DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 100

Wani mai lalurar gani ya cike neman aikin “Immigration” a Nijeriya

0

Wani mai lalurar gani daga jihar Sokoto ya cike neman aiki a hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya ‘Immigration’.

Daily Trust ta ruwaito yadda mutumin mai suna Umar Muhammad dan shekaru 25 ya nemi aikin, duk da cewa ya rasa idanunsa tun yana kimanin shekaru 6 da haihuwa a hannun wasu ‘yan kungiyar asiri.

Ya bayyana kwarin gwiwa da cewa akwai sabuwar doka da ta wajabtawa gwamnati bai wa masu bukata ta musamman damar neman aiki da kaso biyar.

Cikin larurar tasa, Umar ya kammala karatun NCE a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, inda yanzu haka yake karatun digiri a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke jihar.

A baya kafin wannan lokaci dai ya taba samun takardar aiki da gwamnatin jihar Sokoto a lokacin da tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal ke daf da sauka, sai dai gwamnatin yanzu ta dakatar da aikin saboda wasu dalilai, kamar yadda ya shaidawa jaridar.

Gwamnan Legas zai gabatar da Naira tiriliyan 4.2 a matsayin kasafin kudin 2026

0

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya shirya gabatar da Naira tiriliyan 4.2 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2026.

Jaridar Punch ta ruwaito yadda majalisar dokokin jihar ta tabbatar da karbar bukatar gwamnan a cikin wata wasika da ya aike mata, yana mai neman ta tsayar masa da rana don zuwa ya gabatar.

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labari dai, majalisar ba ta tsayar da ranar da za ta gayyaci gwamnan don ya gabatar da kasafin ba.

Jam’iyyar ADC ta sake bukatar rajistar su Atiku a hukumance

0

Jam’iyyar ADC reshen jihar Adamawa ta bukaci tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal su yi rajistar zama mambobinta a hukumance.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban ADC na Adamawa Shehu Yohanna na yin wannan kira, yana mai cewa cikin makon nan Atiku Abubakar zai je jiharsa ta Adamawa don gabatar da bikin ranar haihuwa da kuma wasu al’amura.

[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

A cewar sa, yana sa ran Atiku Abubakar zai yi amfani da wannan dama don yankar tikitin zama cikakken dan jam’iyya.

Kafin wannan lokaci dai jam’iyyar ta ADC reshen Adamawa, ta sha bai wa su Atiku wa’adin yankar katin zama cikakkun mambobi, sai dai har zuwa wannan lokaci babu wani yunkuri daga manyan ‘yan siyasar.

Gwamnan Taraba ya dage komawa APC saboda sace ‘yan makaranta a Kebbi

0

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya sanar da jinkirta komawarsa jam’iyyar APC sakamakon sace ‘yan makaranta da ‘yan bindiga suka yi a Kebbi.

 

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun gwamnan, Kefas ya bayyana cewa gabatar da wani lamarin siyasa a daidai lokacin da kasa ke cikin irin wannan yanayi na sabon jimamin matsalar tsaro ba abu ne da ya dace ba.

 

Jaridar Punch ta ruwaito sakataren jam’iyyar APC na Nijeriya Felix Morka, na bayyana cewa an dage bikin tarbar gwamnan zuwa wani lokaci da za a sanar nan gaba.

 

A baya dai an tsara ficewar gwamna Kefas daga jam’iyyar hamayya ta PDP, tare da komawa APC mai mulkin Nijeriya a ranar Laraba 19 ga watan Nuwamban 2025.

Majalisar dattawa ta bukaci a dauki matasa aikin tsaro domin magance matsalar tsaro

0

Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla 100,000 cikin rundunonin tsaro domin ƙarfafa tsaron ƙasar da ya yi rauni.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, wannan matakin ya biyo bayan kudirin da Sanata Abdullahi Yahaya na Kebbi ta Arewa ya gabatar, inda ya ce matsalar tsaro ta kai wani yanayi mai tayar da hankali da ke bukatar gaggawar daukar matakin kasa.

Sanatoci irin su Abdul Ningi da Aminu Tambuwal sun ce lamarin barazana ce ga makomar kasa, suna kira ga ‘yan majalisa su guji siyasantar da batun, yayin da tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya nuna takaicinsa cewa duk da kudaden tsaro masu yawa, hare-hare da sace-sace na ci-gaba.

Majalisar ta kuma kafa kwamiti na wucin-gadi domin binciken yadda aka yi amfani da kudaden shirin “Safe School” duk da cewa makarantun ƙasar na kara zama cikin hadari, musamman bayan sace dalibai a Kebbi.

Matukar dimokradiyya ta gaza a Nijeriya sai ya shafi fadin Yammacin Afrika – ECOWAS

0

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a duk faɗin Yammacin Afrika, kamar yadda shugaban hukumar, Omar Touray, ya bayyana a wajen kaddamar da shirin “Regional Partnership for Democracy” a Abuja.

Wakilinsa, Abdel-Fatau Musah, ya ce dimokuradiyya na cikin tsananin barazana a yankin, yana yaba wa Nijeriya, Ghana, Senegal da Cabo Verde bisa tsayuwa kan tsarin jam’iyyu da dama, tare da nanata cewa matsalar Nijeriya na iya shafar makomar yankin baki ɗaya.

