Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 21

Hadin kan siyasa na karuwa a Kano – Gwaman Kano

0

Gwamnan Kano State, Abba Kabir Yusuf, ya ce ana samun ci gaba a hadin kan siyasa a jihar, yana mai fatan rikicin masarautar Kano zai warware cikin lumana.

Ya bayyana hakan ne a zaman addu’a da karatun Alkur’ani da aka yi a Kano, inda ya ce ana ganin sakamakon addu’o’in ta fuskar karuwar fahimta tsakanin shugabanni.

Jaridar Daily Trust ta ambato ya yi alkawarin hada kan ‘yan siyasa da yaki da daba, yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yaba da shirin addu’ar hadin kai da ake yi a jihar.

Wike ya ja layi da wanda ba sa goyon bayan Tinubu

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce zai mara wa duk dan takarar da ke goyon bayan Shugaban Kasa, Bola Tinubu, baya a zaben kananan hukumomin FCT da za a gudanar ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

Wike ya bayyana hakan ne a birnin Abuja yayin bikin cika shekaru 60 na Sanata Sandy Onor, inda ya ce matsayinsa wajibi ne da ya rataya a wuyansa na goyon bayan shugaban kasa.

A cewar Hukumar zaben Nijeriya, INEC, kimanin masu kada kuri’a miliyan 1.68 ne aka tantance domin kada kuri’unsu a zaben.

Inda za a zabi shugabanni da mataimakansu a kananan hukumomi shida na FCT, tare da kansiloli 62 da za su wakilci mazabu 68.

Hukumar ta kuma tabbatar da amfani da manhajar IReV domin nuna sakamakon zabe kai tsaye don kara gaskiya a zabukan kasar.

Manyan jam’iyyun siyasa da suka hada da APC, PDP da ADC sun tsayar da ‘yan takararsu a zaben, yayin da wata babbar kotun tarayya ta hana jam’iyyar LP tsayar da ‘yan takara a zaben bisa zargin tangarda a tsarin fidda gwani.

Tinubu zai kai ziyara jihar Adamawa a ranar Litinin

0

Shugaban kasa, Bola Tinubu, zai kai ziyara ta aiki jihar Adamawa ranar Litinin, kasa da sa’o’i 48 bayan irin wannan ziyara da ya kai a jihar Kebbi.

Sanarwar ta fito ne daga hannun Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ranar 15 ga Fabrairu, 2026.

A yayin ziyarar ta yini guda, Shugaba Tinubu zai kaddamar da wasu manyan ayyuka da aka kammala, sannan ya gana da manyan jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya na jihar.

Daga cikin ayyukan da za a kaddamar a babban birnin jihar, Yola, da Jimeta, akwai titin Galadima Aminu mai layuka takwas da ke hada Gimba da babban birnin jihar.

Sauran ayyukan sun hada da sabon dakin taro na zamani, gyaran kotun koli ta jihar, sabon ginin ofisoshin gwamnati, da kuma sabunta Gidan Gwamnati.

Atiku ya bukaci karin dauki ga ‘yan kasuwar da iftila’in Singa ya shafa

0

Madugun adawa a Nijeriiya Atiku Abubakar ya mika sakon jajantawa ga ’yan kasuwa da iyalan da suka yi asarar dukiya a kasuwar Singer da ke birnin Kano, inda ya bayyana alhininsa kan asarar da aka yi.

Haka kuma, ya yaba da kokarin da gwamnatin Kano ke yi na daukar matakan gaggawa domin tallafawa wadanda suka yi asara, yana cewa hakan na kara samar da fata a cikin halin kunci.

Sai dai ya bukaci a fadada kokarin domin samar da cikakken tallafi, farfado da sana’o’in da abin ya shafa, tare da daukar tsauraran matakan kariya domin kauce wa sake faruwar irin wannan iftila’i a kasuwanni.

Saudiyya ta bukaci Musulmi su fara duban jinjirin Ramadan ranar Talata

0

Babbar Kotun Ƙolin Saudiyya ta bukaci dukkan Musulmi a faɗin Masarautar su fara duban jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 29 ga Sha’aban 1447AH, wanda ya yi daidai da 17 ga Fabrairu, 2026.

Kamar yadda Majalisar ta bayyana a sanarwar da shafin Haramain ya fitar, duk wanda ya hango jinjirin da idon sa ko ta na’urar hangen nesa, ya garzaya kotun da ta fi kusa da shi domin ba da shaidarsa.

Jiragen sojin Amurka sun fara sauka a Maiduguri

Jiragen sojin Amurka sun fara sauka a birnin Maiduguri, Jihar Borno, a wani sabon mataki na haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya.

