DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 102

Kasashen Nijeriya, Mozambique da Sudan na daga cikin kasashen da ake musguna ma Kiristoci – Shugaban darikar Katolika

1

Jagoran Katolika, Pope Leo XIV, ya saka Najeriya cikin jerin kasashen da Kiristoci ke fuskantar tsangwama, tare da Bangladesh, Sudan, Mozambique, da wasu ƙasashe.

Leo ya wallafa hakan ne a shafinsa na X, inda ya nuna damuwarsa kan hare-haren da ake kaiwa al’ummomin Kiristoci da coci-coci, sannan ya yi kira da yin addu’o’i don zaman lafiya da hadin kai.

Maganganun Pope sun yi daidai da na shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya sanya Nijeriya a matsayin ‘kasar da ke cikin damuwa ta musamman’ kan tsangwamar addini ga Kiristoci wanda hakan ya jawo hankalin duniya kan batun tsangwamar addini a Nijeriya.

Sai dai gwamnatin Nijeriya ta musanta wannan zargi, tana mai cewa kasar ba ta nuna wariya ga wani addini ba, kuma tana matsayin kasa mai zaman lafiya da bin doka. Gwamnatin ta jaddada cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta ba na addini ba ne, sai dai na laifuka daban-daban.

Kungiyar Arewa maso Tsakiya ta jam’iyyar APC ta yi tir da zanga-zangar da wasu suka yi na nuna kin yarda da gwamnan Filato ya dawo APC

0

Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta yi tir da zanga-zangar da wasu ‘yan APC na jihar Filato suka yi a Jos domin nuna kin amincewa da yiwuwar gwamna Caleb Mutfwang ya koma jam’iyyar inda ta bayyana wannan mataki a matsayin ba na dimokuradiyya ba ne, kuma babu wata doka da ta halatta shi.

A cewar shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, babu wani mutum ko rukuni da ke da ikon hana kowane ɗan Najeriya shiga jam’iyyar da yake so, ciki har da gwamna mai mulki.

Zanga-zangar dai ta faru ne a yayin tarbar sababbin ‘yan jam’iyya da aka yi, inda wasu suka daga alluna suna nuna adawa da shigowar Mutfwang kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kungiyar ta sake jaddada kiran da take yi wa Mutfwang ya sauya sheƙa zuwa APC domin ƙara wa jam’iyyar ƙarfi kafin 2027, tana zargin masu adawa da yunkurin da neman biyan bukatunsu na kai.

Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta nemi Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamna Simon Lalong su shiga tsakani domin tabbatar da cewa an karɓi gwamnan cikin sauƙi.

PDP bangaren Wike sun kira taron gaggawa na shugabanni da ƴan kwamitin amintattu na jam’iyyar

0

Bangaren jam’iyyar PDP da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da cewa za a gudanar da taron gaggawa na kwamitin amintattu da na zartaswa na jam’iyyar a ranar Talata, 18 ga watan Nuwamba, 2025, a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja.

A cikin sanarwar da sakataren Jam’iyyar na bangaren Wike, Samuel Anyanwu, ta nuna wadda mai taimakawa ministan wajen yada labarai, Lere Olayinka, ya wallafa, taron amintattun zai fara da misalin 11 na safe, yayin da na zartaswa zai biyo baya da karfe 2 na rana.

Sanarwar ta ce halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar yana da muhimmanci domin tattaunawa kan muhimman batutuwa, musamman bayan da PDP a taronta na kasa da aka yi a Ibadan ta kori Wike, Anyanwu, Ayo Fayose, Kamaldeen Ajibade da wasu shugabanni bisa zargin cin amanar jam’iyya.

Korarsu ta biyo bayan kudirin da Bode George ya gabatar, Samaila Buga na PDP Bauchi ya mara wa baya, sannan gwamna Bala Mohammed ya sanya wa kwamitin muryar amincewa wadda ta nuna sahalewar wakilai kan hukuncin share baragurbin cikin jam’iyyar.

‘Yan sandan Nijeriya sun musanta rahoton yunkurin hallaka sojan da suka yi cacar baki da Wike a Abuja

0

Rundunar ’yan sandan Abuja ta musanta rahotannin da ke cewa an yi yunkurin hallaka jami’in sojan ruwa, Laftanar Ahmed Yerima, a Abuja inda ta ce labarin ba gaskiya ba ne kuma ba a samu rahotonsa a ko’ina cikin birnin ba.

Rahotannin da suka bazu a kafofin sada zumunta sun yi zargin cewa wasu da ba a san ko su wanene ba, sanye da kata bakake, a cikin motocin Hilux marasa lamba, sun bi motar Yerima daga NIPCO a Kubwa zuwa hanyar Gado Nasco.

Wasu sun alakanta lamarin da sabanin filin da ya shiga tsakaninsa da Ministan FCT, Barista Nyesom Wike kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta ce babu wani rahoto da aka samu game da haka, kuma jama’a su yi watsi da labarin domin kauce wa tada hankula.

Rundunar ta kuma gargadi jama’a da su guji yada bayanan da ba a tabbatar da su ba domin kauce wa haifar da firgici ba gaira ba dalili.

