DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 404

An janye dokar hana fita bakidaya a jihohin Kano, Kaduna da Jigawa

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da janye dokar hana fita bakidaya a jihar bayan zanga-zanga tsadar rayuwa da aka gudanar da ta rikide ta koma tarzoma a wasu yankunan jihar.

A cikin wata sanarwa daga Samuel Aruwan da ke kula da ma’aikatar tsaron cikin gida na jihar, ta ce dama garuruwan Zaria da Kaduna ne aka sanya dokar biyo bayan hargitsi da aka samu a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa, amma an janye bayan samun rangwamen wannan lamari.

Kazalika, jihar Jigawa ma ta sanar da janye dokar hana fita din bakidaya a kananan hukumomi 8 na jihar da aka kakaba biyo bayan tashin tarzoma a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar Sagir Musa ya fitar, ta ce kananan hukumomin da aka sanya wannan doka a baya su ne Kazaure, Birnin Kudu, Gumel, Hadejia, Kiyawa, Babura, Roni da babban birnin jihar, Dutse.

Jihar Kano ma ta sanar da janye wannan doka bakidaya kamar yadda Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sanar.

Gwamnatin jihar ta ce ta yanke shawarar janye dokar ne biyo bayan samun rahotannin ingancin tsaro a sassan da aka samu rahotannin tashin hankali a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Muna zargin wasu mutane sun mallaki otal-otal da kudi mallakin jihar Kano a kasashen waje – Barr Muhyi Rimin-Gado

0
Hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta ce ta gano yadda aka sace sama da Naira biliyan 50 daga asusun gwamnatin jihar da na kananan hukumomi  44 na jihar.
Kazalika hukumar ta hannun shugaban ta Barr Muhyi Magaji Rimin Gado, ta ce ta gano yadda aka yi amfani da kudi Naira miliyan 450 domin sayo gidan sauro a magance zazzabin malaria a jihar.
Shugaban hukumar ya bayyana hakan a wajen taron haras da ma’aikatan gwamnatin jihar, inda ya ce hukumar na kuma bin kadin wasu kadarori da take zargin an yi amfani da kudin sata wajen mallakarsu a Dubai, London da Abuja, ciki kuwa hada otal-otal.

Peter Obi ya yi alhinin kan rayukan da aka rasa yayin zanga-zanga

 Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya nuna bakin cikinsa kan yadda aka samu asarar rayuka a lokacin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.

Peter Obi ya yi alhinin ne a shafinsa na X a ranar Lahadi.

Ya ce, “A yayin da zanga-zangar adawa ta tsadar rayuwa ta kammala a hukumance a jiya, ina so in sake mika sakon ta’aziyyata ga duk wadanda suka rasa rayukansu, ciki har da jami’an tsaro a yayin wannan zanga-zan

gar.

SERAP na son a binciki gwamnoni yadda suka yi da bashin da suka ci daga bankin duniya

 SERAP na son a binciki gwamnoni yadda suka yi da bashin da suka ci daga bankin duniya

Kungiyar SERAP ta bukaci shugaban Nijeriya Bola Tinubu, da ya umurci babban lauyan tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) da sauran hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa su yi gaggawar gudanar da bincike kan yadda gwamnonin kasar suka kashe kudaden da suka kai dala bilyan $1.5bn sa suka amso lamunin Bankin Duniya don rage talauci da kare lafiyar jama’a a fadin jihohin.

Ba mu samu umurnin biyan N70,000 ga masu bautar kasa ba – Hukumar NYSC

 Ba mu samu umurnin biyan N70,000 ga masu bautar kasa ba – Hukumar NYSC 

Hukumar da ke kula da matasa masu yi wa kasa hidima NYSC ta ce har yanzu ba su samu umurnin kan ko za su biya ‘yan bautar kasa mafi karancin albashi na N70,000.

Hukumar NYSC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a Mista Eddy Megwa ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Gwamnatin Nijeriya dai ta riga ta sanar da N70,000 a matsayin mafi karancin abin da za a iya biyan karamin ma’aikaci a fadin kasar.

Matasa za su ci moriyar gwamnatin Tinubu – Shettima

 Matasa za su ci moriyar gwamnatin Tinubu – Shettima 

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Bola Tinubu na tallafawa da karfafawa matasa ‘yan Najeriya kwarin guiwa wajen yin fice a sana’o’in da suka zaba.

 A cewarsa, shugaban kasa yana mutunta matasan Najeriya, kuma jajircewarsa na bayyana a cikin nade-naden mukaman da ya yi da kuma manufofin gwamnati da tsare-tsare irin su asusun zuba jari na matasa, iDICE Programme, da bankin raya matasa na kasa da dai sauransu.

 Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar matasan jam’iyyar APC, karkashin jagorancin shugaban matasan jam’iyyar na kasa Dayo Israel, a ziyarar ban girma da suka kai fadar shugaban kasa.

Atiku ya yi takaicin yadda wasu ke yunkurin dakile ci gaban matatar man Dangote

 Atiku ya yi takaicin yadda wasu ke yunkurin dakile matatar Dangote 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi fatali da yunkurin dakile ci gaban matatar man Dangote.

A wani sakon da ya fitar ta hanyar X a ranar Asabar, Atiku ya bayyana matatar a matsayin wani muhimmin aiki na kamfanoni masu zaman kansu.

Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su tabbatar da cewa babu wani daga gida ko waje sa za a hada kai da su don hana kasar cin moriyar matatar m

an ba.

An sake sassauta dokar hana fita a Jos jihar Plateau

 An sake sassauta dokar hana fita a Jos jihar Plateau 

Gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta kafa a Jos babban birnin jihar, wanda zai ba da damar zirga-zirga daga karfe 10 na safe zuwa 6 na yamma.

Haryanzu jihohi ba su karbi Naira biliyan 570 daga gwamnatin tarayya – Gwamna Seyi

 

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce jiharsa ba ta amshi Naira Biliyan N570bn da Gwamnatin Tarayya ta ba jihohi domin yaki da yunwa kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito

A yayin da yake jawabi ga ‘yan Najeriya a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin kasar Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta biya ₦570bn ga jihohi 36.

Makinde ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Alhamis, ya ce jihar ba ta da masaniyar irin wannan tallafin.

Makinde shi ne gwamna na biyu daga jam’iyyar PDP da ya caccaki shugaba Tinubu kan jawabin sa.

An biya naira biliyan 700 a matsayin cin hanci a Nijeriya a 2023 – ICPC

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta nuna takaicin ta kan yadda ake samun yawaitar cin hanci da rashawa a Nijeriya.

Shugaban hukumar Musa Aliyu ne ya bayyana hakan a wurin wani taro da jami’ar Ahmadu Bello ta shirya.

A cewar sa kimanin Mutane miliyan 87 a Nigeria ke da hannu bumu-bumu da cin hanci da rashawa da suka Kai naira biliyan 700 da aka gano a cikin shekara ta 2023 inda a yankin karkara lamarin yafi yawa fiye da birane.

Shugaban ya ce cin hanci da rashawa shi ne babban cikas ga ci gaban Najeriya

Hukumar ta ICPC ta himmatu wajen tabbatar da ‘yancin dan Adam da inganta adalci a tsakanin al’umma ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa