Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 20

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta nuna rashin gamsuwa da hukumar Hisbah da aka kafa a jihar Neja

0

Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar Neja, CAN, ta bayyana rashin gamsuwa da kudurin dokar Hisbah da majalisar dokokin jihar ke shirin amincewa da ita inda tace hakan na nuna wariya da nuna bambanci ga Kiristoci.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa CAN ta ce dokar za ta ƙara raba kan al’umma da ke addini daban-daban a jihar, maimakon ta ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai.

Shugaban CAN na jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, ya yi gargadin cewa kudurin dokar hukumar Hisbah wanda ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Chanchaga, Mohammed Abubakar, ya gabatar, na iya jawo cece-kuce kuma bai kamata bangaren zartarwa ya amince da shi ba.

Hukumar ICPC ta fara bibiyar ayyukan da suka lakume sama da Naira biliyan 21 a jihar Sokoto

0

Hukumar ICPC mai yaki da ayyukan rashawa a Nijeriya ta fara bibiyar ayyuka 64, na ‘yan majalisa da aka kiyasta kuɗinsu kimanin Naira biliyan 21.6 a jihar Sokoto.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa wannan bincike na karkashin mataki na 8 a shirin ICPC na bibiyar ayyukan ‘yan majalisa wanda ake aiwatarwa a jihohi daban-daban na ƙasar.

Shugaban tawagar binciken, Aminu Bala, ya bayyana cewa za su duba ayyuka a fannoni daban-daban kamar kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwan sha, noma, da kuma lantarki.

A cewarsa, sun gano kura-kurai a wasu ayyuka da aka aiwatar a Kalambaina da Gwuiwa a karamar hukumar Wamakko, da kuma Mabera da Mana a Sokoto ta Kudu.

Gwamnatin Nijeriya ta yi karar El-rufa’i kan zargin kutse a wayar Nuhu Ribadu

Gwamnatin Nijeriya ta shigar da karar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin yin kutse kiran wayar mai ba Shugaba Tinubu shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa an shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CR/99/2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A yayin wata hira da yayi El-Rufai ya bayyana cewa ya san mutanen da suka yi kutse a wayar Ribadu, amma bai kai rahoto ga hukumomin tsaro ba, abin da ya saba wa Sashi na 27(b) na dokar Cybercrimes ta 2024.

Sanata Shehu Sani ya bukaci hukumar EFCC ta binciki zamanin mulkin El-Rufai a jihar Kaduna

0

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bukaci hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci su gudanar da cikakken bincike kan wa’adin shekaru takwas na tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin almundahana da cin zarafi.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito cewa Shehu ya yi wannan kira ne yayin taron manema labarai a Kaduna, inda ya bukaci hukumomin su binciki abin da ya kira karkatar da kudaden al’umma da suka kai daruruwan biliyoyin naira a tsakanin 2015 zuwa 2023.

Ya kuma yi kira ga hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta Nijeriya EFCC, da ta dauki mataki kan rahotannin da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar na zargin aikata ba daidai ba, domin tabbatar da adalci.

Ku sanya ido sosai kan zaben da za a gudanar a 2027 – Kiran Peter Obi ga ‘yan Nijeriya

0

Tsohon ɗan takarar shugabacin Nijeriya Peter Obi, ya yi kira ga ’yan kasar da su kasance masu sa ido sosai a zaɓen 2027, yana jaddada cewa dole ne kowace ƙuri’a a kirga ta, tare da yin gargaɗi ga duk wanda zai yi ƙoƙarin kawo cikas ga sahihin zaɓe.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Obi ya wallafa saƙon ne a shafinsa na X, inda ya bukaci masu jefa ƙuri’a su tsaya a rumfunan zaɓe bayan sun kaɗa ƙuri’unsu domin su shaida an ƙirga da kuma tura sakamakon zuwa hukumomi.

Obi ya ce halartar jama’a da sa ido a rumfunan zaɓe na da matuƙar muhimmanci wajen kare dimokiraɗiyya da hana maguɗin zaɓe.

Majalisar dokokin Nijeriya na shirin sauya ranar zaben 2027 zuwa 13 ga watan Fabarairu – Punch

0

Majalisar Dokokin Nijeriya ta sanar da cewa za ta yi zama na gaggawa a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, domin duba yiwuwar sauya ranar da aka sanya zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Jaridar Punch ta rawaito cewa majalisar na shirin matsar da ranar zaɓen shugaban ƙasar daga 20 ga Fabrairu zuwa 13 ga Fabrairu, 2027, bayan samun korafe-korafe daga masu ruwa da tsaki.

A wata sanarwa da magatakardan majalisar, Kamoru Ogunlana ya fitar, an umarci sanatoci da ‘yan majalisar wakilai su koma a ranar Talata, domin daukar matakai da ke da muhimmanci.

A binciki musabbabin ibtila’in da ya afku a kasuwar Singa jihar Kano – Tinubu

0

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya jajanta wa ‘yan kasuwa da al’ummar jihar Kano kan mummunar asarar ‘yan kasuwa suka yi a kasuwar Singer a karshen mako.

A yammacin ranar Asabar ne, wuta ta tashi a kasuwar har zuwa safiyar Lahadi, inda ta yi barna mai yawa a sashen kasuwar kayan abinci.

Shugaban kasar, wanda tun da fari ya tuntubi Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin samun rahoton halin da ake ciki, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin tashinta, wanda ke yawan jefa ‘yan kasuwa cikin halin kunci kamar yadda Bayo Onanuga mai magana da yawunsa ya sanar.

Obama ya yi tir da zarafin da Trump ya yi masa shi da mai dakinsa

0

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi tir da yadda aka yi amfani da hoton sa da matarsa, Michelle Obama, a wani bidiyo da Donald Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda aka nuna su a matsayin birrai.

Bidiyon wanda aka riga aka goge daga asusun Trump, ya yi kaurin suna ne bayan ya hada hoton iyalan Obama da wani bidiyo mai ƙaryataccen zargi kan zaɓen 2020. Trump ya ce bai ga bangaren da ya saba wa ɗabi’a ba kuma bai yi nadama ba.

Bidiyon ya jawo suka daga bangarori daban-daban na siyasa, inda ake kallon sa a matsayin abin zargi da rashin mutunci, musamman tun da hoton ya yi amfani da tsohuwar ƙiyayya ta nuna bakaken fata a matsayin birrai.

An shirya wa Shugaban jamhuriyar Niger tarba ta musamman a Aaljeria

0

Shugaban Niger, Janar Abdurahamane Tiani, ya isa Algeria ranar Lahadi, 15 ga Fabrairu, 2026.

Inda ya samu tarba ta musamman daga Shugaba Abdelmadjid Tebboune na Algeria.

Ziyarar ta aiki da karfafa alaka wadda jaridar CNSP ta ambato na daga cikin kokarin karfafa dangantaka da hadin kai tsakanin kasashen Niger da Algeria, a cikin muradin amfanin al’ummomin kasashen biyu.

El-Rufai ya nemi Ribadu ya yi karin haske kan ‘gubar’ thallium sulphate mai matukar hatsari

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bukaci Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da ya fayyace rahotannin da ke cewa ofishin NSA ya shigo da sinadarin thallium sulphate, wanda ake dauka a matsayin guba mai matukar hadari.

A cikin wata wasika mai taken “Request for Clarification on the Procurement of Thallium Sulphate”, Malam El-Rufai ya ce akwai muhimman tambayoyi da ya kamata NSA din ya amsa domin kawar da shakku da ke tattare da batun.