai tsada.

A gefe guda kuma, matatar ta fitar da jirage 17 na kayayyakin man fetur zuwa wasu ƙasashen Afirka a watan Maris, abin da ke nuna muhimmancinta a matsayin babbar mai samar da man fetur a nahiyar.

Ana sa ran wannan ci gaba zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da man fetur daga waje, tare da daidaita farashi a kasuwar cikin gida idan aka ci gaba da wannan tsari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata