Jam’iyyun NNPP da APC sun yi watsi da zargin da wasu ‘yan majalisar Amurka suka yi kan tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kungiyar makiyaya da Miyetti Allah da kuma Miyetti Allah Kautal Hore, na cewa suna tauye ‘yancin addini a Nijeriya.
‘Yan majalisar dai sun gabatar da wani kuduri da ke bukatar a kwace kadarorin wadanda suka zarga, tare da hana su bizar shiga Amurka.
Sai dai APC ta ce zargi kawai bai isa hujjar hana Kwankwaso morar ‘yancinsa na yawo ba, kana babu cikakken bincike tare da bin tsarin da ya dace kan lamarin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ita kuwa jam’iyyar NNPP, yayin wani taron manema labarai a Abuja, bayyana lamarin ta yi a matsayin bi-ta-da-kulli kawai.
