Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaObi ba ya bukatar hadaka da PDP ko kawance da Atiku don...

Obi ba ya bukatar hadaka da PDP ko kawance da Atiku don kayar da Tinubu – NLC

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, baya bukatar haɗin kan jam’iyyar PDP ko wasu jiga-jigan siyasa irinsu Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Nasiru El-rufa’I domin samun nasara a zaben 2027.

Wannan jawabi ya fito daga bakin Mataimakin shugaban kungiyar ta ƙasa, Farfesa Theophilus Ndubuaku, a wata hira ta musamman. Ya ce Peter Obi na da farin jini a tsakanin al’umma, kuma shi ne mutum mafi cancanta da zai iya gaba-da gaba a kokarin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaben da ke tafe.

Farfesa Ndubuaku ya kuma ƙaryata jita-jitar da ke yawo kan cewa Peter Obi zai koma jam’iyyar PDP, yana mai cewa PDP ta zama jam’iyyar da ke cike da rikice-rikice da rudani a kan sahihancin manufarta.

Ya jaddada cewa Peter Obi da jam’iyyar Labour za su tsaya tsayin daka wajen gina sabon tsari mai inganci a siyasar Najeriya, ba tare da dogaro da tsofaffin tsari na raunanan jam’iyyu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata