Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 25

‘Yansanda sun cafke ‘Dan da ake zargi wajen yin garkuwa da mahaifinsa a Adamawa

0

Jami’an ‘yansanda a jihar Adamawa sun cafke wani matashi da ake zargi da hada baki da ɓata-gari wajen yin garkuwa da mahaifinsa.

Mai magana da yawun rundunar SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da kamen wadanda ake zargi da aikata laifin, bayan gudanar da binciken sirri da kuma hadin gwiwa da jami’an sa kai, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar sa, rundunar ta dauki mataki ne bayan korafin da aka shigar gabanta na batan mutumin mai suna Alhaji Ahmadu a garin Malabu da ke karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa.

A cewar sa, duka matasa ukun da aka kama sun amsa hannu a sace shi, ciki har da dansa na cikinsa, kuma rundunar tana ci gaba da bincike don ceto wanda aka yi garkuwa da shi cikin koshin lafiya.

Hukumar NiMet ta shawarci manoma da su jinkirta fara shuka

0

Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi hasashen saukar damina da wuri a shekarar 2025, musamman a jihohi irin Kano, Neja, River da wasu 12.

Ministan harkokin sufurin jiragen saman kasar Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya gargadi manoma da su guji fara shuka da wuri don gujewa fuskantar kalubale a kan kayan amfanin gona.

Ministan ya kara da cewa duk da kasancewar an fara samun saukar ruwan sama a wasu yankunan Nijeriya, akwai yiwuwar samun sauran lokaci kafin ainahin damina ta fadi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

‘Yan vigilante sun kwankwashi kan matashi da kusa

0

‘Yan vigilante sun kwankwashi kan wani matashi da kusa bayan sun zarge shi da satar kaza a Zaria jihar Kaduna.

Mahaifin matashin, Malam Salisu Nuhu wanda aka fi sani da Babandede, ya tabbatar da lamarin tare da zargin jami’an vigilante biyu da yin aika-aikar.

A cewar sa, shi ne ya aiki dan nasa ya siyar da kaza a kasuwa, kafin jami’an su zarge shi da sata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tuni dai DPO na ‘yansandan yankin na Zaria Nura Abubakar ya ce an cafke mutum guda da ake zargi cikin jami’an, tare da shan alwashin gudanar da cikakken bincike.

Gwamnatin Nijeriya ta umurci NAFDAC ta dakatar da haramci kan barasar leda

0

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta umurci hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC ta dakatar da haramta amfani da barasar leda a fadin kasar.

 

Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin kasar ta fitar.

 

Sanarwar ta kuma ja kunnen hukumar da ta dakatar da rufe masana’antu da kuma gidajen ajiya duk a kan batun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Haka kuma ta ce an cimma matsayar ne bayan tattaunawa tsakanin ofishin sakataren gwamnatin tarayya da kuma na mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, musamman kan abin da ya shafi tsaro a sakamakon haramcin.

Amurka na iya taka rawar gani fiye da na ‘yar kallo a zaben 2027 – Yakubu Dogara

0

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Yakubu Dogara, ya yi gargadin cewa Amurka na iya taka rawa mai zurfi, ba wai ta zura ido ba kawai, a zaben gama-gari na Nijeriya na shekarar 2027.

Dogara ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a gidan talabijin na Channels, inda ya ce sha’awar Amurka ta samo asali ne daga muhimmancin Nijeriya ga zaman lafiyar Afirka da kuma muradun Amurka na kasa da kasa.

Ya ce tsarin hulda tsakanin kasashe na duniya ya raunana, inda kasashe ke kara tsananta kare muradunsu.

Dogara ya ce Amurka ba za ta so Nijeriya ta durkushe ba, domin hakan na iya haifar da mummunan tasiri ga Afirka baki daya, don haka zai zama cikin muradunsu su sa ido sosai kan zaben 2027.

Bisa radin kaina na yi murabus daga shugabancin hukumar NAHCON – Farfesa Abdullahi Pakistan

0

Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Sheikh Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa na Shugaba kuma Babban Darakta na hukumar, daga ranar Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.

A cikin wata sanarwar da ya aike wa manema labarai, Farfesa Usman ya ce murabus din nasa ya samo asali ne daga dalilai na kansa kawai, bayan yin addu’a da tuntubar iyalansa, ba tare da wata matsala ko sabani da gwamnati ko hukumar ba.

Ya ce ya mika rubutacciyar wasikar murabus dinsa ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa tanadin Sashe na 3(6) na Dokar Kafa Hukumar NAHCON ta 2006.

Tsohon shugaban hukumar ya nuna godiya ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima bisa amincewa da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake rike da mukamin, tare da yaba wa mambobin kwamitin gudanarwa, ma’aikatan NAHCON da sauran abokan hulda ciki har da hukumomin aikin hajji na jihohi da mahukuntan Saudiyya.

