Sunday, April 5, 2026
Home Blog Page 5

Wani yaro dan shekaru 16 ya halbe abokinsa da bindiga yayin da suke wasa a jihar Niger

0

Wani yaro mai shekaru 16 mai suna Emmanuel Danladi ya harbe abokinsa Titus Joseph mai shekara 15 har lahira da bindigar mahaifinsa a garin Kwamba da ke Suleja a Jihar Niger.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da yaran biyu ke wasa a gidan Emmanuel, inda ya dauki bindigar da mahaifinsa Danladi Baba ke amfani da ita a kungiyar sa-kai, ya harbi abokin nasa a ciki, wanda daga bisani ya mutu.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an kama Emmanuel da mahaifinsa, sannan aka kai gawar mamacin babban asibitin Suleja yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Amnesty International ta soki yadda Hukumar DSS ke kama mutane saboda fadin ra’ayinsu kan rikicin Iran, Amurka da Isra’ila

0

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta nuna damuwa kan abin da ta kira kara tsaurara mataki da Hukumar farin kaya ta DSS ke yi kan masu yin sharhi a kafofin sada zumunta game da yakin Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar ta ce akalla mutane biyu mazauna Kaduna an tsare su, kuma ana shirin gurfanar da daya daga cikinsu a kotu bisa tuhume-tuhumen da ta kira marasa tushe.

A cewar kungiyar, sukar manufofin gwamnatocin Amurka ko Isra’ila hakki ne na ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada, don haka ta bukaci hukumomin kasar su mutunta wannan hakki ba tare da tsoratar da masu ra’ayi ba.

Matatar man Dangote ta kara farashin man fetur zuwa N1,175

0

Matatar mai ta Dangote ta kara farashin fetur daga matatar (ex-depot) zuwa N1,175 kan kowace lita, bayan rage shi zuwa naira 1,075 a farkon makon nan.

Rahotanni sun ce karin farashin ya biyo bayan tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, inda farashin Brent crude oil ya tashi daga kusan dala 91 zuwa sama da dala 100 kan kowace ganga.

Sauyin farashin ya sa wasu masu rumbunan mai dakatar da saye da sayarwa na dan lokaci domin tantance sabon tsarin farashin, yayin da tashin farashin danyen mai ke da nasaba da rikicin da ke tsakanin Amurka, Iran da Isra’ila.

‘Yan bindiga sun yi ajalin wani magidanci tare da garkuwa da iyalinsa a jihar Kebbi

0

Wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin wani mutum mai suna Sufiyanu Garba mai shekaru 35 tare da yin garkuwa da mai dakinsa a unguwar Badariya da ke Birnin Kebbi a Jihar Kebbi.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Bashir Usman, ya ce an kai mamacin asibitin Sir Yahaya Memorial inda likita ya tabbatar da rasuwarsa, yayin da aka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa.

Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci sashen binciken manyan laifuka su karbi shari’ar domin bincike tare da kokarin ceto matar da aka sace da kuma kamo wadanda suka aikata laifin.

Kotu ta sanya 1 ga Afrilu domin gurfanar da Sule Lamido da dansa kan sabon zargin badakalar N1.35bn

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 1 ga Afrilu domin sake gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, kan zargin almundahanar kudin da ya kai Naira Biliyan 1.3.

Alkalin kotun, Peter Lifu, ya dage shari’ar ne bayan Lamido da ‘ya’yansa biyu, Aminu Lamido da Mustapha Lamido, ba su halarci kotu ba domin karanta musu tuhuma.

Hukumar EFCC na zargin su da safarar kudade ta hanyar kwangiloli na bogi lokacin da Lamido ke gwamnan jihar tsakanin 2007 zuwa 2015, zargin da kotun kolin Nijeriya ta ce dole a cigaba da shari’ar domin su kare kansu.

Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma a Katsina ta dakatar da dalibai 20 saboda satar jarabawa

0

Majalisar Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma da ke Jihar Katsina ta amince da dakatar da dalibai 20 bayan a same su da laifin satar jarabawa.

