Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 14

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

0

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar ‘yan sandan kasar a matsayin IGP na 23.

A cewar fadar shugaban Nijeriya, zai gudanar da aikin ne a matsayin muƙaddashi  har sai an tantance shi kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Takaitaccen Tarihin Sa

  • Haihuwa: An haife shi a ranar 13 ga Afrilu, 1966, a Jihar Legas.
  • Karatu: Yana da digiri a fannin Turanci (English Education) daga Jami’ar Jihar Legas (LASU). Sannan yana da digiri na biyu (Masters) guda biyu: daya a fannin Gudanarwa (Public Administration) daga Jami’ar Adekunle Ajasin, daya kuma a fannin Kimiyyar Laifuka (Criminology) daga LASU.
  • Fannin Kwarewa: Ya halarci kwasa-kwasai da dama a gida da waje kan yaki da fataucin makamai, zambar intanet (internet fraud), da binciken kimiya na gano masu laifi (forensics).
  • Disu ya shiga aikin dan sanda ne a shekarar 1992 a matsayin babban jami’i (Cadet ASP), inda ya samu horo a Makarantar Horon ‘Yan Sanda ta Wudil da ke Jihar Kano.
  • Ga wasu daga cikin manyan mukaman da ya rike:
  • AIG FCID Alagbon: Kafin nadinsa na yanzu, shi ne Mataimakin Sufeto Janar mai kula da sashin binciken manyan laifuka a Legas.
  • Kwamishinan ‘Yan Sanda (CP): Ya taba rike rundunar ‘yan sanda ta Abuja (FCT) a 2024 da ta Jihar Rivers a 2023.
  • Kwamandan IRT: Shi ne ya gaji Abba Kyari a matsayin shugaban tawagar gano masu laifi (Intelligence Response Team) a shekarar 2021.
  • Kwamandan RRS: Ya taba jagorantar rundunar gaggawa (Rapid Response Squad) ta Jihar Legas.
  • Babban Jami’i ga IGP: Ya taba zama Principal Staff Officer ga tsohon IGP Egbetokun.

Me Ya Faru da IGP Kayode Egbetokun?


An nada Egbetokun ne a matsayin wanda ya gaji Usman Alkali Baba. Ko da yake ya kamata ya yi ritaya a ranar 4 ga Satumba, 2024 (lokacin da ya cika shekaru 60), sai dai gyaran da aka yi wa dokar ‘yan sanda ya ba shi damar ci gaba da wa’adin shekaru hudu, wanda hakan zai kai shi har zuwa watan Oktoba, 2027.

Sai dai, ya yi murabus sakamakon wasu dalilai, inda fadar shugaban Nijeriya ta sanar da nadin Disu domin ya jagoranci rundunar yan sandan Nijeriya.

Shugaba Tinubu ya amince da naɗa Tunji Disu, a matsayin babban Sufeton ‘Yan Sanda na riƙo

0

Shugaban Tinubu ya karɓi murabus ɗin Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, bayan mika masa wasiƙar murabus da ya yi tare da naɗa Tunji Disu a matsayin sabon shugaban ‘yan sanda na riko.

Shugaba Tinubu ya nuna godiya matuƙa ga Egbetokun bisa tsawon shekaru da ya yi yana hidima, nagarta da jajircewa da ya yi ga rundunar ‘yan sanda da Nijeriya baki ɗaya.

Shugaban ya amince da naɗa mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda Tunji Disu a matsayin Sufeto Janar na ‘yan sanda na riƙo, wanda zai fara aiki nan take.

Kotu ta amince da a gurfanar da mutanen da ake zargi da alaka da Bello Turji 

0

Kotun tarayya da ke Abuja ta amince da buƙatar Gwamnati na gurfanar da mutane biyar da ake zargi da alaƙa da fitaccen dan bindiga Bello Turji, bayan sun ƙi bayyana a gaban kotu sau uku a jere duk da sammacin da aka kai.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukunci bayan lauyan gwamnatin tarayya, ya nemi a aiwatar da tanadin Sashe na 352(4) na dokar gudanar da Shari’ar laifuka (ACJA) ta 2015, ganin cewa ba a samu waɗanda ake tuhuma ba duk da umarnin kama su.

Kotun ta bayyana cewa duk da fitar da sammacin kama mutanen, jami’an tsaro sun kasa gano inda suke domin gurfanar da su, sakamakon haka, alƙalin ya amince da a ci gaba da shari’ar ba tare da halartar su ba, tare da ɗaga sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga Afrilu domin ci gaba da gabatar da shaidu.

Gwamnatin Tinubu ta musanta biyan kudin fansa don ceto daliban Papiri jihar Neja

0

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa zargin da ke yawo a wasu rahotannin kafafen yada labarai na duniya na cewa an biya kaso mai tsoka na kudin fansa domin ceto daliban da aka sace daga makarantar St. Mary’s a Jihar Niger, ba gaskiya ba ne, sannan rahotannin ba su da tushe.

Ministan Yada Labaran kasar Mohammed Idris, ya ce babu wasu kudin fansa da aka biya, kuma babu wani kwamandan ‘yan ta’adda da aka saki. Ministan ya jaddada cewa hukumomin tsaro sun musanta irin wadannan ikirari tun da farko.

Ya ambaci Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), da shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa, yana mai cewa duk sun fito karara sun musanta batun biyan kudin fansa.

