DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 99

Amnesty International ta koka kan halin da jihar Katsina ke ciki kan batun tsaro

0

Kungiyar kare hakin bil’adama ta Amnesty International ta gargadi cewa hare-haren ’yan bindiga da ƙungiyoyin ta’addanci suna tura Jihar Katsina zuwa ga mummunan bala’in jin-kai, yayin da dubban al’ummomi ke tserewa daga gidajensu saboda tsananin rashin tsaro.

A cewar kungiyar, mutane da dama sun rasa matsuguni, yara na mutuwa saboda ƙarancin abinci, sannan iyaye, musamman mata, na kallo rayukan yarensu na salwanta a gaban idanuwansu. Amnesty International ta rawaito cewa Kungiyar likitoci ta MSF ta tabbatar da cewa yara 652 sun mutu sakamakon matsanancin rashin abinci cikin watanni shida na farko na bana.

DCL Hausa ta ruwaito cewa Amnesty International ta nuna damuwa matuƙa kan yadda mutane a ƙananan hukumomi 13 cikin 34 ke fama da hare-hare, garkuwa, kwace amfanin gona da ƙona gidaje, lamarin da ya hana ma’aikatan jin-kai shiga da agajin gaggawa.

Kididdigar UNICEF ta nuna cewa yara sama da 300,000 ba sa zuwa makaranta a Katsina saboda tsaro, tare da karin dubban yara a Dandume, Jibiya, Safana, Batsari, Faskari, Funtua da Kankia da ke fama da matsananciyar rashin lafiya da abinci. Amnesty International ta bukaci gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina su dauki mataki na gaggawa wajen kawo ƙarshen wannan tashin hankali.

Gwamnatin Sokoto ta kammala aikin samar da lantarki na kashin kanta na N7bn

0

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kammala aikin gina tashar samar da wutar lantarki ta mai zaman kanta, kamar yadda Kwamishinan Makamashi, Alhaji Sanusi Danfulani, ya bayyana yayin ziyarar duba aikin da aka kai ranar Laraba.

Kamar yadda Kwamishinan ya shaida wa manema labarai, gwamnatin jihar ta zuba biliyoyin naira a aikin, tare da ƙarin N1.5bn da Gwamna Ahmad Aliyu ya saki kwanan nan domin gyare-gyare da kammala aikin.

A yayin da yake karin haske, Daraktan Sashen Lantarki na ma’aikatar, Injiniya Abubakar Shehu, ya bayyana cewa an gwada wasu sassan injinan a makon da ya gabata, sai dai ya ƙi fayyace matakin da gwamnati za ta ɗauka kan yadda za a tura wutar zuwa jama’a, yana mai cewa wannan ya rage ga hukumomin wutar lantarki.

Rahotanni sun nuna cewa aikin na megawatt 38 an bai wa kamfanin Vulcan Capital Energy na Amurka ne a 2008 kan kuɗin N3.8bn da wa’adin watanni shida, amma an yi ta tsawaita lokacin kammalawa daga 2009 zuwa 2010, 2011, 2013, 2014, 2016 har zuwa 2019 kafin a ce yanzu an kammala shi.

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai

Majalisar dokokin jihar Kebbi ta dakatar da shugaban karamar hukumar Fakai a jihar Kebbi da DCL Hausa ta yi rahoton zargin da ake yi masa na cefanar da fili da ‘transatomomi’.

Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Fakai, Muhammad Mahuta, bisa zargin aikata munanan ayyuka da sakaci wajen gudanar da aikinsa, biyo bayan amincewa da rahoton kwamiti na musamman da majalisar ta kafa ƙarƙashin jagorancin Salihu Dangoje, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

A cewar kwamitin, bincike ya gano zarge-zargen haɗa hannu wajen cire da kuma yunƙurin sayar da injinan wuta guda biyar, rabon gonakin gwamnati ba bisa ka’ida ba, da karya yarjejeniyar aikin gyaran madatsar Mahuta.

Kwamitin ya ce Mahuta ya bayyana musu cewa an ɗauki injinan ne domin gyara da izinin wani jami’in KEDCO mai suna Malam Nasir, wanda bai amsa gayyatar kwamitin ba.

Sai dai a ranar 14 ga Nuwamba, shugaban ƙaramar hukumar ya amsa gaban kwamitin cewa ya yi almundahanar injinan guda biyar da ake shirin sayar wa wani Alhaji Kabiru Dauda kan naira miliyan 2.5 kowanne.

Lantarkin N40.61bn ta salwanta tun kafin ta kai ga masu amfani a Nijeriya – NERC

0

Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya(NERC) ta bayyana cewa an yi asarar wutar lantarki da ta kai Naira biliyan 40.61 a layukan ba da lantarki, wacce bata kai ga cibiyoyin rarrabawa ba.

Lamarin ya faru ne duk da ƙarancin lantarkin da ake samu a gidaje da kamfanoni a fadin ƙasar, in ji rahoton jaridar Daily Trust.

A cewar rahotannin da hukumar ta fitar na kwata-kwata, kamar yadda jaridu suka ruwaito, an yi asarar biliyan N22.64 a rubu’i na farko na 2025, yayin da asarar ta kai biliyan N17.97 a rubu’i na biyu.

Hukumar ta bayyana wannan a matsayin Transmission Loss Factor (TLF), wato kaso na wutar da masana’antar samarwa ta tura amma ta salwanta a hanya ko kuma aka yi amfani da ita a tashoshi, ba tare da ta kai ga kamfanonin rarrabawa ko ƙasashen waje ba.