Barayin daji sun hallaka mutane 3 tare da sace akalla 64 a jihar Zamfara

0

’Yan bindiga sun hallaka mutane uku tare da sace akalla 64 a Fegin Baza da ke Tsafe, jihar Zamfara. Mata da yara na cikin wadanda aka yi garkuwa da su, sannan mutane hudu sun jikkata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, daga cikin wadanda aka kashe har da jigo a jam’iyyar APC, Umaru Moriki, wanda aka harba a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe. Shaidun gani da ido sun ce maharan sama da 30 ne dauke da bindigogi a kan babura.

Harin ya faru kwana guda bayan ziyarar ministan tsaro Bello Matawalle, wanda ya sanar da turo sabbin sojoji tare da alkawarin murkushe ’yan bindiga.

Zamfara na ci-gaba da fama da hare-hare a kauyuka da hanyoyi, lamarin da ya tilasta dubban mutane barin gidajensu bayan garkuwa, kashe-kashe da barna sun yi kamari.

Za a iya kawo karshen matsalolin Arewa aka hada kai – Uba Sani

0

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce Arewacin Nijeriya na da kwararru da hazikan ‘yan kasa da za su iya magance matsalolin ci-gaba da ake fama da su, muddin manyan yankin suka haɗa kai domin tafiyar hanya ɗaya.

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da shugabancin Arewa Consultative Forum (ACF), ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bashir Dalhatu, ya kai masa ziyara a Kaduna.

Ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta tashi tsaye don ta yi aiki wajen warware talauci, gibin ilimi da matsalolin lafiya da suka daɗe suna damun yankin.

Gwamnan ya jaddada cewa Arewa na da dubban kwararru a fannonin kasuwanci, harkokin lafiya, masana’antu, karatu da kirkire-kirkire, waɗanda ake buƙatar haɗa su a wuri ɗaya.

Halin kuncin da ‘yan Nijeriya ke ciki ne zai yanke wa Tinubu hukunci a zaben 2027 – NNPP

0

Jam’iyyun hamayya na NNPP da ADC reshen jihar Osun sun ce halin tsananin talauci da ake ciki yanzu shi ne zai yanke wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu hukunci a zaben 2027, ba wai sauye sauyen jam’iyya ko dabarun siyasa ba.

Jaridar Punch, ta ruwaito cewa jam’iyyun biyu sun bayyana haka ne sakamakon yawaitar sauya sheka da ke faruwa a PDP, LP da NNPP, ciki har da gwamnoni uku da suka bar PDP a cikin watanni biyu da suka wuce domin komawa APC.

Mai magana da yawun NNPP, Dipo Johnson, ya ce duk da barin wasu ‘yan majalisa, jam’iyyar tana rike da mafi yawa daga cikin wakilanta 19, yana mai zargin APC da amfani da kudi wajen ingiza ‘yan majalisun tarayya zuwa jam’iyyarsu.

Kungiyar MPLJ a Nijar ta dau alhakin hari kan bututun man Nijar a yankin Agadem

0

Kungiyar ‘yan tawaye ta’ Mouvement Patriotique pour la Liberté et la Justice’ wato MPLJ ta dauki alhakin harin da aka kai a wannan rana ta 16 ga watan Nuwamba kan bututun man Nijar, kusa da cibiyar hakar man fetur ta Agadem da ke jihar Diffa.

Kungiyar tawayen ta sanar da daukan alhakin wannan hari ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan rana ta Lahadi mai dauke da sa hannun shugabanta Moussa Konai.

 

A cikin sanarwar, kungiyar ta ce ta kai wannan hari ne biyo bayan karewar wa’adin da ta bada a sanarwar ta ta karshe, inda ta gargadi kamfanoni da masana’antu masu hakar ma’adanai kan su guji hada kai da hukumomin Nijar wadanda ta ke adawa da su.

Kazalika kungiyar ta MPLJ ta ce muddin aka ci gaba da yin biris da gargadinta, za ta zafafa kai irin wadannan hare-hare har sai an kai ga rufe kamfanin tace mai na SORAZ sannan kuma a mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya.

Ina sharbar hawaye a duk lokacin da na samu labarin halaka mutane – Godswill Akphabio

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya Sanata Godswill Akpabio, ya ce gwamnati na da nauyin dawo da zaman lafiya a jihar Filato da Nijeriya baki ɗaya a wuyanta, yana mai jaddada cewa ba wata ƙasa da za ta kawo wa ƙasar zaman lafiya sai ‘yan Nijeriya da kansu.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito Akpabio na yin wannan bayani ne ranar Asabar a Jos yayin taron tarbar sababbin ‘yan wadanda suka koma jam’iyyar APC.

Akphabio ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar magance matsalar rashin tsaro da ta addabi Filato da wasu sassan ƙasar.

Akpabio ya bayyana damuwarsa kan yadda rikici da zubar da jini suka dade suna addabar jihar tun daga shekarar 2010, yana mai cewa duk lokacin da ya ji an hallaka mutum, ko yaro ne ko babba idanunsa na cika da hawaye.

Gwamnan jihar Taraba Agbu Kefas ya jaddada shirinsa na komawa APC

0

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya tabbatar da shirinsa na sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Laraba, 19 ga Nuwamban 2025.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa Gwamna Kefas ya bayyana wa manema labarai cewa wannan mataki nasa ya samo asali ne daga bukatar cigaban al’ummar Taraba, yana mai cewa sauyin jam’iyyar tasa sa ba don son rai bace, domin kuwa yana da alaka da makomar jihar.

Ya kara da cewa shirye-shiryen karbar sa a APC sun yi nisa, tare da dubban magoya baya a jihar.