Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 4

Hukumar FIFA ta ci tarar kungiyoyin kwallon kafar Nijeriya da DR Congo

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA, ta ci tarar kungiyoyin kwallon kafar Nijeriya da DR Congo saboda wasu laifuka da suka faru yayin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.

Hukumar ta ce magoya bayan ƙasashen biyu sun aikata abubuwan da suka saɓa da dokokin ta a wasan share fage na nahiyar Afirka.

A wasan, tawagar Super Eagles ta sha kashi a hannun DR Congo da ci 4–3 a bugun fenariti, bayan an tashi 1–1 bayan ƙarin lokaci.

Rahoton ladabtarwa na FIFA ya nuna cewa an ci tarar Najeriya ne saboda rashin tsaro da kuma jefa abubuwa cikin fili daga bangaren magoya baya, wanda ya saɓa da sashe na 17.2.b na dokokin ladabtarwa.

Ita kuwa DR Congo an hukunta ta ne sakamakon amfani da na’urar laser daga bangaren magoya bayanta domin haske ’yan wasan Najeriya, wanda ya saba wa sashe na 17.2.c na dokokin.

A hukuncin da ta yanke, FIFA ta ci tarar Najeriya franc na Switzerland 1,000, yayin da ta ci DR Congo franc 5,000.

Nasarar da DR Congo ta samu a kan Najeriya ta ba ta damar tsallakawa zuwa wasan neman tikitin shiga gasar ta duniya da za a buga a kasar Mexico a karshen wannan wata.

Shugaba Tinubu ya umurci a rarraba shinkafa wadatacciya ga ‘yan Nijeriya

Shugaba Tinubu ya umurci a rarraba shinkafa wadatacciya ga ‘yan Nijeriya don azumtar Ramadan da Lent

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin raba shinkafa a faɗin Najeriya domin tallafa wa al’ummar da ke gudanar da azumin Ramadan da kuma na Kiristoci na Lent.

Umarnin ya fito ne ta hannun ƙungiyar magoya bayan shugaban ƙasar mai suna Renewed Hope Ambassadors.

A wata sanarwa da gwamnan Imo State, Hope Uzodinma, wanda shi ne Darakta Janar na ƙungiyar, ya fitar a ranar Asabar, ya ce shirin rabon shinkafar na da nufin tallafa wa ‘yan ƙasa a lokacin azumi.

Dan majalisar wakilan Nijeriya ya sauys sheka daga PDP zuwa ADC

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Tambuwal/Kebbe a jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya koma ADC.

A cikin wasiƙar da ya aika wa shugaban PDP na mazabar Dogon Daji/Salah Ward a ƙaramar hukumar Tambuwal, mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Maris, 2026, Dasuki ya ce rikicin shugabanci da ya daɗe yana addabar jam’iyyar ne ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar.

Ya bayyana cewa matsalolin cikin gida na jam’iyyar sun raunana ƙarfin PDP wajen taka rawar da ta kamata a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya.

Dan majalisar ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da abokan siyasarsa da kuma al’ummar mazabarsa, inda suka nuna damuwa kan halin da jam’iyyar da kuma ƙasar ke ciki.

Sanata Wamako ya raba wa marayu su 10,000 tallafin N1,000 kowane a jihar Sokoto

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko, ya bayar da tallafin miliyan 10, ga mutane dubu 10 da kuma kayan sawa domin tallafa wa marayu da sauran masu ƙaramin ƙarfi kafin bikin Sallah.

Rahotanni sun ce an miƙa gudummawar ta hannun hukumar zakka ta jihar Sokoto, inda shugaban hukumar, Lawal Maidoki, ya karɓi kayan a birnin na Sokoto a ranar Asabar.

Sanatan ya bayyana cewa an tsara bayar da tallafin ne domin bai wa mutane kusan 10,000, musamman marayu, su samu damar yin bikin Sallah cikin farin ciki.

Ban shirya yin yarjejeniyar sulhu da Iran don kawo karshen yakin da ake yi ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce har yanzu bai shirya yin wata yarjejeniya da Iran domin kawo karshen rikicin da ke kara tsananta tsakanin kasashen biyu ba.

TRT Afrika ta rawaito na Trump na bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na NBC News, inda ya ce sharuddan da ake tattaunawa kansu a yanzu ba su kai matsayin da za su gamsar da shi ba.

Ya kuma kara da cewa wani muhimmin sharadi a duk wata yarjejeniyar shine Iran ta amince da daina shirinta na mallakar makaman nukiliya.

A cewarsa, Iran na son a kulla yarjejeniya, amma shi bai shirya amincewa ba har sai an cimma sharuddan da suka dace da bukatar su.