Gwamnatin ta ce nasarar ceto daliban ba tare da asarar rai ba, sakamakon aikin leken asiri da tsare-tsaren soji ne. Ta kuma gargadi kafafen yada labarai da su rika tantance sahihancin bayanai kafin wallafawa, tana mai cewa rahotannin da ba su da tabbaci na iya karfafa gwiwar masu aikata laifi ko rage kwarin gwiwar jami’an tsaro.

Atiku ya buƙaci Gwamnatin Nijeriya da ta bayyana dalilin tsare El-Rufai

0

Madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar, ya buƙaci Gwamnatin kasar da ta ta bayyana dalilin tsare tsohon Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa rahotannin da ke nuna cewa lafiyarsa na fuskantar barazana, tare hana iyalansa da lauyoyinsa damar ganinsa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Atiku ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa ga iyalai, abokai da masu goyon bayan El-Rufai, yana mai cewa Gwamnatin Nijeriya na da alhakin bayyana dalilin da yasa hukuma ke tsare shi.

Atiku ya ce hakan na ƙara haifar da shakku a zukatan jama’a, tare da jaddada cewa kundin tsarin mulki ya tanadi kare mutunci, lafiyar wanda ake tsare da shi, da ba shi damar samun kulawar lafiya.

An tilasta wa IGP Kayode Egbetokun yin murabus daga mukaminsa – Premium times

Rahotanni na nuni da cewa an tilasta wa Sufeto Janar na ‘yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, yin murabus daga muƙaminsa bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda majiyoyi daga fadar shugaban ƙasar suka tabbatar.

Jaridar Premium times ta rawaito cewa majiyar ta ce an bukaci Egbetokun ya ajiye muƙaminsa ne a wani taro da aka yi da shugaban ƙasa a fadarsa a ranar Litinin.

An kuma bayyana cewa ana shirin nada mataimakin Sufeto Janar na ‘yan Sanda AIG, Tunji Disu, domin maye gurbinsa, amma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto ba a fitar da sanarwar nadin nasa a hukumance ba.

Nijeriya ta zamo ta biyar a ƙasashen da suka fi ƙwarewa a harshen Turanci a nahiyar Afrika

0

A wani rahoto da EF SET na shekarar 2025 ta fitar kasar Afirka ta Kudu ce ta ke kan gaba a jerin ƙasashen Afirka wajen ƙwarewar harshen Turanci.

Rahoton ya nuna cewa ƙididdigar ta dogara ne kan sakamakon kusan miliyan 2.2 daga ƙasashe da yankuna 123 na duniya da suka shiga tsarin.

A kasashen Afrika Zimbabwe ce ta zo ta biyu a kasashen da ke da kwarewa wajen harshen Turanci,Kenya ta zo ta uku,Zambia ta hudu yayinda Nijeriya ta zamo ta biyar a cikin jerin da EF SET ta fitar.

Majalisar Wakilan Nijeriya ta ɗage komawar zaman majalisa zuwa 5 ga Maris

0

Majalisar Wakilan Nijeriya, ta ɗage komawar zaman majalisa daga Talata, 24 ga Fabrairu 2026, zuwa Alhamis, 5 ga Maris 2026.

Sakataren Majalisar, Kamoru Ogunlana, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin bai wa kwamitoci damar kammala zaman kare kasafin kuɗi da suke yi.

A cewarsa, an ɗage komawar zaman ne saboda buƙatar kwamitocin majalisar su kammala tattaunawa da ma’aikatun gwamnati, hukumomi da cibiyoyi, kan kasafin kuɗin shekarar 2026.

Jam’iyyar APC za ta iya amincewa da Yilwatda da Ajibola Basiru a babban taron ta

0

Wasu rahotanni na nuni da cewa jam’iyyar APC na dab da amincewa da ci gaba da rike mukaman shugabancin jam’iyyar na ƙasa Yilwatda da sakataren ta na kasa Ajibola Basiru a taron da jam’iyyar ke shirin gudanarwa.

Jaridar Punch ta ce rahotanni daga cikin jam’iyyar sun nuna cewa manyan jiga-jigan APC na karkata ga ci gaba da riƙe waɗannan shugabanni biyu a mukamansu, ganin rawar da suka taka wajen daidaita harkokin jam’iyyar da rage rikice-rikicen cikin gida.

An ce tsarin zai taimaka wajen gujewa rigingimu masu zafi da ka iya raba kawunan jam’iyyar a gaban babban taron ƙasa.

Hukumar alhazan Nijeriya NAHCON ta umurci jihohi su mayar wa maniyyatan da ba a yi musu rajista ba kuɗaɗensu

0

Hukumar alhazan Nijeriya NAHCON, ta umarci hukumomin kula da aikin hajji na jihohi da su mayar wa maniyyatan da ba a kammala musu rajista ba kuɗin da suka biya domin aikin hajjin 2026, sakamakon raguwar adadin kujerun aikin hajji da kuma tsauraran ka’idojin biza daga Saudiyya.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana cewa raguwar kujerun aikin hajjin da aka ware wa Nijeriya, tare da gajeren wa’adin kammala biza da Saudiyya ta sanya, sun tilasta wa NAHCON daukar matakin da zai kare hakkin maniyyata da ba su samu damar kammala rajista ba.

NAHCON ta bukaci hukumomin jihohi da su tabbatar da anbi hanyoyin da suka dace wajen mayar da kuɗin, tare da sanar da maniyyata hanyoyin karɓar kuɗinsu ba tare da jinkiri ba.