Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 11

Guinea ta soke rajistar jam’iyyu 40 ciki har da babbar jam’iyyar adawa a ƙasar

Gwamnatin Guinea ta soke rijistar jam’iyyun siyasa 40, ciki har da manyan jam’iyyun adawa guda uku, ta hanyar wata doka da aka fitar da dare.

Matakin ya zo ne kasa da watanni biyu bayan rantsar da shugaban kasar Mamady Doumbouya tsohon shugaban mulkin soja bayan zaben da aka yi a karshen 2025.

Gwamnatin ta ce an rusa jam’iyyun ne saboda sun gaza cika wasu sharudda na doka.

Nijar na shirin fara amfani da sabon Fesfo mai tambarin AES

Wani kamfani mai suna Al Itisal Al Jadeed da ke kasar Libiya ne ma’aikatar cikin gidan Nijar ta bai wa kwangilar buga sabon Fesfo ɗin tare da katin shaidar zama ɗan kasa ta kasashen kungiyar AES.

Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso dai da ke karkashin kungiyar ta AES tun bayan ficewar su daga kungiyar ECOWAS ne suka sanar da samarwa kansu takardar fesfo din kasashen.

Sai dai har kawo yanzu kasar Nijar na amfani da tsohon sanfarin fesfon mai dauke da tambarin kungiyar ECOWAS.

Gwamnatin Tinubu ta tafka kuskure wajen rabon muƙaman Jakadun Nijeriya – ADC

Jam’iyyar ADC mai adawa a Nijeriya ta soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan sanar da rabon mukaman jakadu zuwa ƙasashen waje, tana mai cewa matakin kuskure ne na diflomasiyya kuma wata alama ce ta rashin kwarewar gwamnati.

A cikin wata sanarwa da Mallam Bolaji Abdullahi, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, ya fitar, ADC ta ce sanar da mukaman jakadu kafin samun amincewar ƙasashen da za su karɓe su na iya jefa Nijeriya cikin kunyatar diflomasiyya.

Jam’iyyar ta bayyana cewa a ƙarƙashin yarjejeniyar Vienna kan hulɗar diflomasiyya, musamman sashe na 4, dole ne ƙasar da ke aikawa da jakada ta fara neman amincewar ƙasar da za ta karɓe shi kafin sanar da nadin a hukumance.

Ta ce sanar da nadin jakadu sannan a ce ana neman wannan amincewa yana nuna gwamnati ba ta fahimci muhimman ƙa’idojin diflomasiyya ba.

Ana hasashen ministocin Tinubu 4 za su ajiye aiki don neman wasu mukamai a 2027 – Jaridar Punch

Rahotanni na nuna cewa akalla ministoci hudu a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na shirin ajiye mukamansu domin neman wasu mukaman siyasa a jihohinsu gabanin babban zaben 2027.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa daga cikin ministocin da ake zargin suna da wannan buri akwai ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu, ministan lafiya Muhammad Ali Pate, ministan harkokin waje Yusuf Maitama Tuggar, da kuma karamin ministan kwadago Nkeiruka Onyejeocha.

Bincike ya nuna cewa wadannan ministoci na duba yiwuwar tsayawa takarar gwamna ko kuma wasu mukaman siyasa a jihohinsu, musamman a jihohin da gwamnoni za su kammala wa’adin mulkinsu na biyu a shekarar 2027.

Dokar zabe ta tanadi cewa duk wani mai rike da mukamin gwamnati da aka nada dole ne ya ajiye mukaminsa kafin ya shiga zaben fidda gwani a kowace jam’iyya.

Barcelona na tattaunawa da Manchester United kan sayen Marcus Rashford

Kungiyar FC Barcelona na matakin karshe na tattaunawa da Manchester United domin daukar dan wasan gaba Marcus Rashford.

Rahotanni sun nuna cewa ana tattaunawar cinikin ne kan kusan Euro miliyan 30, idan aka cimma yarjejeniyar, Rashford na iya zama cikakken dan wasan kunfiyar Barcelona a kakar wasanni mai zuwa.

Sojoji sun yi ajalin barayin daji, ciki hada mataimakin Ado Aleiro a jihar Katsina

Ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida ta jihar Katsina ta bayyana cewa rundunar rundunar sojin Nijeriya ta yi ajalin ‘yan bindiga 45 a wani artabu da ya faru a karamar hukumar Danmusa.