Tinubu ya kare Nijeriya daga faɗawa rikicin farashin mai da kasashen Duniya ke fama da shi – Uzodimma

Gwamnan jihar Imo State, Hope Uzodimma, ya ce shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kare ƙasar daga mummunan rikicin farashin mai da ya addabi kasashen duniya sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya, duk da cewa farashin litar mai ya kai kusan N1,300 a Nijeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Uzodimma ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga ta kungiyar City Boy Movement a gidan gwamnati da ke Owerri a karshen mako.

Gwamnan ya ce rikicin da ya ɓarke tsakanin Iran, Israel da kuma Amurka ya haifar da tashin farashin mai a duniya, musamman bayan da aka samu matsala a mashigar jiragen ruwa ta Strait of Hormuz, wadda kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur na duniya ke bi ta cikinta.

Duk da haka, Uzodimma ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen kauce wa karancin mai da kuma hauhawar farashi fiye da haka a cikin gida.

Shugaba Trump na Amurka ya bukaci kasashe da su tura jiragen yaki na ruwa don kare mashigin Hormuz

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bukaci wasu ƙasashe su tura jiragen yaƙin ruwa domin taimakawa wajen kare Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar man fetur ta duniya da rikicin Gabas ta Tsakiya ya jefa cikin barazana.

Jaridar Punch ta rawaito Trump na bayyana hakan ne a ranar Asabar ta shafinsa na sada zumunta inda ya ce kasashe da dama za su hada kai da Amurka domin tabbatar da cewa mashigin ya kasance a bude ga jiragen ruwa na kasuwanci.

Trump ya kuma yi kira ga manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki kamar China, Faransa, Japan, Koriya ta Kudu da Birtaniya su tura jiragen ruwa zuwa yankin, ganin cewa su ma rikicin da ake samu na iya shafar tattalin arzikinsu.

Hukumar ba da agajin gaggawa a Nijeriya NEMA ta karbi ‘yan kasar 147 da suka makale a Jamhuriyar Nijar

Hukumar ba da agajin gaggawa a Nijeriya NEMA ta karɓi ‘yan kasar 147 da suka dawo daga Jamhuriyar a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, a wani mataki na tallafawa ‘yan kasar da ke dawowa daga ƙasashen waje.

A wata sanarwa da ofishin NEMA na Kano ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a, hukumar ta ce ‘yan Nijeriya din sun iso daga birnin Niamey a ranar 5 ga Maris, 2026 da misalin karfe 12:19 na rana.

Sanarwar ta bayyana cewa an gudanar da aikin karɓar su ne tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi da suka haɗa da Nigerian Red Cross Society, da kuma Nigeria Security and Civil Defence Corps.

Hukumar ta ce an gudanar da tantance bayanan mutanen da suka dawo a ranar 6 ga Maris, inda aka gano cewa cikinsu akwai maza manya 136, mata manya biyar, yara maza uku da kuma yara mata uku.

Amurka za ta tura karin sojoji zuwa yankin Gabas ta Tsakiya

Gwamnatin Amurka na shirin tura karin sojoji da jiragen ruwan yaki zuwa yankin Gabas ta Tsakiya yayin da rikici da Iran ke kara tsananta, musamman a yankin.

TRT Afrika ta rawaito cewa ma’aikatar tsaron Amurka na duba yiwuwar tura karin jiragen yaki zuwa yankin domin tallafa wa rundunar da ke can.

Rahoton ya ce sakataren tsaro na Amurka, Pete Hegseth, ya amince da bukatar rundunar ta tura wani bangare na rundunar jiragen ruwa tare da rundunar United States Marine Corps, wadda yawanci ke dauke da jiragen yaki da kusan sojoji 5,000.

Rahoton ya kara da cewa jirgin yaki na ruwa USS Tripoli, wanda ke da sansani a Japan, tare da sojojin da ke cikinsa, sun riga sun nufi yankin Gabas ta Tsakiya domin karfafa rundunar Amurka.

Gina sabon filin wasa na Manchester United mai ɗaukar mutane 100,000 na fuskantar kalubale

Shirin gina sabon filin wasan Manchester United mai kujeru 100,000 na fuskantar matsala bayan da aka samu tangarda wajen mallakar wani fili da ke kusa da Old Trafford.

Jaridar The Sun ta bayyana cewa an sanar da shirin gina sabon filin wasan a bara kan kudin da ya kai kusan fam biliyan biyu £2bn, amma batun mallakar filin da ake bukata ya zama babban cikas ga fara aikin.

Majiyoyi sun ce attajirin dan kasuwa Jim Ratcliffe na iya bukatar karin kusan fam biliyan daya £1bn, domin daƙile jinkirin da ake fuskanta.

Kungiyar ta bayar da kusan fam miliyan 50 domin sayen filin, amma kamfanin Freightliner Group, wanda ke da filin, yana kimanta darajarsa zuwa kusan fam miliyan 400.