Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 19

‘Yan bindiga sun sace matafiya shida a kusa da Makurdi, tare da neman a biyasu Miliyan 100

0

Sojojin Nijeriya sun sanar da fara taron tantance yara da ‘yan uwan sojoji da suka rasu, a cikin wani shiri na bayar da tallafin ilimi na shekarar 2026.

A wata sanarwar rundunar sojin ta wallafa a shafin ta na X ranar Alhamis, an bayyana cewa tantancewar za ta gudana a dukkanin yankuna shida na Nijeriya tsakanin Fabrairu da Maris 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa, shirin tallafin ilimi na daga cikin tsare-tsaren jin kai na Sojojin Nijeriya da nufin tabbatar da cewa yaran ma’aikatan da suka rasu suna samun ilimi a matakai na Firamare, Sakandare da Jami’a.

Mune ke tsare da Elrufa’i, in ji hukumar ICPC

0

Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana cewa tana tsare da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai.

Hukumar ta ce El-Rufai yana hannunta har bayan an tashi aiki na ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026.

A wata sanarwa da kakakin hukumar, J. Okor Odey, ya fitar, ICPC ta ce ana rike da shi ne dangane da bincike da take gudanarwa.

Kotu ta yi wa tsohon shugaban Koriya ta Kudu ɗaurin rai da rai kan haddasa bore

0

Kotun ta yanke hukunci ga tsohon shugaban kasar Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yoel ne a ranar Alhamis, bayan samunsa da laifin jagorantar yunƙurin tayar da bore ta hanyar ayyana dokar ta-ɓaci a shekarar 2024.

Yoon ya bayyana dokar ta-ɓaci ne kwatsam a wani jawabi da yayi a gidan Talabijin a watan Disambar 2024, inda ya ce akwai buƙatar ɗaukar tsauraran matakai domin kawar da ƙungiyoyin da ke adawa da ƙasa a majalisar dokokin ƙasar.

Tsohon shugaban mai shekaru 65, wanda aka tube daga muƙaminsa, daga bisani aka kama shi tare da gurfanar da shi a kan jerin tuhuma da suka haɗa da tayar da bore da hana aiki ga hukumomin shari’a.

Alkalin da ya jagoranci shari’ar, Ji Gwi-yeon, ya ce Yoon ya tura sojoji zuwa ginin majalisar dokoki ne domin murƙushe abokan hamayyarsa na siyasa, waɗanda ke hana shi aiwatar da manufofinsa.

Tinubu ya taya kiristoci da musulmi murnar fara azumin Lent da Ramadana

0

Fadar Shugaban kasa ce ta fitar da sanarwar inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon gaisuwa ga kiristoci da musulmi bisa fara azumin Lent da Ramadan a lokaci guda.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya kiristoci da musulmi murnar fara azumin Lent da Ramadan, wadanda suka zo a rana guda a bana.

Ya ce lokutan ibadun suna tunatar da ‘yan kasa muhimmancin imani, sadaukarwa da kaunar juna, tare da bukatar zaman lafiya, hadin kai da addu’ar cigaban kasa.

Shugaban ya yi fatan darussa da albarkatun wadannan lokuta masu tsarki su dawwama a rayuwar al’umma.

Darajar Naira za ta iya dagawa zuwa ₦1,100 kan dala a 2026 – Dangote

0

Sanannen dan kasuwa a Afrika Aliko Dangote, ya ce ana sa ran darajar naira za ta iya dagawa zuwa kusan ₦1,100 kan dala ɗaya a shekarar 2026, idan sauye-sauyen tattalin arziƙi da rage dogaro da shigo da kaya daga waje suka ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Dangote ya faɗi hakan ne a lokacin ƙaddamar da wani shiri da aka kaddamar kan masana’antu na 2025, inda ya jaddada muhimmancin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida domin rage buƙatar dala daga waje.

Ya bayyana cewa farfadowar naira da ake gani a ‘yan makonnin nan na da alaƙa da manufofin gwamnati na ƙarfafa masana’antu da kuma rage shigo da kayayyaki, musamman man fetur da wasu muhimman kayayyaki.

