Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 18

DSS za su gurfanar da Elrufa’i gaban kuliya a ranar 25 ga Fabrairu

Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya , SSS ta ce za ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna State, Nasir El-Rufai, a gaban kotu ranar 25 ga Fabrairu, bisa zargin aikata laifukan intanet.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeri NAN, ya rawaito mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta saka ranar shari’ar bayan babban alkalin kotun tarayya, mai shari’a John Tsoho, ya mika mata shari’ar.

DSS ta shigar da tuhume tuhume uku kan El-Rufai bisa zargin yin kutse a kiran wayar mai ba shugaba Tinubu shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu.

A wata hira da El-rufa’i ya yi a gidan talabijin na Arise a kwanakin baya, ya ce shi da wasu suna sauraron kiran wayar Nuhu Ribadu abinda wasu ke ganin hakan na barazana ga tsaron kasa.

ICPC na bin diddigin ayyukan mazaɓu na Naira biliyan 13.5 a Katsina

0

Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta kaddamar da Mataki na 8 na shirin bibiyar ayyukan mazabu da na sashen zartarwa a Jihar Katsina, inda ake sa ido kan jimillar ayyuka 39 da kudinsu ya kai naira biliyan 13.5 a yankunan sanatoci da mazabun tarayya na jihar.

A cewar hukumar, tawagar bibiyar ayyukan ta hada da manyan jami’ai daga hedikwata da ofishin Katsina.

Hukumar ta ce ana gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar Nigerian Institute of Quantity Surveyors da kafafen yada labarai domin tabbatar da inganci, amfani da kudi yadda ya dace, da bin ka’idojin ayyuka.

Tuni an duba ayyukan cibiyoyin lafiya a birnin Katsina, hanyoyi a Funtua da Kankia, da ayyukan samar da ruwa a Kurfi, Dutsin-Ma, Mashi da Dutsi. Haka kuma an bibiyi ayyukan makarantu a Kafur, Sandamu, Daura da Mai’Adua, tare da fitilun kan tituna na hasken rana da shirye-shiryen tallafa wa al’umma.

Hukumar ta ce shirin na gudana karkashin kulawar kwamishinan da ke kula da jihar Katsina, Mr Ludam S. Samuel, a wani yunkuri na kara habaka gaskiya da rikon amana a ayyukan gwamnati.

Zan fi so Arsenal ta dauki gasar Firimiyar kasar Ingila maimakon kungiyar Manchester City – Wayne Rooney

0

Tsohon kyaftin ɗin kungiya Manchester United, Wayne Rooney, ya bayyana cewa zai fi so ya ga Arsenal ta lashe kofin Premier League a bana, maimakon Manchester City ko Liverpool.

Ya ce dangantakarsa da tsohuwar ƙungiyarsa ta Manchester United na shafar wannan ra’ayi, musamman idan aka kwatanta da Liverpool.

Rooney ya amince da irin nasarar da Man City ke yi a ƙarƙashin jagorancin Pep Guardiola, amma ya nuna cewa gasar kakar nan na da matuƙar tsauri, kuma wasannin da za su haɗu da manyan ƙungiyoyin musamman idan Arsenal da Man City suka haɗu a gasar UEFA Champions League za su taka muhimmiyar rawa wajen tantance wanda zai ɗaga kofin.

’Yan bindiga sun yi ajalin mutane 33 a jihar Kebbi

0

Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 33 sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Bui da ke karamar hukumar Arewa ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa bincike ya nuna maharan na shigowa yankin ne daga karamar hukumae Gudu da ke jihar Sokoto State.

Ya ce bayan harin, mazauna ƙauyukan Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal da Dan Mai Ago sun tashi tsaye domin kare kansu, abin da ya jawo artabu mai tsanani da ya yi sanadin mutuwar mutane 33.

A cewar sa ’yan sandan tare da sojoji da sauran hukumomin tsaro sun ƙara tura jami’ai da kayan aiki zuwa yankin, tare da ci gaba da sintiri domin dawo da zaman lafiya da hana sake faruwar irin wannan hari.

