Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 12

Mataimakin Sufeto na ‘yan sanda Frank Mba da wasu manyan jami’an ‘yan sanda za su yi ritaya

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (DIG), Frank Mba, tare da wasu manyan jami’a na shirin yin ritaya bayan sauye-sauyen shugabanci da aka yi a rundunar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sauyin ya biyo bayan sauke tsohon sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, da kuma nada sabon Sufeto Janar, Olatunji Disu, wanda aka rantsar a ranar Laraba a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda na 23 na Nijeriya.

Rahotanni daga hedikwatar rundunar sun nuna cewa manyan jami’an da ke kan mukamin DIG sun riga sun fara shirin barin ofisoshinsu, suna jiran sanarwar hukuma kafin su yi ritaya.

Hakan na zuwa ne yayin da ake shirin daga darajar wasu jami’ai daga mukamin mataimakin Sufeto Janar (AIG) zuwa DIG.

Gwamnatin Jigawa ta kori wasu masu samar da abincin azumi 22 kan zargin badakala a shirin ciyarwar watan Ramadan

Gwamnatin jihar Jigawa ta sallami wasu masu samar da abinci guda 22 da ke cikin shirin rabon abinci na watan Ramadan bisa zargin yaudara, rashin gaskiya da kuma wasu zarge-zargen almundahana wajen tafiyar da kudade.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa matakin na daga cikin yunkurin gwamnati na tabbatar da gaskiya da rikon amana a shirin da aka kaddamar domin ciyar da talakawa da marasa ƙarfi a watan Ramadan na shekarar 2026.

Gwamnan jihar, Umar Namadi, ne ya kaddamar da shirin wanda ke da niyyar ciyar da mutane kusan miliyan 7.9 a cibiyoyi 640 da aka ware domin rabon abinci a fadin jihar.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa bayan kusan makonni biyu da fara shirin, bincike da sa ido da aka gudanar tare da koke-koken jama’a sun gano wasu manyan laifuffuka daga wasu masu samar da abincin.

Kotu ta bada belin Abubakar Malami, matarsa da ɗansa kan miliyan 200 kowanne

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da beli ga tsohon Ministan Shari’a na tarayya, Abubakar Malami, da matarsa Asabe Bashir, tare da ɗansu Abdulaziz Malami.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin bayar da belin kan Naira miliyan 200 ga kowanne daga cikinsu tare da mutane biyu da za su tsaya musu.

Kotun ta kuma shar’anta cewa ɗaya daga cikin waɗanda za su tsaya musu dole ne ya ajiye takardun mallakar gida a unguwannin Maitama ko Asokoro, waɗanda ke cikin manyan unguwannin birnin Abuja.

Har ila yau kotun ta umarci waɗanda ake tuhuma da su miƙa fasfo dinsu na ƙasashen waje ga kotu.

Sai dai kotun ta ce har sai sun cika dukkan sharuddan belin, za su ci gaba da kasancewa a hannun hukumar kula da gidajen gyaran hali.

Ina da ƙwarin gwiwar lashe zaɓen gwamnan jihar Ogun a zaɓen 2027 – Iyabo Obasanjo

Tsohuwar Sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya Iyabo Obasanjo, ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar lashe zaben gwamnan jihar Ogun a 2027, tana mai cewa ita ce ‘yar takara mafi ƙarfi a fafatawar.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa Iyabo Obasanjo ta bayyana hakan ne a wata hira da ta yi, inda ta yi magana kan dawowarta siyasa, burinta na zama gwamna da kuma goyon bayan da take sa ran samu daga iyalanta.

Ta ce tana da yakinin cewa iyayenta, ciki har da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, za su zabe ta idan ta tsaya takara, ta ce a matsayinta na mace mai kusan shekaru 60, tana ganin ta yi sa’a kasancewar har yanzu tana da iyaye biyu da rai.

Messi ya kai wa Trump ziyara

Shugaban Amurka Donald Trump ya karɓi fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa Lionel Messi tare da takwarorinsa na ƙungiyar Inter Miami CF a fadar White House, domin karrama su bayan nasarar da suka samu ta lashe MLS Cup 2025.

