Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 13

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

0

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa.

Rubutun da ba a san marubucinsa ba ya bayyana shi a matsayin mutum mai shekaru 84, alhali Obasanjo zai cika shekaru 89 a ranar 5 ga Maris, 2026.

Da yake magana a wajen taron bikin cikarsa shekaru 89 a Abeokuta, Jihar Ogun, Obasanjo ya bayyana masu yada labarin a matsayin marasa aikin yi, yana mai cewa Allah Ya tabbatar masa da tsawon rai da karfin ci gaba da ayyukansa.

Daga karshe kuma ya ce, yana nan daram kamar yadda aka saba.

Ba ni da wani dan takara shafaffe da mai a 2027 bayan Tinubu – Uba Sani

0

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ba shi da dan takarar da ya fi so gabanin zabukan fidda gwani na 2027, yana mai cewa ba zai tsoma baki a tsarin zaben ’yan takara ba.

Uba Sani ya bayyana haka ne yayin buda baki da ’yan Majalisar Dokokin jihar, inda ya bukaci masu neman mukamai su nemi goyon bayan mambobin jam’iyya maimakon dogaro da uban gida. Ya ce zai mara wa duk wanda ya samu rinjaye a zabukan fidda gwani na APC.

Sai dai ya ce dan takarar da yake goyon baya shi ne Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2027.

Gwamnan ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyya su hada kai, yana mai cewa tsaro a Kaduna ya inganta tun bayan hawansa mulki a 2023.

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya ya kaddamar da kwamitin aiwatar da ‘yan sandan jihohi

Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya Tunji Disu, ya kaddamar da kwamitin mutum takwas domin aiwatar da tsarin kafa ’yan sandan jihohi, bayan amincewa da nadinsa a matsayin IGP na 23 a kasar.

Disu ya ce matakin na daga cikin manufofinsa na gyaran aikin ’yan sanda da karfafa tsaro a fadin kasa. An nada Farfesa Olu Ogunsakin a matsayin shugaban kwamitin.

Disu ya jaddada cewa shugabanci nauyi ne, ba mukami ba, yana mai kiran a sanya kwarewa da rikon amana tare da girmama hakkokin bil’adama a dukkanin ayyukan rundunar.

Nadin Disu ya biyo bayan amincewar Hukumar ‘Yan sanda da kuma nadin da Shugaba Tinubu ya yi masa bayan murabus din tsohon IGP, kuma ana sa ran rantsar da shi a hukumance yayin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Ofishin jakadancin Amurka ya soke neman biza a Abuja saboda fargabar zanga-zanga

0

Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya soke dukkan alƙawuran neman biza na ranar 4 ga Maris, 2026 a Abuja, sakamakon yiwuwar zanga-zanga da ka iya barkewa saboda rikicin Amurka da Iran.

Sanarwar da ofishin ya fitar ta ce akwai barazanar zanga-zanga a Babban Birnin Tarayya, don haka ta bukaci ’yan ƙasar Amurka da ke Abuja su zauna a gidajensu tare da kauce wa wuraren taro. Ta kuma ce za a tuntubi masu neman biza domin sake tsara musu sabuwar rana.

Matakin na zuwa ne bayan rahotannin mutuwar jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, lamarin da ya kara tsananta rikicin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ofishin ya jaddada cewa sashen jakadanci na Abuja da ofishin jakadanci a Legas za su ci gaba da aiki, tare da shawartar jama’a su rika bibiyar shafinsu domin samun karin bayani.

Kungiyar Kare Hakkin Dan’Adam ta nemi a sauya ranar tantance ’yan sanda saboda Ramadan

0

Kungiyar Kare Hakkin Dan’Adam ta nemi a sauya ranar tantance ’yan sanda saboda Ramadan

Kungiyar kare hakkin dan’Adam ta kasa da kasa (IHRC-RFT) ta bukaci a sake duba ranar tantance masu neman aikin dan sanda 50,000 da hukumar ‘yan sanda da rundunar ‘yan sandan Nijeriya suka shirya fara yi a ranar 9 ga Maris, 2026, sakamakon zuwan hakan daidai da watan Ramadan.

Kungiyar ta ce ta samu koke daga masu neman aikin cewa azumin Ramadan na iya jefa su cikin wahala, duba da irin gwajin jiki da ake yi a tantancewar. Ta roki shugabannin hukumomin tsaro da kwamitocin majalisa da su duba yiwuwar dagewa zuwa bayan Ramadan domin tabbatar da adalci da daidaito.

