Majalisar Dattawan Nijeriya za ta gudanar da zaman gaggawa a yau Talata, sakamakon karuwar muhawara da zanga-zanga kan gyaran Dokar Zabe, musamman batun tura sakamakon zabe ta yanar gizo.
Sanarwar zaman ta fito ne a cikin wata takarda da Magatakardar Majalisar, Emmanuel Odo, ya fitar bisa umarnin Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio.
Muhawarar ta fi karkata ne kan Sashe na 60, Karamin Sashe na 3, wanda ya shafi tura sakamakon zabe ta yanar gizo.
Majalisar ta ki amincewa da kudurin da zai wajabta tura sakamakon zabe kai tsaye a lokaci guda, inda ta bar tanadin da ke cikin Dokar Zabe ta 2022.
Tanadin da aka bari na cewa jami’in rumfar zabe zai tura sakamakon, ciki har da adadin masu kada kuri’a, ta hanyar da Hukumar Zabe (INEC) za ta tanada.
Kudurin da aka ki amincewa da shi kuwa ya bukaci a rika tura sakamakon rumfar zabe kai tsaye zuwa dandalin IREV bayan kammala sa hannu da hatimi kan takardun sakamako.