An gudanar da taron ne a ranar Alhamis, inda Messi ya jagoranci ‘yan wasan ƙungiyar tare da kocinsu Javier Mascherano da kuma ɗaya daga cikin mamallaka kulob ɗin Jorge Mas wajen ganawa da Trump.

A jawabin da ya gabatar, Trump ya tuna da yadda fitaccen ɗan wasan Brazil Pelé ya taka leda a Amurka a shekarun 1970 lokacin da yake buga wa New York Cosmos, yana mai cewa tasirin sa ya taimaka wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa a Amurka,sai dai ya ƙara da cewa Messi ma na iya zama mafi kyau fiye da Pelé.

Za mu fara hukunta duk wani dan kasar waje da wa’adin bizarsa ya kare a Nijeriya kuma ya ci gaba da zama – Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa yanzu tana da cikakken tsarin gano tare da cafke baƙin ƙasashen waje da suka wuce wa’adin zaman da aka ba su a ƙasar.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin taron nazarin ayyukan ma’aikatar cikin gida na shekarar 2026.

Ministan ya ce gwamnati yanzu tana da cikakkun bayanan dukkan mutanen da suka shiga Nijeriya cikin shekaru goma da suka gabata, wanda hakan ke ba jami’an gwamnati damar gano waɗanda suka karya dokar zaman ƙasar.

Ya ce an samu wannan cigaba ne bayan kafa cibiyoyin kula da ayyuka na zamani a hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya.

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Tinubu Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce tasirin Obasanjo a Nijeriya Afirka da ma duniya baki ɗaya yana da girma sosai.

Shugaban ya jaddada cewa Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa ƙasa hidima, inda ya taba zama shugaban mulkin soja daga shekarar 1976 zuwa 1979, kafin ya miƙa mulki ga gwamnatin farar hula a 1979.

Haka kuma ya sake zama shugaban ƙasa na farar hula a jamhuriya ta huɗu daga 1999 zuwa 2007.

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci, saboda rikicin da ke ƙara tsananta a yankin gabas ta tsakiya kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

Rahoton wanda jaridar Bloomberg ta wallafa, ya ce an ɗauki matakin ne saboda yiwuwar samun ƙarancin makamashi sakamakon yaƙin da ke faruwa a yankin.

China na daga cikin manyan ƙasashen da ke shigar da danyen mai kasarta daga waje, kuma tana cikin ƙasashen Asiya da ke dogaro da mashigin ruwa na Hormuz wajen jigilar makamashi.

Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 bisa zarginsu da satar jarrabawa

Jami’ar tarayya da ke jihar Jigawa ta kori dalibai 20 tare da dakatar da wasu 15 daga karatu bisa samunsu da laifin satar jarabawa.

Rahotanni sun ce matakin ya biyo bayan shawarar kwamitin jami’ar da ke binciken laifukan jarrabawa na zangon karatu na biyu na shekarar 2024/2025.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktar harkokin ilimi ta jami’ar, Nora Dannatta ta sanya wa hannu, yayin da daraktan hulda da jama’a na makarantar, Abdullahi Yahaya-Bello, ya fitar da a birnin Dutse.

Sanarwar ta bayyana cewa majalisar jami’ar ta kuma wanke dalibai biyu daga zargin da ake musu, kazalika daliban da aka dau wannan matakin sun fito ne daga ɓangarori daban-daban na jami’ar.

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

0

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne a Jos bayan zaben Rufus Bature a matsayin shugaban jam’iyyar APC na jihar ta hanyar maslaha.

Gwamnan ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da zama karfi a jihar, yana mai kira ga mambobi su hada kai da sulhu domin karfafa tsari. Ya kuma sanar da shirin daukar sabbin mambobi na wata guda, inda ya bukaci kowane mamba ya jawo akalla mutum goma cikin jam’iyyar.

A jawabinsa na karbar mukami, Rufus Bature ya gode wa shugabanni da wakilai bisa amincewar da suka ba shi, yana mai alkawarin ci gaba da aiki tukuru domin dorewar nasarorin jam’iyyar a Plateau.