DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 103

Na jagoranci yin sulhu da ‘yan bindiga akalla 600 – Sheikh Gumi

0

Sanannen Malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya mayar da martani ga masu kira da a kama shi kan tsokacinsa game da matsalar ‘yan bindiga da tsaro, inda ya kare rawar da yake takawa wajen shiga tsakanin tattaunawa da kungiyoyin ta’addanci domin neman samun zaman lafiya.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Gumi ya dade yana bayyana kansa a matsayin wanda ke shiga tsakani tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga, sai dai wasu na zarginsa da kare ‘yan ta’adda saboda ya fi jaddada maganar tattaunawa maimakon amfani da karfin soja.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, malamin ya bayyana masu kira da a kama shi a matsayin marasa kishin kasa da basu son gaskiya, inda ya ce aikinsa na shiga tsakanin tattaunawa da ‘yan bindiga ba wani laifi ba ne, domin kokari yake yi wajen kawo karshen tashin hankali.

Tinubu na shirin fitar da sunayen sabbin Jakadun Nijeriya

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu na shirin fitar da jerin sunayen jakadu da za su wakilci Nijeriya a manyan kasashe cikin makonni masu zuwa, a cewar majiyoyi daga fadar shugaban kasa.

Wannan mataki na zuwa ne bayan damuwar da jama’a ke nunawa kan yadda rashin jakadu ya rage karfin diflomasiyyar Nijeriya, musamman a kasashen da ke da muhimmanci ga hulɗar ƙasa da ƙasa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Tinubu ya janye dukkan tsoffin jakadu a watan Satumban 2023 domin sake fasalin manufofin ƙasar a ketare, sai dai jinkirin tantance sababbin jakadu ya kai shekara biyu ba tare da sabbin nade-naden ba.

Kokar su Wike daga PDP ba zai magance matsalarta ba – Celeb Muftwang

0

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya nesanta kansa daga matakin jam’iyyar PDP na korar Ministan Abuja, Nyesom Wike, da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, da sauran manyan jiga-jigai da aka zarga da yi wa jam’iyyar zagon kasa.

A cikin wata sanarwa da daraktan yada Labaran gwamnan Gyang Bere ya fitar, Mutfwang ya bayyana cewa wannan batu ba a tattauna shi ba a taron Gwamnonin PDP kafin a gabatar da shi a gangamin jam’iyyar da ake gudanarwa a Ibadan.

Ya ce matakin da aka dauka bai dace ba, kuma ba shi ne hanya mafi dacewa don magance rikicin jam’iyyar ba.

Atiku da Kwankwaso ba za su taba zama inuwar jam’iyya guda ba – Jigo a APC

0

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kudu maso gabashin Nijeriya Ijeoma Arodiogbu, ya ce rade-radin da ake yi cewa Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin yin kawance kafin zaben 2027 ba shi da tushe ballantana makama.

Jaridar Punch ta rawaito Arodiogbu na cewa babu wata hanya da tsohon gwamnan na Kano zai koma tafiya ɗaya da Atiku, duk da kyakkyawar mu’amalar da suka nuna a bikin zagayowar ranar haihuwar Kwankwaso makonni biyu da suka gabata.

Ya ce idan Kwankwaso zai yi wani sauyi, zai fi dacewa ya koma APC domin hakan zai fi amfani a siyasarsa, ya ce ko da Atiku ya yi yunƙurin bai wa Kwankwaso wata dama hakan ba zai yi wani tasiri ba.

NNPP ce za ta sake lashe zabe a jihar Kano – Shugabanta na Kasa Ajuji Ahmed

0

Shugaban jam’iyyar NNPP na Nijeriya Ajuji Ahmed, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta sake lashe zaben jihar Kano a 2027 duk da ficewar wasu ’yan majalisa daga cikinta.

Jaridar Punch ta rawaito Ajuji na cewa, rahotannin ficewar wasu mambobin majalisar wakilai daga jam’iyyar zuwa APC ba su rage damar da NNPP ke da shi ba, domin ficewar ta su jawo sababbin mambobi da dama suna shiga jam’iyyar musamman daga Kano.