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya roki ‘yan kasar da su rika sanya Tinubu cikin addu’o’insu

0

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bukaci ‘yan kasar da su rika sanya Shugaba Bola Ahmed Tinubu a cikin addu’o’insu yayin da Musulmi ke gudanar da Ramadan, Kiristoci kuma ke azumin Lent.

A cikin wata sanarwa da mataimakinsa kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, Shettima ya ce wannan lokaci mai tsarki na ibada ya kamata ya zama dama ta roƙon Allah ya bai wa Tinubu hikima, ƙarfi da hangen nesa domin tafiyar da al’amuran ƙasa yadda ya dace, musamman a wannan lokaci na sauye-sauyen manufofi da ƙalubalen shugabanci.

Ya jaddada cewa haɗuwar Ramadan da Lent a lokaci guda dama ce ta haɗa kai wajen yin addu’a domin shugabanci nagari, zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Rundunar sojin Nijeriya za ta ɗauki nauyin karatun ‘ya’yan sojojin da suka rasa rayukansu

0

Sojojin Nijeriya sun sanar da fara taron tantance yara da ‘yan uwan sojoji da suka rasu, a cikin wani shiri na bayar da tallafin ilimi na shekarar 2026.

A wata sanarwar rundunar sojin ta wallafa a shafin ta na X ranar Alhamis, an bayyana cewa tantancewar za ta gudana a dukkanin yankuna shida na Nijeriya tsakanin Fabrairu da Maris 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa, shirin tallafin ilimi na daga cikin tsare-tsaren jin kai na Sojojin Nijeriya da nufin tabbatar da cewa yaran ma’aikatan da suka rasu suna samun ilimi a matakai na Firamare, Sakandare da Jami’a.

Kasar Sierra Leone, ta karrama babban hafsan tsaron Nijeriya Olufemi Oluyede da lambar yabo

0

Shugaban ƙasar Sierra Leone, Julius Maada Bio, ya karrama babban hafsan tsaron Nijeriya CDS, Janar Olufemi Oluyede, da lambar yabo ta Grand Commander of the Order of the Rokel.

An ba Oluyede wannan lambar yabone a wani gagarumin faretin sojoji da aka gudanar, yayin gagarumin bikin sojoji da aka gudanar, kamar yadda daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya sanar a ranar Alhamis.

Baya ga karrama CDS na Nijeriya, an kuma bai wa wasu fitattun mutane daga Nijeriya, Guinea, Birtaniya, Amurka da Kenya lambobin yabo a wajen bikin.

Gwamnatin Yobe ta sassauta dokar hana fitar dare

0

Mai ba Gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Dahiru Abdulsalam, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron tsaro da mataimakin Gwamnan jihar, Idi Barde Gubana, ya jagoranta.

A cewarsa, kwamitin tsaron jihar ya ga dacewar sassauta dokar ne domin bai wa Musulmi damar gudanar da ayyukan addini cikin sauƙi a lokacin azumi.

Ya bayyana cewa an kira taron tsaron ne domin tantance yanayin tsaro a faɗin jihar, tare da tabbatar da cewa al’umma sun gudanar da kwanaki 30 na azumi cikin lumana, tare da kare rayuka da dukiyoyinsu yadda ya kamata.

Majalisar dokokin jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige Fubara

0

An dauki matakin dakatar da shirin tsige gwamnan ne a yayin zaman majalisar da ke gudana a birnin Fatakwal na jihar ta Rivers.

Tun da fari, majalisar ta soma shirin tsige Gwamna Fubara da mataimakiyarsa bisa zargin aikata manyan laifuffuka da suka haɗa da rushe ginin majalisar dokoki da kashe kuɗaɗe ba tare da amincewar majalisa ba, da sauran zarge-zarge.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule, ne ya jagoranci zaman da aka dakatar da shirin.

‘Yan sanda a Ingila sun cafke dan’uwan Sarki Charles

0

An kama Prince Andrew, tsohon yariman Birtaniya kuma kanin King Charles III, bisa zargin aikata laifin cin amana lokacin da yake riƙe da mukamin gwamnati.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun dauki matakin ne yayin da suke binciken zargin cewa ya miƙa wasu bayanan sirri da aka ce na gwamnati da Jeffrey Epstein, wanda aka taba samu da laifukan lalata.