Kungiyar ta ce irin wannan mataki zai nuna girmama bambancin addini da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki kan daidaito da kare hakkokin jama’a.

Kotu ta dage shari’ar Abubakar Malami zuwa 10 Ga Maris

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami, da dansa Abdulaziz kan zargin tallafa wa ta’addanci zuwa ranar 10 ga Maris, 2026.

Dagewar ta biyo bayan bukatar shugaban masu gabatar da kararraki na Nijeriya, Rotimi Oyedepo, wanda ya ce an sauya shari’ar daga hannun DSS zuwa ofishinsa, don haka yana bukatar karin lokaci domin nazarin takardun karar.

Lauyan wadanda ake kara bai yi adawa da dagewar ba, amma ya bukaci kotu ta soke karar idan masu kara ba su fara gabatar da shaidu a ranar da aka sanya ba.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta amince da dagewar tare da umartar masu kara su fara shari’a a ranar da aka kayyade.

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da ziyarar ibada ta Kiristoci zuwa Isra’ila

0

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da dakatar da duk wata ziyara ta Kirista zuwa Isra’ila sakamakon halin tsaro a Gabas ta Tsakiya.

Hukumar kula da ziyarar ibada ta Kiristoci a Nijeriya (NCPC) ta bayyana hakan ta bakin Sakataren Zartarwarta, Bishop Stephen Adegbite, a wata sanarwa da aka fitar an Abuja.

Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci an Israel, tare da jaddada cewa tsaro da jin dadin mahajjata su ne a gaba. Dakatarwar ta shafi har da shirye-shiryen da kamfanoni masu zaman kansu ke gudanarwa har sai lamarin ya daidaita.

NCPC ta kuma bayyana cewa ta kammala aikin babban ziyarar 2025 zuwa Isra’ila da Jordan, inda rukuni na karshe ya iso lafiya a filin jirgin saman Murtala Muhammed a ranar 3 ga Maris.

Mata biyu da ke tsare a hannun ‘yan bindiga sun haihu a jihar Sokoto

0

Wasu mata biyu cikin mutum takwas da aka sace a kauyen Takatsaba da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto sun haifi jarirai namiji da mace yayin da suke tsare a hannun ’yan bindiga, makonni bakwai bayan sace su tare da wasu ’yan uwansu shida.

Wani dan uwan wadanda abin ya shafa ya ce maharan sun kai hari kauyen, sun yi ajalin wani dattijo sannan suka sace mutum takwas daga gida daya.

A cewarsa, an biya sama da Naira miliyan takwas daga cikin kudin fansa Naira miliyan goma da aka nema, yayin da uku daga cikin wadanda aka sace suka tsere kuma yanzu suna karbar magani a Sabon Birni.

Hakazalika, ya yi kira ga hukumomin tsaro su kara kaimi a yankin, amma kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar ya ce ba su da rahoton faruwar lamarin saboda ba a kai musu kara ba.

Jihohin APC sun sake mara wa Tinubu baya matsayin dan takara a zaɓen 2027

Jam’iyyar APC a jihohi da dama ta sake bayyana goyon bayanta ga shugaba Bola Tinubu, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Rahoton Daily Trust ya ce tarukan zaɓen shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a jihohi da dama ranar Talata sun jaddada wannan matsaya, inda jihohi kamar Kaduna, Gombe, Kebbi, Taraba da Edo suka sabunta kiran Tinubu ya tsaya takara karo na biyu.

A jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani ya ce jam’iyyar za ta hada kai domin tabbatar da nasara daga matakin mazabu har sama.

Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya bukaci sabbin shugabannin APC na jihar su samar wa Tinubu akalla kuri’u miliyan biyu a 2027.

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

0

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, gaban kotu ba, duk da an yi masa tambayoyi tsawon kwanaki uku kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Daily Nigerian ta rawaito cewa, hukumar ta tsare El-Rufai a hannunta na tsawon kwanaki biyu, daga ranar 16 zuwa 18 ga Fabrairu, bisa zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa.

Wata majiya daga cikin hukumar ta shaida wa NAN cewa haryanzu ana ci gaba da binciken tsohon gwamnan, shi ya sa ba a kai shi gaban kotu ba tukuna.

Majiyar ta ƙara da cewa EFCC ba za ta yi gaggawar shigar da ƙara a kotu ba kan zargin da ta ke yi, sai ta kammala cikakken bincike cikin ƙwarewa da bin ƙa’ida.