Rahoton ya nuna cewa adadin da aka yi asara ya zarce kashi 7 cikin 100 da aka amince, inda aka samu kashi 9 cikin 100 na salwantar wutar a kwata na farko, abin da ya nuna raguwar ingancin tsarin watsawa.

Pantami ya ba gwamnatin Nijeriya shawarar yin amfani da fasahar zamani don yakar ayyukan ta’addanci

0

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana damuwarsa bisa yawaitar hare-hare, kisa da kuma garkuwa da mutane da ake fuskanta a jihohin ƙasar nan, musamman Kebbi da Zamfara.

Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi tir da yawaitar tashe-tashen hankula a fadin Nijeriya, musamman hare-haren da ake yi da kuma garkuwa da mutane da dama a jihohin Kebbi da Zamfara.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yana Allah wadai da abin bakin cikin, Pantami ya yi kira ga hukumomin gwamnati da su gaggauta rungumar sabbin dabaru na zamani da suka dogara ga fasaha domin yakar ta’addanci da kuma kare rayukan ‘yan kasa.

Pantami ya ce amfani da fasahohi na zamani zai taimaka wajen cafke masu aikata laifin, hana sake faruwar irin wadannan hare-hare, da kuma dawo da zaman lafiya.

Ya kuma bukaci ’yan kasa su rika bada bayanan sirri da zai taimaka wa hukumomin tsaro wajen tunkarar miyagun laifuka.

Gwamnatin Kwara ta sanar da rufe makarantun boko a kananan hukumomi 4 na jihar

0

Gwamnatin jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a wasu kananan hukumomi hudu na jihar, bayan hare-hare da suka yi ƙamari cikin sa’o’i 48 da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Laraba, mutane uku sun rasa rayukansu a kauyen Bokungi da ke karamar hukumar Edu, yayin da aka kai hari kan wata coci a garin Eruku da ke karamar hukumar Ekiti, inda mutane biyu suka mutu, sannan aka sace mutum 30.

Wani ganau ya ce maharan sun fara sace mutane huɗu ciki har da ɗan banga, sai daga baya suka kashe manoma biyu da kuma jikkata ɗaya.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta ɗauki matakan tsaro a dukkan makarantu don kare rayuwar ɗalibai da malamai, tare da tabbatar da cewa ba za a bar makarantu cikin haɗari ba.

Matakin ya shafi makarantu a kananan hukumomin Ifelodun, Ekiti, Irepodun, Isin da Oke Ero. Matakin dai ya biyo bayan karuwar hare-haren ‘yan bindiga a yankunan kananan hukumomin.

‘Yan sandan Abuja sun yi ajalin ‘yan ta’adda lokacin da suka dakile wani hari

0

Rundunar ‘yan sandan Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya ta dakile wani yunƙurin garkuwa da mutane da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne su kimanin 30 suka yi a kauyen Guto da ke karamar hukumar Bwari.

A cewar sanarwar da SP Josephine Adeh, kakakin rundunar ‘yan sandan ta aike wa DCL Hausa, ta ce ‘yan sandan sun yi ajalin biyu daga cikin maharan yayin da sauran suka tsere cikin daji.

Sai dai a yayin musayar wuta, wani ɗan sanda ya samu mummunar rauni, inda daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsa a asibitin Bwari.

Wasu tsoffin ‘yan majalisar dokokin Kano sun yi mubaya’a ga Barau Jibrin a takarar gwamna a 2027

1

Wasu tsoffin ‘yan majalisar dokokin jihar Kano da kuma masu ci a yanzu sun mara wa mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Barau Jibrin baya don tsayawa takarar gwamna a shekarar 2027.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar mutanen da adadinsu ya zarta 200, sun kai wa dan majalisar dattawan mai wakiltar Kano ta Arewa ziyara ne karkashin jagorancin tsohon kakakin majalisar dokokin Kano Rt. Hon. Abdul’aziz Gafasa, inda suka bayyana shi a matsayin mafi cancanta da takarar gwamnan Kano a jam’iyyar APC.

 

A cewar su, ayyukan da Barau Jibrin ke gabatarwa sun taba rayukan daukacin al’ummar jihar Kano daga kowace shiyya, a don haka za su yi iya bakin kokari wajen hada kan mutane a yi tafiyarsa baki daya.

Gwamnati ta binciki ta’azzarar matsalar tsaro a Nijeriya – Kwankwaso

0

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta da gudanar da bincike kan musabbabin ta’azzarar matsalar tsaro a wasu sassan kasar.

 

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya yi Allah-wadai da sace ‘yan makaranta 25 da ‘yan bindiga suka yi a jihar Kebbi, bayan farmakin da suka kai.

 

Kazalika Kwankwaso ya nuna damuwa da sauran matsalolin tsaro da ke faruwa a jihohi irin su Zamfara da Kano, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

A hannu guda, ya bayyana kisan Birgediya Janar Musa Uba a Borno a matsayin wani bakin tabo a fagen tsaron Nijeriya, yana mai bukatar a gaggauta bincikar lamarin.

Gwamnan Kano ya dauki malaman lissafi 400 aiki a makarantun sakandire

0

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan takardar daukar malaman lissafi 400 a makarantun sakandiren da ke fadin jihar aiki.

 

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta bayyana cewa daukar matakin wani yunkuri ne na cike gibin da ake samu a ilimin daliban jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

 

A cewar sa, darasin lissafi shi ne ginshikin kimiyya, fasaha, kirkire-kirkire har ma da fagen injiniyanci, a don haka ya zama wajibi gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta matakin iliminta.

 

Gwamnan ya bukaci sabbin malaman da su sanya kwarewa da mayar da hankali wajen ganin sun sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.