Daraktan yada labarai na jami’ar, Nasiru M. Abdul, ya ce an yanke hukuncin ne a taron majalisar jami’ar karo na 138 bayan duba rahoton kwamitin ladabtar da dalibai.

Mataimakin shugaban jami’ar, Mohammed Khalid Othman, ya ce an dauki matakin ne bisa dokokin jami’ar domin ya zama gargadi ga sauran dalibai da kuma hana karya ka’idojin jarabawa.

MURIC ta bukaci Gwamnatin Nijeriya da ta samar wa matatun mai na cikin gida isasshen danyen mai

0

Kungiyar kare hakkin Musulmi, MURIC, ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da samar wa matatun mai na cikin gida isasshen danyen mai domin karfafa samar da makamashi a Nijeriya.

Kungiyar ta yaba wa gwamnati bayan sanarwar dakatar da shigo da man fetur daga waje da NMDPRA ta yi, tana mai cewa matakin ya biyo bayan karuwar samar da fetur a cikin gida.

Daraktan kungiyar, Ishaq Akintola, ya ce ya kamata gwamnati ta ba matatar Dangote cikakken danyen mai domin ta iya aiki yadda ya kamata, yana mai rokon Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya bayar da umarnin hakan domin saukaka farashin mai ga ‘yan Nijeriya.

Akwai bukatar sake duba yarjejeniyar bashin da NNPCL ya ciyo wa Nijeriya – Gwamnatocin jihohi

0

Gwamnatocin jihohin Nijeriya sun bukaci a sake duba tsarin bashin da kasar ke biya da danyen mai na Dala Biliyan 8

Rahotanni sun nuna cewa kamfanin NNPCL ya jinginar da ganga dubu 272,500 na danyen mai a rana domin karbar bashin da ya kai dala biliyan 8.86. wanda daga ciki aka biya kusan dala biliyan 2.61, yayin da ake bin Nijeriya sama da dala biliyan 6.

Bukatar binciken ta fito ne daga taron kwamitin rarraba asusun tarayya da aka gudanar a Enugu, inda jami’an gwamnati da kwararru suka tattauna hanyoyin dakile asarar kudaden shiga da ke shafar raba kudaden tsakanin matakan gwamnati uku.

Mahalarta taron sun bukaci duk wata yarjejeniya ta bashin danyen mai ta samu amincewar majalisa, a bayyana cikakkun bayanai game da ita, sannan a gudanar da bincike mai zaman kansa domin kare kudaden Asusun Tarayya.

Sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei na iya kasancewa a raye amma a jikkace – Donald Trump

0

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, yana ganin sabon Jagoran koli na Iran Mojtaba Khamenei, na iya kasancewa da rai amma cikin mummunan yanayi bayan hare-haren da Amurka da Israel suka kai.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Fox News, inda ya ce duk da cewa ba a ga Khamenei ba tun bayan nada shi a matsayin jagora, yana zaton yana raye amma ya jikkata.

A cikin sakon farko da aka karanta a madadinsa, Khamenei ya yi alkawarin ci gaba da rufe mashigin ruwa na Strait of Hormuz, tare da gargadin kasashen da ke dauke da sansanonin sojin Amurka cewa Iran na iya kai musu hari idan suka ci gaba da bai wa Amurka mafaka.

Shugaba Tinubu ya amince da sayen sabbin makaman yaki domin dakile matsalar tsaro

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da sayen karin kayan aikin soja domin karfafa yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a fadin Nijeriya.

Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya bayyana hakan bayan ganawar shugaban kasa da hafsoshin rundunonin tsaro, inda ya ce an gabatar wa shugaban rahoto kan yadda ake gudanar da ayyukan tsaro a sassan kasar.

Ya ce duk da hare-haren da aka samu a baya-bayan nan, sojoji sun yi nasarar hallaka wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’adda tare da kwace wasu kayayyakinsu, yana mai cewa rundunar sojin Nijeriya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron al’ummar kasar.