Masana harkokin lafiya sun bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ba da fifiko wajen samarwa da wadatar da maganin harbin maciji (antivenom) a asibitoci fadin Nijeriya, yayin da rahotanni ke nuna cewa kasar na samun kusan harbin maciji 43,000 a duk shekara.
Manyan kwararrun lafiyar sun bayyana cewa karancin samun wannan muhimmin magani na ci gaba da haddasa mutuwar mutane da dama da maciji ke harba a kasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sun kuma nuna cewa baya ga karancin maganin, wadanda harbin maciji ya shafa na kashe tsakanin N180,000 zuwa N250,000 a kan kashi daya na maganin, adadin da ya kai kusan albashin watanni hudu ga ma’aikacin da ke karbar mafi karancin albashi na N70,000 a Nijeriya.
A cikin wata sanarwar bayan wani taro kan kula da harbin maciji da hanyoyin bincike, wanda aka wata kungiya ta gudanar a Jami’ar Gombe, kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin matsalar da aka yi watsi da ita, duk da irin barnar da take haifarwa a fadin kasar.
Ana samun harbin maciji kusan 43,000 a Nijeriya duk shekara – Masana
Gwamnatin Kogi ta rufe kasuwanni da tashoshin mota saboda matsalar tsaro
Gwamnatin Jihar Kogi ta sanar da rufe wasu kasuwanni da tashoshin mota na ɗan lokaci a sassan Yankin Kogi ta Yamma, a wani mataki na ƙara tsaurara matakan tsaro domin fatattakar ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Mista Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Lahadi, 8 ga watan Fabrairun 2026.
Fanwo ya ce rufe kasuwannin da tashoshin motar na daga cikin goyon bayan da gwamnatin jihar ke bai wa ayyukan samar da tsaro da ake gudanarwa, tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA) da kuma shugabannin hukumomin tsaro a jihar Kogi.
Majalisar Dokokin Kano ta musanta yunkurin tsige mataimakin gwamna
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karyata rahotannin da ke yawo na cewa ana shirin tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Aminu Abdulsalam Gwarzo, tana mai bayyana rahotannin a matsayin marasa tushe.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Asabar, mai magana da yawun Kakakin Majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya ce babu wata tattaunawa, kudiri ko shiri a cikin Majalisar da ke nufin tsige mataimakin gwamnan.
Ya jaddada cewa rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa ba su da sahihanci, kuma na iya haddasa tashin hankali na siyasa ba tare da wani dalili ba a jihar.
Kasashe na iya kin amincewa da sabbin jakadun Tinubu saboda karancin wa’adin aiki
Rahotanni daga jaridar Punch sun nuna cewa wasu daga cikin sabbin jakadun da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada na iya fuskantar matsalar kin amincewa daga kasashen da aka tura su, sakamakon karancin lokacin wa’adin aikinsu.
Manyan jami’ai a Fadar Shugaban Kasa da kuma ma’aikatar harkokin diflomasiyya sun bayyana cewa Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya na fuskantar kalubale wajen samun agrément — wato amincewar hukuma daga kasashen da za su karbi jakadun — ga wasu daga cikin wadanda aka zaba.
A cewarsu, wasu kasashe na bukatar jakada ya samu akalla wa’adin aiki na shekara daya ko biyu, wanda yawanci ake daura shi da tsawon wa’adin gwamnatin kasar da ta aike shi.
Tun da zaben shugaban kasa na gaba zai gudana a watan Fabrairun 2027, kuma wa’adin farko na Shugaba Tinubu zai kare a watan Mayun shekarar, jami’an sun bayyana damuwa cewa wasu kasashe ba za su so karbar jakadun da wa’adinsu ya yi kankanta ba a wannan lokaci.
Wani babban jami’in diflomasiyya da ya nemi a sakaya sunansa saboda muhimmancin batun ya ce:
“Babbar matsalar da muke fuskanta yanzu ita ce kasashe da dama, misali Indiya, na iya cewa idan wa’adin jakada bai kai shekara daya ko biyu ba, za su samu matsala wajen karbarsa. A yawancin lokuta, ana kallon wa’adin aiki har zuwa karshen gwamnatin da ke kan mulki.”
Gwamnatin Sokoto ta nesanta kanta da kyautar mota da shago da aka bai wa Rahama Saidu
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da batun bai wa ƴar TikTok Rahama Saidu mota da shago, wanda wani mai suna Sanin Jaman ya yi, a wani faifan bidiyo ya karade kafafen sada zumunta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ofishin Mai Magana da yawun Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya fitar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce, Sanin Jaman ya bayyana cewa kyautar da ya bai wa Rahama Saidu a kashin kansa ne, domin nuna godiya da yabon da take yi wa gwamnatin Ahmad Aliyu a jihar Sokoto.