Kamar yadda jami’ai suka bayyana, wani jirgin sojin Amurka ya sauka a daren Alhamis a filin jirgin saman Maiduguri, yayin da ake sa ran ƙarin jirage za su iso a ƙarshen mako.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kusan jami’an Amurka 200 ne, ciki har da masu nazarin bayanan sirri, masu ba da shawara da masu horaswa za su zo Nijeriya.

alibin jiragen nau’in C-17 ne masu ɗaukar kaya, waɗanda ke kawo jami’ai da kayan aiki domin tallafa wa rundunonin tsaron Nijeriya a yaƙi da matsalolin tsaro a arewa maso gabas.

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

0

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar Niger.

Mazauna yankin sun ce harin farko ya faru ne da misalin karfe 3:00 na asubahin ranar 14 ga Fabrairu a Tugan-Makeri, inda aka mutane 6 suka rasa rayukansu, aka kona gidaje tare da sace wasu. Daga baya da misalin karfe 6:00 na safe, maharan sun kai farmaki Konsoko da Pissa inda aka ce an hallaka karin mutane 26.

Wani mazaunin yankin, Hassan Abdullahi, ya shaida cewa ’yan bindigar sun kai sama da 200 kuma sun shafe awanni suna cin karensu babu babbaka, daga karfe 6:00 na safe zuwa kusan 10:00 na safe.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da harin Tugan-Makeri da mutuwar mutum shida, yana mai cewa jami’an tsaro sun bazama yankin domin daukar mataki da ceto wadanda aka sace, yayin da cikakken bayani kan sauran hare-haren ke jiran tabbaci.

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

0

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da ayyuka na gari.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X mai taken “Nigeria Needs Our Love in Action” a ranar 14 ga Fabrairu, Obi ya ce soyayya ba ji kawai ba ce, illa sadaukarwa, ladabi da rikon amana ga abin da yake daidai, gaskiya, tausayi, mutuntaka da kishin al’umma.

Ya ce nuna soyayya ga Nijeriya na nufin goyon bayan zaɓe na gaskiya, ƙin rashawa, kwaɗayi da rarrabuwar kai, tare da marawa masu nagarta baya. Ya ƙara da cewa kishin ƙasa na gaskiya shi ne nuna kura-kurai tare da bayar da mafita, da kuma inganta adalci, ƙwarewa, gaskiya da zuba jari a ilimi da kiwon lafiya.

Obi ya kammala da kira ga ’yan Nijeriya da su mayar da soyayya aiki a rayuwarsu ta yau da kullum, yana mai cewa sabuwar Nijeriya na yiwuwa idan aka rungumi soyayya mai ɗorewa.

Nijeriya na da damar jagorantar Afirka ta zama babbar nahiya a duniya – António Guterres

0

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya bukaci Nijeriya ta jagoranci Afirka wajen neman sauyi a tsarin duniya, yana mai cewa ƙasar na da ƙarfin da zai kai nahiyar mataki babba.

Guterres ya bayyana hakan ne bayan ganawa da Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, a gefen taron koli na 39 na Kungiyar Afrik da aka gudanar an Addis Ababa, Habasha. Ya ce yawan al’umma, dorewar dimokuraɗiyya da albarkatun ƙasa da na ɗan Adam da Nijeriya ke da su sun ba ta dama ta zama jagora.

Ya kuma yaba wa sauye-sauyen tattalin arziki na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rawar da ƙasar ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel da ECOWAS duk da ƙalubalen tsaro na cikin gida.

A nasa bangaren, Shettima ya jaddada aniyar Nijeriya na ci gaba da aiki tare da Majalisar Dinkin Duniya tare da neman gyaran tsarinta domin bai wa Afirka wakilci mai ƙarfi, yana mai cewa Nijeriya ta cancanci kujera ta dindindin a Kwamitin Sulhu inda bangarorin biyu suka yi alƙawarin ƙara zurfafa haɗin gwiwa.

Mun saurari kiran da aka ba da umarnin kama ni bayan wani ya yi kutsen wayar Ribadu – El-Rufai

0

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce ya saurari wata tattaunawar waya da ya danganta da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, inda ya yi zargin cewa an bayar da umarnin kama shi.

Rahotanni sun ce jami’an DSS sun yi ƙoƙarin kama shi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja bayan dawowarsa daga Masar.

A wata hira da BBC Hausa, El-Rufai ya ce gwagwarmayar siyasa domin sauya gwamnati ta fara, yana mai cewa da tuni an gurfanar da shi idan akwai hujjar zargi a kansa.

A wata hira da ARISE Television, ya ce ba EFCC ba ce ke da hannu a lamarin, sai dai ya zargi ICPC da neman taimakon DSS domin kama shi, yana mai cewa lauyoyinsa sun riga sun tuntubi EFCC kan batun gayyata.

El-Rufai ya amince cewa sauraren kiran waya ba bisa ka’ida ba ne, amma ya dage kan cewa ya samu bayanan ne ta wata hanya. Har zuwa hada wannan rahoto, hukumomin da aka ambata ba su yi martani ba.