DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 101

Hayaniya ta barke a sakatariyar PDP a Abuja

0

An yi hatsaniya a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Abuja sakamakon yunkurin bangarori biyu na jam’iyyar su gudanar da zaman nasu a rana ɗaya, abin da ya haifar da rikici a harabar Wadata Plaza.

Rahotanni sun bayyana cewa sakataren jam’iyyar na bangaren Wike, Samuel Anyanwu, ya isa sakatariyar tare da magoya bayansa, sai daga baya kuma mambobin bangaren Taminu Turaki suka iso amma ba a bari suka shiga ba.

Wasu gwamnoni biyu daga bangaren Turaki sun tilasta shiga, amma da sauran ’ya’yan bangaren suka yi ƙoƙarin bi, jami’an tsaro suka harba bindiga da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su.

Lamarin ya haifar da firgici inda mutane suka watse domin neman tsira kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A jawabinsa kafin zuwan ɗayan bangaren, Anyanwu ya ce ƙarin tsaro da aka gani al’ada ce domin kaucewa tashin hankali, kana ya bayyana shirin bangarensa na gudanar da zaman BoT da NEC.

Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore ya yi Allah-wadai da sace dalibai a jihar Kebbi

0

Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yi Allah-wadai da sace ‘yan mata 25 daga Makarantar sakandare ta gwamnati, da ke a Maga, a karamar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi, tare da kiran addu’a ga wadanda abin ya shafa.

Moore ya ce duk da har yanzu ba su samu cikakken bayani ba kan wannan mummunan hari, amma ya bayyana cewa yana kyautata zaton ya faru ne a wani yanki na Kiristoci a Arewacin Nijeriya, kuma ya bukaci hukumomi su dauki kwakkwaran mataki.

An kai harin ne da safiyar ranar Litinin, inda ‘yan bindiga suka shiga makarantar da makamai, suka hallaka mataimakin shugaban makarantar, tare da raunata wasu ma’aikata, sannan suka sace ‘yan mata 25 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tsare-tsaren gwamnati na da manufar yaki da talauci a tsakanin matasa – Shugaba Tinubu

0

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki da na gyare-gyaren hukumomin gwamnati suna nufin bai wa matasa kwarewa da ilimi mai inganci domin su iya fafatawa a duniya da kuma tabbatar da makomarsu ta hanyar ci-gaban ilimi.

Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin yayin da yake karbar Duke na Edinburgh, Prince Edward, a Fadar shugaban Nijeriya, Abuja kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, batun matasa zai kasance gaba-gaba a taron G-20 da za a gudanar wannan makon, inda ya kara da cewa manufofin gwamnati sun mayar da hankali kan yawan jama’a da bunkasa kwarewa don habaka tattalin arziki.

Hakazalika, ya jaddada cewa sabon shirin bayar da rancen dalibai wani muhimmin mataki ne na fadada damar samun ilimi ga matasa, inda ya ce gwamnati na amfani da kyawawan dabaru wajen samar da kwarewa a fannoni da dama, domin inganta rayuwar matasa da ci-gaban kasa.

Shugaba Tinubu ya gargadi alkalan Nijeriya cewa adalci ba hajar sayarwa ba ce

1

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya gargadi alkalan Najeriya cewa dole adalci ya kasance a tsarkake ba tare da yunƙurin cakuda shi da rashawa ba.

Yayin taron alkalai da aka buɗe a Abuja a ranar Litinin, Tinubu ya ce alkalan manyan kotuna su ne ginshikan adalci, kuma gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a horo, jin daɗi da aikin cibiyar shari’a ta ƙasa.

Tinubu ya jaddada cewa babu wani gyara da za ya yi tasiri ba tare da gaskiya da rikon amana ba, yana gargadin cewa cin hanci a bangaren shari’a na iya rushe ƙasar baki ɗaya.

Ya kuma nuna damuwa kan yawan shari’o’in da ke taruwa da jinkirin yanke hukunci, yana mai cewa dole kotuna su ɗauki matakai na gaggawa domin dawo da amincewar jama’a da ƙarfafa tsarin mulkin Nijeriya.

Atiku Abubakar ya nuna damuwarsa kan sace dalibai a jihar Kebbi

1

Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana damuwa kan harin da aka kai Makarantar ‘yan mata ta Gwamnati da ke Maga a Jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin mutuwar mataimakin shugaban makarantar da kuma sace wasu dalibai inda ya wannan al’amari ya sake tabbatar da irin tabarbarewar tsaron da ƙasar ke fuskanta.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na facebook, Atiku ya kuma yi Allah-wadai da kisan jigon APC, Umar Moriki, da kuma sace iyalai da dama a karamar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, yana mai bayyana wadannan hare-haren a matsayin aikata barna da ya sabawa duk wata al’umma mai bin doka.

Hakazalika, ya kuma ambaci irin tashin hankalin da ake fama da shi a Jihar Filato, Benue da wasu yankuna, inda ya ce al’ummomi na ci-gaba da fuskantar hare-hare.

Haka ma a karama Hukumar Shanono ta Kano, ya jaddada cewa mutanen yankin na tserewa daga gidajensu saboda fargabar hare-hare.

Madugun adawar ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta sake fasalin tsaro, ta ƙara yawan jami’an tsaro a yankunan da abin ya fi shafa tare da ƙara amfani da bayanan leƙen asiri wajen dakile hare-hare sannan kuma ya ce ’yan Najeriya sun cancanci kariya, mtuntawa da zaman lafiya.