A wata sanarwar da kwamishinan ma’aikatar, Nasir Mu’azu, ya fitar ta ce an gudanar da wannan farmaki ne bayan samun bayanan sirri daga jami’an tsaro.

Daga cikin ‘yan bindigar da aka halaka akwai Alti, wanda ake cewa shi ne ɗan uwan shahararren jagoran ‘yan bindiga Adamu Alieru, haka kuma an kashe wani fitaccen dan bindiga da ake kira Damale.

Amurka ta hana wasu jami’an gwamnatin Rwanda shiga ƙasar kan zargin tallafa wa ‘yan tawayen M23

Gwamnatin Amurka ta kakaba takunkumin biza kan wasu manyan jami’an gwamnatin Rwanda, tana zarginsu da tallafa wa kungiyar ‘yan tawaye ta March 23 Movement M23 da kuma kawo cikas ga zaman lafiya a gabashin jamhuriyar dimukradiyyar Congo.

Jaridar Punch ta rawaito cewa ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa za ta hana wasu manyan jami’an gwamnatin Rwanda shiga Amurka saboda rawar da ake zargin suna takawa wajen haddasa rikici a yankin.

Sanarwar ta ce ci gaba da tallafa wa M23 da kuma saba yarjejeniyar na kara haddasa tashin hankali tare da kawo barazana ga zaman lafiya a yankin Great Lakes na Afirka.

Amurka ta kuma bukaci bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar su cika alkawurransu, ciki har da gwamnatin Congo ta dakile kungiyar FDLR, yayin da Rwanda kuma za ta janye sojojinta da kayan aikinta na soja daga cikin Congo.

Iyalan Nasir El-Rufai sun yi Allah Wadai da ci gaba da tsare shi ba bisa doka ba

Iyalan tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da tsare shi ba bisa ka’ida ba a hannun Hukumar ICPC, duk da cewa umurnin kotun magistare da aka samu don tsare shi ya ƙare.

A wata sanarwa da dan sa, Mohammed Bello El-Rufai, ya sanyawa hannu a madadin ƴan uwansa, sun ce an kama El-Rufai ne tun 18 ga Fabrairu 2026, sannan ICPC ta samu umarnin kotun majistare na tsare shi ranar 19 ga Fabrairu, amma umarnin ya ba da damar tsare shi na kwanaki 14 kacal.

Iyalan sun bayyana cewa wa’adin kwanakin ya riga ya cika, amma har yanzu ba a gurfanar da shi a kotun da ta dace ba, kuma ba a sake samun wani sabon izini daga kotu da zai ba da damar ci gaba da tsare shi ba.

Dan wasan gaba na kungiyar Al-Nassr FC, Cristiano Ronaldo, ya samu rauni mai tsanani

Rahotanni sun ce kocin kungiyar, Jorge Jesus, ya tabbatar da cewa Ronaldo zai yi tafiya zuwa Spain domin samun kulawa ta musamman daga wani kwararren likita da ke kula da lafiyarsa.

Fabrizio Romano ya rawaito cewa an yanke shawarar kai shi Spain ne domin a ba shi kulawa ta musamman da za ta taimaka wajen warkar da raunin cikin gaggawa.

Sai dai har yanzu ba a bayyana irin raunin da Ronaldo ya samu ba, amma ana sa ran karin bayani zai fito daga kungiyar Al-Nassr FC nan gaba.

‘Yan sanda sun kama mutumin da ya sayar da ɗan ‘yar uwarsa jariri kan Naira miliyan 2

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekara 30 bisa zargin sayar da jaririn ‘yar uwarsa ɗan wata guda a kan kudi Naira miliyan biyu.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN, ya rawaito cewa wanda ake zargin, mazaunin Igbogbo, Ikorodu, ya bayyana cewa ya sayar da jaririn ne domin samun kudin da za a yi jana’izar mahaifiyarsu.

Lamarin ya fito fili ne bayan mahaifiyar jaririn ta kai korafi ga ‘yan sanda.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olohundare Jimoh, ya umarci a mika binciken shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar, wato SCID, da ke Panti, domin zurfafa bincike kan lamarin.