Musah ya yi kira ga ƙasashen Yammacin Afrika su sake nazarin wa’adin shekara huɗu na shugabanci saboda rashin wadatar da yake yi wajen aiwatar da manyan shirye-shirye da kuma gina dimokuradiyya mai ɗorewa.

Haka kuma, ya bayyana kalubalen da ke barazana ga tsarin mulki a yankin, ciki har da juyin mulki, amfani da kotu wajen karkatar da doka, da kuma hana jam’iyyun adawa damar shiga siyasa, yana mai cewa wa’adin shekara huɗu ba ya wadatarwa ga ƙasashe irin su Nijeriya da Ghana wajen magance matsalolin ci-gaba.

PDP tsagin Wike ta kori Bala Muhd da Dauda Lawan, gwamnonin Bauchi da Zamfara

0

Jam’iyyar PDP ta kara shiga wani sabon rikici a ranar Talata bayan bangaren kwamitin zartaswa da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tabbatar da korar gwamna Oyo, Seyi Makinde, da na Bauchi, Bala Mohammed da kuma na Zamfara, Dauda Lawal.

Kamar yadda sanarwar da Sanata Sam Anyanwu ya karanta ta bayyana, zaman NEC da aka yi a Wadata Plaza ya kuma kori tsohon shugaban kwamitin amintattu, Adolphus Wabara, Bode George da sabon shugaban jam’iyyar da aka zaba Kabiru Turaki, SAN.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan babban taron PDP na Ibadan da ya haifar da sabani, lamarin da ya janyo arangama bayan bangarorin biyu sun shirya zaman NEC da BoT a sakatariyar jam’iyyar.

PDP ta kuma rushe shugabanni a jihohi shida tare da umartar kafa rikon kwarya, sannan ta amince da fara hukunci kan wasu jiga-jigan jam’iyya bisa zargin karya doka da bata sunan jam’iyya kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Babban hafsan sojin kasa ya umurci sojoji da su tsaurara wajen ganin sun ceto dalibai mata da aka sace a jihar Kebbi

0

Babban hafsan rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya umarci dakarun Operation Fansan Yamma da su matsa kaimi wajen ceto daliban GGCSS Maga da aka yi garkuwa da su a Danko/Wasagu.

A cikin wata sanarwa da Kyaftin David Adewusi ta bayyana, Janar Shaibu ya umurci haka ne yayin kai ziyarar aiki a jihar Kebbi inda ya bukaci dakarun su yi aiki bisa bayanan leƙen asiri tare da bin sawun ’yan bindiga dare da rana, sannan da hada kai da ’yan banga da mafarauta domin sanin hanyoyin yankin.

Haka kuma, ya kai ziyarar ta’aziyya ga sarkin Danko da shugabar makarantar, yana tabbatar musu da cewa rundunar soji za ta tabbatar an kubutar da daliban ba tare da lahani ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ya umarci dakaru su kasance masu ladabi da ƙwarewa tare da bin ka’idojin aiki domin dawo da zaman lafiya a Kebbi da yankunan da ke makwabtaka.

’Yan bindiga sun sace fasinjoji shida a hanyar Ogobia–Adoka a Benue

0

’Yan bindiga sun tare wata motar haya suka tafi da fasinjoji shida sannan suka kashe direba a hanyar Ogobia–Adoka da ke ƙaramar hukumar Otukpo a Jihar Benue, kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Lamarin ya faru a ƙarshen mako, in ji shugaban ƙaramar hukumar Otukpo, Alfred Omakwu, wanda ya tabbatar da faruwar abin ta wayar tarho, yana mai cewa har yanzu ba a san matsayin fasinjojin ba sai dai jita-jitar cewa an fara tattaunawa da iyalansu.

Wasu mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun tilasta motar ta tsaya, abin da ya jawo ta shiga cikin daji kafin a tafi da fasinjojin zuwa wuri da ba a sani ba.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Benue, DSP Udeme Edet, ta ce za ta fitar da karin bayani daga baya, amma har zuwa lokacin wannan rahoto ba ta dawo da martani ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano za ta karfafa tsaro a iyakokin jihar

0

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gana da kwamandojin rundunar ‘yan sanda don duba dabarun tsaro da karfafa matakan tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.

Taron, da aka gudanar a ranar Litinin a hedkwatar ‘yan sandan ta jihar Kano, ya hada manyan jami’an sassa daban-daban na ayukka da dabaru da leken asiri kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

CP Bakori ya ce taron ya bai wa rundunar damar nazarin nasarorin da aka samu wajen hana laifuka da aiwatar da doka a jihar, tare da tsara hanyoyin kara karfafa ayyukan tsaro, kuma ya jaddada muhimmancin hada kai da al’umma, inda ya umarci shugabannin ayyukan da su karfafa wayar da kan jama’a a matakai na gida.

Hakazalika, ya ce taron ya mai da hankali musamman kan yanayin tsaro a kan iyakokin Kano, musamman karamar hukumomi Shanono, Tsanyawa da Rogo, inda ya bayyana ci-gaban da ake yi wajen kara jami’ai da kayan aiki, tare da bukatar a ci gaba da lura da sabbin barazanar tsaro.