Jami’an tsaro sun kaddamar da shirin ceto daliban da aka sace a jihar Kebbi

1

’Yan sanda da sojoji sun kaddamar da bincike da aikin ceto domin kubutar da dalibai 25 da aka sace daga makarantar ’Yan Mata ta gwamnati da ke Maga, ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewar rahotannin da aka samu daga jami’an tsaro, maharan sun kutsa makarantar da safiyar Litinin, inda suka hallaka ma’aikaci ɗaya tare da jikkata wani jami’in tsaro a lokacin da suka mamaye harabar makarantar.

Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da lamarin, inda ta bayyana cewa tawagar da ke gadin makarantar ta yi musayar wuta da maharan, amma ’yan bindigar sun riga sun shiga cikin makarantar suka kwashe daliban zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa an tura tawaga ta musamman tare da hadin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro domin bin diddigin hanyoyin da maharan suka bi da kuma lalubo dazuzzukan da ake zargin sun tsere.

Shugaba Tinubu ya jijina ma tawagar Super Eagles ta Nijeriya kuma ya bukaci su mayar da hankali kan gasar cin kofin nahiyar Afrika

0

Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa tawagar kwallon kafa ta Nijeriya, Super Eagles bisa jajircewarsu a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026, duk da rashin nasarar da suka sha a hannun DR Congo bayan bugun fenariti a Rabat, Morocco.

Wasan ya ƙare 1 da 1 bayan mintuna 120, inda DR Congo ta doke Nijeriya da ci 4 da 3 a bugun fenariti.

Tinubu ya ce dole a jinjina ƙoƙarin ‘yan wasan duk da ba a samu sakamakon da ake so ba, kamar yadda mai ba shi shawara kan labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a duba kura-kuran da aka samu a wasan, tare da gyara duk wani gibin da ya hana ƙungiyar samun nasara.

A cewarsa, yanzu hankali ya koma kan gasar kofin nahiyar Afrika da za a yi a Morocco daga watan Janairu zuwa Fabrairu 2026 inda ya ce Super Eagles na bukatar dawo da kima da martabarsu a gasar nahiyar.

Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya su cigaba da mara wa ƙungiyar baya, yana cewa duk da rashin sa’a, Eagles sun nuna jajircewa da himma tun daga wasan farko har zuwa bugun fenaritin da ya yanke hukuncin karawar.

PDP za ta bude kofar hadaka da jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027 – Kabiru Turaki

1

Zababben shugaban jam’iyyar PDP, Kabiru Tanimu Turaki (SAN), ya ce jam’iyyar za ta yi la’akari da duk wani haɗin gwiwa da zai karfafa dimokuradiyya kafin zaben 2027.

Kabiru ya bayyana cewa PDP za ta mayar da hankali wajen ceto Nijeriya daga matsalolinta, sannan za ta bi kowace hanya ta siyasa wacce jama’a za su yaba da ita.

A cewarsa, jam’iyyar za ta yi aiki tare da sauran jam’iyyun adawa, kungiyoyin farar hula, da manema labarai domin tabbatar da dimokuradiyya, inda ya ce duk wani zaɓi da jama’a za su amince da shi za a yi la’akari da shi.

Matatar man Dangote ta yi karin haske kan dalilin saukowar farashin man fetur

0

Matatar man Dangote ta bayyana rahotannin da ke cewa saukin farashin fetur ya samo asali ne daga dakatar da harajin shigo da fetur da dizal na kashi 15 a matsayin shaci-fadi.

Kamfanin ya ce gaskiyar lamarin shi ne saukin ya samo asali ne daga rage farashin wasu kayayyaki da kashi 5.6 a ranar 6 ga Nuwamba.

Dangote ya jaddada cewa harajin kaso 15 na shigo da kaya ya riga ya samu amincewar shugaban Nijeriya tun ranar 21 ga watan Oktoba, kuma hakan bai yi tasiri kan farashin kamfanin ba.

Hakazalika, ya tabbatar da ci-gaba da samar da fetur mai inganci a farashi mai rahusa, tare da kira ga kafofin watsa labarai da masu ruwa da tsaki su dogara kan sahihan bayanai wajen sanar da jama’a.

Nicki Minaj za ta yi jawabi a majalisar dinkin duniya kan zargin hare-hare a kan Kiristoci a Nijeriya

1

Shahararriyar mawakiyar Amurka, Onika Maraj-Petty wadda aka fi sani da Nicki Minaj, za ta yi jawabi gaban Majalisar Dinkin Duniya a New York a ranar Talata, inda ake sa ran za ta tabo batun hare-haren da ake cewa ana kai wa Kiristoci a Nijeriya.

Za ta bayyana ne tare da jakadan Amurka a MDD, Michael Waltz, da Alex Bruesewitz, ma ba shugaban Amurka Donald Trump shawara.

Wannan ci-gaban ya fito ne daga rahoton Eric Cortellessa na mujallar Time, wanda ya tabbatar da halartar Minaj inda Waltz ya yabe ta, yana cewa ba wai ta shahara a kiɗa kaɗai ba, har ma tana da jajircewar magana kan abin da take ganin rashin adalci ne, musamman abin da ya kira cin zarafi ga Kiristoci a Nijeriya.

Minaj ta mayar da martani tana godiya saboda gayyatar, tare da cewa ba za ta yi shiru ba kan duk wani abu da ta dauka a matsayin rashin adalci kuma wannan wani hakki ne da take dauka da muhimmanci.

Shirye-shiryen taron sun biyo bayan ikirarin Trump na cewa ana aiwatar da kisan kiyashi ga Kiristoci a Nijeriya, yana mai kira ga Majalisa ta dauki mataki gaggawa.

Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta wannan zargi, tana cewa matsalar tsaron Nijeriya ba ta ta’allaka ba da addini, duk da cewa jami’an Amurka na ci-gaba da nuna damuwa.