Sai dai gwamnatin jihar ta jaddada cewa ba ta da hannu ko alaƙa da wannan kyauta, tare da nesanta Gwamna Ahmad Aliyu da gwamnatin jihar Sokoto daga lamarin baki ɗaya.
Rasha na son shiga tsakani don sasanta ECOWAS da ƙungiyar AES
Ƙasar Rasha ta bayyana aniyarta ta taka rawar shiga tsakani domin sasanta Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da ƙungiyar AES, wadda ta ƙunshi Nijar, Mali da Burkina Faso.
Jakadan Rasha a ƙasashen Bénin da Togo, Igor Evdokimov, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labaran ƙasar Rasha, TASS.
A cewarsa, Moscow na shirin bayar da gudummawa wajen dawo da tattaunawa da fahimta tsakanin ƙasashen ECOWAS da takwarorinsu na ƙungiyar AES, bayan rarrabuwar kawuna da ta ɓulla a baya.
Evdokimov ya ce duk wasu muhimman matakai sun kammala domin buɗe sabbin hanyoyi na ƙarfafa tattaunawa da sulhu tsakanin ɓangarorin biyu.
Kazalika, ya jaddada cewa ƙasar Rasha ta shirya tsaf domin taka rawar shiga tsakanin, a matsayin mai neman samar da fahimta da kwanciyar hankali a yankin Yammacin Afirka.
Gwamnatin Nijeriya ta amince da sake buɗe bodar Tsamiya da ke jihar Kebbi domin haɓɓaka kasuwanci
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta amince da sake buɗe iyakar ƙasa ta Tsamiya da ke jihar Kebbi domin ci gaba da kasuwancin ƙetare iyaka, tare da sanya tsauraran matakan tsaro da bin ƙa’idoji.
Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS), CG Adewale Adeniyi, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar Kebbi, ciki har da ’yan kasuwa, masu safarar kaya da kuma ’yan kasuwar albasa.
Adeniyi ya ce matakin sake buɗe iyakar ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya, inda ya jaddada cewa za a gudanar da kasuwancin ne cikin kulawa ta musamman domin tabbatar da tsaro da bin dokokin kwastam.
Wike ya ba ƴan kwangila kwanaki 3 su kwashe sharar Abuja ko ya kwace aikin hannunsu
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa kwangiloli kwanaki uku su kammala share shara a garuruwan Abuja ko kuma fuskantar dakatar da kwangilarsu.
Wike ya bayar da wannan gargadi ne bayan ziyarar duba ayyukan hanyoyi a Karu, Bwari, Kubwa da hanyar Apo–Karshi a Abuja ranar Juma’a.
Ministan ya nuna damuwa kan tarin shara da ke ƙaruwa a gefen hanyar Orozo–Apo–Karshi yayin ziyarar.
Nijar da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da farfado da kasuwanci a iyakar kasashen
Daraktan Janar na Hukumar Kwastam na Nijar, Colonel Mohamed Siddo Yacouba, ya kai ziyarar aiki a Abuja inda ya tattauna da takwaransa na Hukumar Kwastam ta Nijeriya.
Bayan wani zama tsakanin wakilan ƙasashen biyu, an rattaba hannu kan yarjejeniyoyi don ƙarfafa tsaro a iyakar kasashen don sauƙaƙe da farfado da harkokin kasuwanci a manyan hanyoyin shiga da fita tsakanin kasashen.
Wannan mataki na nuna fara sasantawa tsakanin mahukuntan Abuja da Niamey bayan watanni na rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen makwabta.
An kama ɗan jaridar Mali bisa zargin cin mutuncin shugaban Nijar, Janar Tiani
Hukumomin ƙasar Mali sun kama tare da tsare ɗan jarida Youssouf Sissoko, bisa zargin cin mutuncin shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tiani.
Sissoko, wanda shi ne Daraktan Jaridar Alternance a Mali, an kama shi ne a ranar Alhamis, 5 ga Fabrairu 2026, bayan jaridar tasa ta wallafa wani labari da a ciki ta caccaki Janar Tiani, tare da zarginsa da ɗora alhakin harin da ƙungiyar IS ta kai a Yamai kan Faransa, Bénin da Côte d’Ivoire.
A cikin labarin, jaridar ta kuma zargi Janar Tiani da ƙarya, tare da cewa yana ƙoƙarin mayar da ƙasar Nijar wani dakin gwaje-gwaje na siyasar guba.
Sai dai ƙungiyar ’yan jarida masu zaman kansu ta riga ta bayyana damuwarta kan kamun Sissoko, inda ta bukaci a bayar da belinsa kafin ranar 9 ga Maris 2026, ranar da ake sa ran a gurfanar da shi gaban kotu.
