Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 10

An nada DCP Anthony Okon mukamin sabon kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya IGP Olatunji Rilwan Disu ya amince da nadin DCP Anthony Okon Placid a matsayin sabon kakakin rundunar ‘yansandan Nijeriya

DCP Placid, wanda aka haifa a Uyo, jihar Akwa Ibom, yana da gogewa sosai a fannonin shugabanci, ayyukan runduna, leken asiri, horo, da aikin wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa.

Ya karanci Geography da Regional Planning a jami’ar Uyo, sannan ya samu digiri na biyu a Law and Diplomacy (M.A.L.D) a jami’ar Jos, kuma ya yi karatun Shari’a a jami’ar NOUN ta Nijeriya.

Peter Obi ya yi rajistar shiga jam’iyyar ADC a hukumance

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi ya yi rajista a ADC a ranar Asabar, inda ya jaddada cewa zaɓen 2027 zai kasance tsakanin ‘yan Najeriya da shugabanci mara inganci.

Obi ya ce yankin Kudu maso Gabas na da hakkin samun shugaban kasa, yana mai cewa babu wani yanki da ya fi shi a Najeriya.

Ya kuma jaddada bukatar fitar da ‘yan Najeriya daga talauci don rage rashin tsaro, tare da karfafa masu rajista su yi kokarin jawo sabbin mambobi zuwa ADC.

A wannan rana, Senator Victor Umeh da tsohon dan majalisa Ben Obi ma sun kammala rajista a jam’iyyar a kananan hukumomin Agulu da Awka, Anaocha da Awka South.

Akwai yiyuwar mutum 2 sun rasa rayukansu a rikicin kabilanci a jihar Adamawa

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa mutum biyu sun rasa rayukansu a sabon rikicin da ya tashi tsakanin al’ummomin Chobo da Bachaman a karamar hukumar Lamurde, ta jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar, Suleiman Yahaya-Nguroje, ya ce rikicin ya barke ne a daren Asabar bayan wasu matasan Chobo sun farmaki garin Lamurde, inda suka yi harbi, abin da ya sa matasan Bachaman suka yi ramuwar gayya.

Jaridar Punch ta ruwaito an tura jami’an ‘yan sanda domin dawo da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da tattara rahotannin hasarar rayuka.

Wannan rikici wanda ya samo asali ne a kan rikicin kasa a yankin, wanda a cikin watanni shida da suka gabata ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 30, musamman mata.

Da izinin Abba aka fitar da kudaden da ake tuhumar mataimakin gwamna – Kwankwasiyya

Ƙungiyar Kwankwasiyya a Kano ta musanta zargin almundahana na naira biliyan 1.1 da ake yi wa Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo, inda ta gabatar da takardu da ke nuna an saki kudin ne da izinin Governor Abba Yusuf.

Rahoton ya nuna cewa takardun daga watan Afrilu zuwa Yuni 2024 sun bayyana cewa an tsara rabon kudin N25m ga kowace karamar hukuma domin samar da ruwa da magunguna, wanda ya kai jimillar N1.1bn ga kananan hukumomi 44.

Jaridar Daily Trust ta ambato, shugabannin Kwankwasiyya sun ce wannan na nuna cewa Gwarzo ya yi aiki ne bisa doka da izinin gwamna, suna kalubalantar zargin majalisar dokoki a matsayin wani mataki na siyasa.

Majalisar jihar ta ba Gwarzo makonni biyu domin ya mayar da martani kafin a kafa kwamitin bincike kan tuhume-tuhumen da ake a kansa.

Za mu kawo karshen rashin tsaro a Nijeriya – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya da rundunar sojin kasar cewa gwamnati za ta yi nasara kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar.

Jaridar Daily Nigerian ta ambato Tinubu ya bayyana haka ne yayin buda baki da sojoji a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda ya yaba wa jarumtaka da sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi wajen kare kasar daga ‘yan ta’adda.

Ya kuma jaddada kudurin gwamnatinsa na kara zuba yin abin da ya dace wajen samar da kayan aiki, bayanan sirri da tallafin aiki domin kara inganta ayyukan rundunar.