Yana mai addu’a ga maniyyatan Nijeriya da Hajji Mabrur.

Majalisar dattawa ta amince da tura sakamakon zabe kai tsaye da tsarin tuka-tuka

Majalisar Dattawan Nijeriya ta janye matsayinta na baya tare da amincewa da tura sakamakon zabe ta kai tsaye daga rumfunan zabe zuwa dandalin IReV na INEC, inda ta tanadi cewa idan tsarin yanargizo ya gaza, takardar EC8A za ta zama babbar hanyar tattara sakamako.

Majalisar ta dauki wannan matsaya ne a zaman gaggawa da ta yi a Abuja, bayan amincewa da kudurin da mai tsawatarwa na Majalisar, Sanata Mohammed Monguno, ya gabatar, wanda Shugaban ‘Yan Adawa, Sanata Abba Moro, ya mara wa baya.

Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sabon tanadin Sashe na 60(3) kafin a kada kuri’a, inda mafi yawan sanatoci suka amince da gyaran.

Sanata Monguno ya ce an dauki matakin ne domin dokar zabe ta dace da muradin ‘yan Nijeriya da kuma tabbatar da sahihin zabe mai gaskiya da adalci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da farko zaman ya kaure da hayaniya, bayan wasu sanatoci sun nuna rashin jin dadi da wasu kalmomi da ke cikin sabon tanadin, sai dai daga bisani Majalisar ta amince da shi.

Shehu sani ya goyi bayan Remi Tinubu kan hare-haren sama na Amurka a Sokoto

0

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya goyi bayan kalaman Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, na maraba da hare-haren sama da Amurka ta kai kan ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto, yana mai cewa matakin ya dace.

Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya ce hare-haren saman da aka kai a watan Disambar 2025 kan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Arewa maso Yamma abin a yaba ne, tare da kira da a kara kai irin wadannan hare-hare daga Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya.

Jaridar Punch ta ambato shi ya ce bai fahimci dalilin da ya sa wasu ke sukar Remi Tinubu ba, duk da munanan laifukan kisan gilla, fyade da garkuwa da ‘yan ta’addan ke aikatawa.

Hare-haren saman sun auku ne a ranar 25 ga Disambar 2025, inda rahotanni suka ce sojojin Amurka, tare da hadin gwiwar gwamnatin Nijeriya, suka kai hari kan ‘yan kungiyar IS a wasu yankuna na Sokoto da ke kusa da iyakar Nijar.

Uwargidan Shugaban Kasa ta yaba da matakin ne yayin wata ziyara da ta kai Washington DC, inda ta bayyana harin a matsayin alheri, tare da bukatar a kara hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka a fannin tsaro da musayar bayanan sirri.

Akpabio ne ke hana amincewa da tura sakamakon zabe kai tsaye – El-rufa’i

0

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna kuma jigo a jam’iyyar ADC, Malam Nasir El-Rufai, ya zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da hana shigar da tanadin tura sakamakon zabe kai tsaye ta yanargizo a cikin kudurin gyaran Dokar Zabe dagangan.

El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 30 Minutes na Trust TV, inda ya ce matsalar ba ta fito daga sanatoci ba, illa daga shugabancin Majalisar.

A cewarsa, yawancin sanatoci na goyon bayan kudurin da Majalisar Wakilai ta amince da shi, wanda ke wajabta tura sakamakon zabe kai tsaye daga rumfunan zabe, amma shugabancin Majalisar Dattawa na dakile batun.

El-Rufai ya zargi jam’iyya mai mulki da tsoron sahihin zabe, yana mai cewa hakan ne ya sa ake kokarin barin damar sauya sakamako bayan an kada kuri’a.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana nadamarsa kan rashin halartar zanga-zangar da Peter Obi da sauran ‘yan adawa suka yi a Majalisar Tarayya, inda ya ce da yana Abuja da ya halarta.

An damfari wata mata kudi N603m don a bata aiki a kamfanin NNPCL

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya, EFCC ta gurfanar da Gidado Ibrahim a gaban Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja, bisa zargin damfarar kudade har N603.4m, inda ake zargin ya karbi kudin ne da sunan shirya wa wata mace mukamin Shugabar Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPC.

A zaman kotun na ranar Litinin, alkalin kotun Mai shari’a H. Muazu ya karanto tuhuma guda shida da suka shafi damfara da amfani da takardun bogi, ciki har da amfani da wata takarda mai taken “ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro” da ake zargin ta bogi ce.

Gidado Ibrahim ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, lamarin da ya sa kotu ta dage shari’ar zuwa 17 ga Fabrairu, 2026, tare da umarnin a tsare shi a gidan yarin Kuje, yayin da ake jiran sauraron bukatar belinsa.