Ficewar Abdulmumin Jibrin Kofa da Sagir Koki zuwa APC a ranar Alhamis ta biyo bayan karanta wasikunsu da kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas ya yi, inda suka zargi rikicin cikin gida na jam’iyyar NNPP a Kano a matsayin dalilin ficewar.

Sai dai Ahmed ya ce NNPP ba ta damu ba, domin suna samun sababbin mambobi masu yawa, yana mai bayar da tabbatacin cewa NNPP za ta ci gaba da rike Kano.

‘Yan bindiga sun halaka jigo a jam’iyyar APCn jihar Zamfara

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun halaka wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Umar Moriki da safiyar ranar Asabar.

Gidan talabijin na Channels, ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, kusa da garin Fegi a karamar hukumar Tsafe, yayin da Marigayin ke tafiya daga Gusau zuwa Kaduna.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC a jihar Zamfara Yusuf Idris ya fitar, jam’iyyar ta bayyana rasuwar Marigayi Moriki a matsayin babban rashi, inda ta ce ya halarci taron shugabannin jam’iyya da karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya jagoranta kafin aukuwar harin.

Marigayi Moriki ya taɓa rike mukamai da dama, ciki har da mataimakin shugaban karamar hukumar Zurmi da mai bai wa gwamna shawara kan hasken wutar lantarki a yankunan karkara, kazalika ya yi takarar kujerar majalisar wakilai ta Zurmi/Shinkafi a zaben 2023.

Jam’iyyar PDP ta kori su Wike daga cikinta

0

Jam’iyyar PDP mai hamayya a Nijeriya ta bayyana korar ministan birnin Abuja Nyesom Wike da wasu ‘ya’yanta daga cikinta.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin kudancin Nijeriya Cif Olabode George ne ya gabatar da kudurin korar yayin babban taron jam’iyyar da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Baya ga ministan Abuja Nyesom Wike, jam’iyyar ta kori tsohon sakatarenta Samuel Anyawu da tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wa’adina na biyu zai zama mai tsauri ga masu tu’ammali da miyagun kwayoyi – Buba Marwa

0

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, Janar Buba Marwa (rtd), ya bayyana cewa wa’adinsa na biyu zai zama mafi tsauri ga duk masu hada-hadar kwayoyi a fadin ƙasar.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a Abuja ranar Asabar, Marwa ya yi wannan gargadi ne yayin da ya koma ofis bayan sake nada shi da Shugaba Bola Tinubu a ranar 14 ga Nuwamban 2025.

Marwa, yayin da yake jawabi ga daruruwan ma’aikata da suka taru domin taya shi murna, ya ce sabon wa’adin na shi zai zama mai matukar kunci ga dilolin miyagun kwayoyi.

Majalisar dokokin Bénin ta amince da kara wa’adin mulki zuwa shekaru 7

0

’Yan majalisar dokokin Benin sun amince da sabuwar dokar gyaran kundin tsarin mulki da ke tsawaita wa’adin mulkin shugaban ƙasar daga shekaru biyar zuwa bakwai.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa duk da tsawaita zangon mulkin, tsarin zaben shugaba sau biyu bai sauya ba.

Sabon kundin tsarin mulkin ya zo ne yayin da Shugaba Patrice Talon ke shirin barin mulki a watan Afrilu bayan ya shafe shekaru goma yana jagorancin ƙasar.

A cewar majalisar, gyaran ya samu amincewar ’yan majalisa 90, yayin da 19 suka yi adawa da shi.

Na dauki matakin doka ne domin bin hakkina a PDP – Sule Lamido

0

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce ya kai kara kotu ne domin kare haƙƙinsa a jam’iyyar PDP, tare da jaddada cewa ba zai halarci taron babbar jam’iyyar da za a gudanar a karshen mako ba.

Lamido ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels inda ya yi bayani kan dalilan daukar matakin.

Ya kara da cewa matakin kotu da ya dauka ba ya da wata alaka da rikicin jam’iyyar, illa kawai neman adalci da gyaran kuskuren da aka yi masa ne.