DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 104

Hare-haren sojojin saman Nijeriya sun tarwatsa sansanin ’yan ta’adda a Zamfara

Rundunar sojin saman Nijeriya ta kaddamar da hare-hare na musamman kan sansanonin ‘yan bindiga, da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, wanda ya lalata wani muhimmin sansanin ’yan ta’adda a yankin.

A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar a shafinsa na X a ranar Asabar, ya ce harin ya gudana ne a ranar 14 ga Nuwamba 2025 ta hannun bangaren sojin sama na Operation Fansan Yamma.

Ejodame ya bayyana cewa luguden wutar ya biyo bayan cikakken binciken leken asiri da sa ido da ya tabbatar da tarin ’yan ta’adda da kuma dabbobin da suka sace a wani dutse da suke amfani da shi wajen boyewa da adana makamansu.

Shugaban mulkin sojin Nijar na ci gaba da ziyayar aiki a kasar

0

Mako guda kenan da shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya fara zagaye cikin mota a kasar

Tun a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba shugaba Tiani ya fara wani rangadi a cikin wadansu yankuna na jihohin kasar da ayarin motocinsa.

Shugaban na Nijar ya fara wannan zagaye ne daga jihar Dosso kafin daga bisani ya zarce Tahoua sai kuma jihar Agadez, yayin da ‘yan jihar Zinder ke dakon zuwan sa a wannan rana ta 15 ga watan Nuwamba.

Masu ruwa da tsaki dai na ganin wannan zagayen da shugaban ke yi na zama irin sa na farko da aka ga wani shugaba na yi a tarihin kasar.

Gwamnatin Nijeriya ta sha alwashin kawo karshen yawaitar faduwar layin wutar lantarki

0

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya karkashin Bola Ahmed Tinubu na aiki tukuru domin kawo karshen yawan faduwar layin wutar lanyarki da kuma tabbatar da tsayayyen hasken wutar a fadin kasar.

Adelabu ya bayyana haka ne a Uyo, jihar Akwa Ibom, yayin da yake ganawa da manema labarai inda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar wutar lantarki, Muhammadu Mamman.

Ministan ya ce tun zuwan Gwamnatin Tinubu an fara aiwatar da sabon tsari domin rage faduwar turakun wutar lantarki, tare da bullo da hanyoyin gudanar da harkokin wutar ta hanya cikin inganci.

Perez yana nan daram a Madrid – Fabrizio Romano

0

Shaharren dan jarida Fabrizio Romano ya bayyana cewa shugaban ƙungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Florentino Perez, bai da wani shirin barin kujerarsa duk da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta a kwanakin nan.

Rahotanni sun bayyana cewa an dade ana rade-radin Perez na iya sauka saboda matsin lamba da kuma batutuwan cikin gida na ƙungiyar ta Real Madrid.

Sai dai Fabrizio ya tabbatar da cewa abin da ake fada ba gaskiya bane, yana mai cewa shugaban na da burin ci gaba da gudanar da ayyukansa a kulob din da ya jagoranta na tsawon shekaru.

Gwamnonin PDP hudu sun isa Ibadan don gudanar da babban taron jam’iyyar

0

Gwamnonin PDP huɗu sun isa birnin Ibadan domin halartar babban taron kasa da jam’iyyar ta shirya, duk da hukuncin kotun tarayya da ta bayar na dakatar da taron.

Jaridar Punch, ta tabbatar da zuwan gwamnonin Bauchi, Bala Mohammed, Zamfara, Dauda Lawal, Adamawa, Ahmadu Fintiri, da na Oyo, Seyi Makinde, domin shirye-shiryen taron da ake son gudanarwa ranar Asabar 15 da Lahadi, 16 ga Nuwamba.

Jam’iyyar PDP na cikin rikici tsakanin bangaren Nyesom Wike da na shugaban riko Umar Damagum, yayin da kotuna daban-daban ke bayar da umarni mabambanta game da halaccin gudanar da taron.

A babbar kotun Abuja, mai shari’a Peter Lifu ya dakatar da taron bayan tsohon Gwamnan jigawa Sule Lamido, ya kai ƙara cewa an hana shi damar sayen fom ɗin takarar shugabancin jam’iyyar.