Gwamnatin Kano ta umurci a rufe dukkan wuraren taro da gidajen Gala

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta bayar da umarnin rufe dukkan wuraren wasanni a fadin jihar, ciki har da wuraren taro da gidajen Gala.

Hukumar ta ce an dauki wannan mataki ne domin bai wa al’umma damar gudanar da azumi da ibadunsu cikin kwanciyar hankali ba tare da hayaniya ba.

Zanga-zangar kyamatar ‘yan Arewa ta yi ajalin Hausawa 4 a Port Harcourt jihar Rivers

0

Kungiyar Hausawa mazauna Jihar Rivers ta bayyana cewa mambobinta hudu sun hadu da ajalinsu a yayin zanga-zangar da ta gudana a karshen makon da ya gabata, wadda aka ce ta shafi ‘yan Arewa a Kasuwar Oil Mill da ke yankin Rumuokwurusi a Port Harcourt.

Shugaban Kungiyar Hausawan Jihar Rivers, Alhaji Musa Saidu, ne ya bayyana hakan a ranar Talata lokacin da ya jagoranci wasu shugabannin Arewa zuwa kasuwar domin duba halin da ake ciki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Ya kuma ce an wawashe tare da lalata shaguna da dama mallakin ‘yan kasuwar Arewa a lokacin tashin hankalin

Vinícius Jr ya yi martani kan nuna masa wariyar launin fata a wasan da Real Madrid suka yi da Benfica

0

Dan wasan gaba na Real Madrid, Vinícius Júnior, ya mayar da martani kan cin zarafin wariyar launin fata da ake zargin an yi masa a wasan gasar zakarun nahiyar Turai tsakanin Benfica da Real Madrid.

Rahotanni sun ce Vinícius ya kai korafi ga alkalin wasa, François Letexier, kan kalaman wariya da aka yi masa daga wasu magoya baya.

Bayan haka, ‘yan wasan Real Madrid sun fice daga filin wasan domin nuna adawa da abin da ya faru, daga bisani, an dakatar da wasan na tsawon mintuna 10 kafin a ci gaba da buga shi.

An samu hayaniya a Majalisar wakilan Nijeriya bayan wasu ‘yan majalisa sun ƙi amincewa da janye ƙudurin gyaran dokar zaɓe ta 2025

0

An ce yunƙurin janye ƙudurin ya janyo cece kuce a yayin zaman majalisar na ranar Talata.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa hayaniyar ta fara ne lokacin da shugaban kwamitin harkokin majalisa, Francis Waive, ya gabatar da buƙatar a janye amincewar da aka yi wa kudurin.

Ya ce an yi hakan ne domin a sake duba dokar don dacewa da sabbin gyare gyaren tsarin gudanar da zaɓe.

Francis Waive ya roƙi ‘yan majalisa sun janye wancan amincewa domin a mayar da kudurin gaban kwamitin don sake yin nazari akai.

Bankin CBN ya yi gargadin hukunta masu wulakanta Naira

0

Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya ƙara tsaurara matakan da yake ɗauka kan masu wulakanta takardar kuɗin Naira, inda ya yi gargaɗi ga ‘yan ƙasa da su daina liƙin kuɗi a wuraren bukukuwa, lalata su, yin jabun kuɗi ko kuma safararsu ba bisa ka’ida ba.

Bankin ya bayyana hakan ne a wajen Baje Kolin Kasuwanci na Ƙasa da Ƙasa na Kaduna, inda ya kuma yi bayani kan muhimman nasarorin da aka samu a ƙarƙashin shirye-shiryen gyaran da yake aiwatarwa.

Mataimakiyar Darakta a Sashen Hulɗa da Jama’a da Zuba Jari ta CBN, Mrs. Sidi Ali Hakama, ta ce girmama Naira wajibi ne a doka da ta ƙasa, tana mai bayyana kuɗin a matsayin alamar martabar Nijeriya.

Ta samu wakilci daga Mataimakin Darakta a Hedikwatar CBN da ke Abuja, Abbas Ibrahim Ahmed.