Kamfanonin rarraba wutar lantarki na Nijeriya sun samu riba sosai — NERC

Hukumar da ke lura da harkokin wutar lantarki ta Nijeriya NERC ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) sun tara Naira biliyan 207.49 daga kudin wutar lantarki a watan Disambar 2025.

A rahoton da hukumar ta fitar a Abuja, ta ce kamfanoni 11 sun caji kwastomomi naira biliyan 258.66, amma an samu gibin kudin shiga na naira biliyan 51.17.

Rahoton ya nuna ingancin karbar kudade da kashi 80.22 cikin dari, yayin da Abuja Electricity Distribution Company, Ikeja Electric da Eko Electricity Distribution Company suka fi samun kudin shiga a watan.

Hukumar tsaron Civil Defence za ta tura dakaru 11,000 da za su kare manoma a gonaki

Hukumar tsaron Civil Defence (NSCDC) ta bayyana shirin tura jami’an ta na Agro-Rangers sama da dubu goma sha daya domin kare manoma a fadin Najeriya yayin da ake shirin fara kakar noma ta shekarar 2026.

Mai magana da yawun hukumar, Babawale Afolabi, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Sunday Punch, inda ya ce hukumar na daukar matakai masu karfi domin tabbatar da tsaron manoma da kuma kare harkokin noma a kasar.

A cewarsa, shugaban hukumar NSCDC, Abubakar Audi, ya sake jaddada kudurin hukumar na tura jami’an da aka horar musamman zuwa wuraren noma domin kare rayukan manoma da dukiyar da ta shafi noma.

Matakin na zuwa ne bayan jerin hare-hare da suka faru kan manoma a wasu sassan Najeriya a shekarar 2025.

An yi hasashen samun hazo na kwanaki 3 a wasu wurare a sassan Nijeriya – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet, ta yi hasashen cewa a wasu sassan kasar za a fuskanci yanayin hazo na kwanaki uku a fadin Nijeriya.

A cewar hukumar, ana sa ran hazo da kura mai zai mamaye yawancin yankin Arewa ta Tsakiya a cikin wannan lokaci.

NiMet ta kuma bayyana cewa a yankin kudancin kasar za a samu rana tare da gajimare kadan, amma akwai yiwuwar samun tsawa da ruwan sama mai da yamma ko dare a wasu jihohin.

Farashin abinci ya ragu da kashi 50% cikin 100 sakamakon gyare gyaren tattalin arziƙi – Ministan Tinubu

Ministan noma na Nijeriya, Abubakar Kyari, ya ce farashin kayayyakin abinci a fadin kasar ya ragu zuwa kashi 50 cikin 100, sakamakon gyare-gyaren da gwamnatin shugaba Tinubu ta aiwatar.

Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da gwamnati ke yi don wayar da kan ‘yan kasa a Abuja ranar Juma’a, inda ya ce gwamnati ta bai wa batun tsaron abinci muhimmanci domin tabbatar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki.

A cewarsa, gwamnati na kokarin kara yawan noman cikin gida tare da rage dogaro da shigo da abinci daga kasashen waje, domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya na samun abinci mai gina jiki cikin sauki.

Farashin man fetur ya haura zuwa ₦1,080 kan kowace lita a Legas

Farashin man fetur ya kai kusan ₦1,080 kan kowace lita a wasu sassan birnin Legas, sakamakon tashin farashin mai a kasuwar duniya da rikicin da ke kara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa binciken da aka gudanar a gidajen mai da dama a Legas ranar Asabar din nan ya nuna farashin fetur, yanzu yana tsakanin ₦1,020 zuwa ₦1,080 kan kowace lita, gwargwadon wurin da tashar mai take.

Rahoton ya ce karin farashin ya biyo bayan karin kudin da matatar Dangote ta sanya wa fetur ga ‘yan kasuwa, inda aka kara shi zuwa ₦995 kan kowace lita daga ₦874 saboda tashin farashin danyen mai a kasuwar duniya.