Likitoci sama da 4,000 sun bar Nijeriya a 2024 – Rahoto

0

Wani rahoto ya nuna cewa likitoci 4,193 ne suka fice daga Nijeriya don neman rayuwa mai inganci a shekarar 2024.

Labari mai alaka: Likita daya na duba marasa lafiya 9,083 in ji kungiyar likitoci a Nijeriya

 

Rahoton wanda ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar, ya kuma yi nuni da cewa jimillar likitoci, masu aikin jinya, kwararru a fannin magunguna da kuma masu gwaje-gwaje 43,221 ne suka fice daga ƙasar a tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Kazalika ya yi gargaɗin cewa karuwar ficewar kwararrun na iya zama babbar barazana ga fannin lafiya na kasar, inda ya yi nuni da muhimmancin kyautata rayuwarsu don ganin sun ci gaba da zama a Nijeriya tare da gudanar da ayyukan su yadda ya dace.

Gwamnan Kano ya rattaba hannu kan bukatar samar da kwalejin Polytechnic a Gaya

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa kwalejin kimiyya da fasaha “Gaya Polytechnic” a wani mataki na fadada damar samun ilimin gaba da sakandare tare da inganta koyon sana’o’in zamani a fadin jihar.

Mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana haka ne bayan rattaba hannun da ya samu halartar shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, da mataimakin shugaban majalisar, Hon. Muhammad Bello Butubutu, wadanda suka mika kudirin.

Gwamnan ya ce sabuwar kwalejin za ta bai wa matasa damarmaki na koyon horo da fasaha da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, kuma wannan shine burin gwamnati wajen fadada harkokin ilimi a fadin jihar Kano.

Ma’aikatan majalisa sun rufe majalisar dokokin jihar Bauchi sakamakon tsunduma yajin aiki 

0

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan majalisun jihohi ta Nijeriya (PASAN) a jihar Bauchi Adamu Yusuf ne ya sanar da hakan ranar Juma’a, bisa bin umarnin shugabancin ƙungiyar na kasa.

Yusuf ya ce yajin aikin na da nufin tilasta wa gwamnatin tarayya ta aiwatar da dokar ‘yancin kuɗi ga majalisun jihohi, wadda ake ganin za ta karfafa tsarin dimokuraɗiyya.

Ya yabawa Gwamna Bala Mohammed bisa matakin da ya ɗauka wajen tabbatar da ‘yancin kuɗi ga majalisar jihar, yana mai kiran gwamnati ta gaggauta aiwatar da dokokin da suka shafi walwalar ma’aikatan majalisu da tsarin mulki.

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta umarci a binciko dalilin rikicin da ya faru a lokacin zaben kasar

0

Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta umarci a binciko dalilin rikicin da ya faru a lokacin zaben kasar da ta sake yin nasara.

Wannan mataki ya biyo bayan zarge-zargen magudi da gallazawa daga gwamnati da ‘yan adawa suka yi, lamarin da ya haddasa zanga-zanga mai muni tare da rasa rayukan daruruwan mutane.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam da ‘yan adawa sun ce an halaka mutanen ne a lokacin da aka katse intanet baki ɗaya a kasar.

A jawabinta na farko a gaban majalisar bayan sake zabenta, Shugaba Samia ta umarci ‘yan sandan kasar da jami’an tsaro su sassauta wa matasa masu zanga-zanga.

Likitoci sun tsunduma yajin aiki kan karancin albashi a Ingila

Dubban likitoci a Ingila sun fara yajin aiki na kwanaki biyar a ranar Juma’a saboda rashin gamsuwa da albashi da kuma karancin guraben horaswa, lamarin da ya janyo tsaikon ayyuka a asibitocin da ke fadin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, wannan shi ne karo na 13 da likitocin ƙasar ke yin yajin aiki tun daga watan Maris din shekarar 2023.

Yajin aikin ya shafi ma’aikatan asibiti da ke kasa da kwararrun likitoci, wadanda su ke da kusan rabin yawan likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati.