DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 405

Ganduje ya nemi hadin kai domin karfafa bangaren shari’a

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya bukaci shugabannin siyasa da su hada kai wajen karfafa bangaren shari’a da tabbatar da bin doka da oda tare da kare ka’idojin dimokradiyya.

Ganduje ya ba da wannan shawarar ne a ranar Alhamis a Abuja, a wajen taron IPAC mai taken Gudunwar Shari’a a Dorewar Dimokuradiyya a Nijeriya.

Ya ce bangaren shari’a na Nijeriya ya taka rawar gani a dorewar dimokradiyya a kasar.

Ambaliyar ruwan sama ya raba titin Kano zuwa Maiduguri

 

Ambaliyar ruwan sama ya raba wani bangare na babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri da ke Malori-Guskuri dake a karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

An ruwaito cewa an samu tsaiko na bin hanyar, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyin.

Da yake jawabi kan lamarin a ranar Alhamis, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jaddada mahimmancin hanyar, wadda ta kasance muhimmiyar hanyar sadarwa tsakanin sassan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Nijeriya.

Gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta gyaran babbar hanyar da ta lalace domin saukaka zirga-zirgar.

Gwamnatin Kano ta zargi Ganduje da wawure wasu kudaden kananan hukumomin

Gwamnatin Kano ta zargi Ganduje da wawure wasu kudaden kananan hukumomin

 

Gwamnatin Kano ta sake bankado wata badakalar Naira Biliyan N57.4bn da take zargin tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da wasu mukarrabansa su uku suka yi

Dr Abdullahi Ganduje da kwamishinansa na kananan hukumomi Murtala Garo da wasu mutane biyu da laifin zamba

Gwamnatin ta Kano ta yi zargin Ganduje da hada baki wajen karkatar da sama da naira biliyan 57.43 da aka ware wa kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Za mu dauki Tinubu aiki a matsayin daraktan yakin neman zaben PDP a 2027 – Bala Muhammed

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya ce jam’iyyar PDP za ta dauki shugaba Tinubu aiki ya zama Daraktan yakin neman zaben jam’iyyar PDP a babban zaben kasar na shekarar 2027.

Bala Muhammed ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomin jam’iyyar PDP a jihar a gidan gwamnati da ke Bauchi a ranar Laraba.

“Akwai yunwa a kasa  kuma mutane sun fara fushi. Dole ne mu magance matsalolinmu na ci gaba.  Babu aikin yi a ko’ina, tsarin ilimin mu ba ya aiki, kuma sabbin manufofin gwamnatin tarayya ba sa aiki.

 “Dole ne su fahimci cewa shirin su ne ya haifar da wadannan matsaloli.  A madadin ku, ina gaya wa Shugaba (Bola) Tinubu ya canza manufofinsa saboda ba sa aiki ko kadan. Inji Gwamnan na jihar Bauchi

Daliban da suka kai jami’ar Al-Qalam Katsina kara, sun yi nasara, har an ci tarar jami’ar N1m

Babbar kotun jihar Katsina ta umurci hukumar gudanarwar jami’ar Al-Qalam da ke Katsina da ta ba tsoffin dalibanta biyu Hawwa’u Sani Barda da Rabi’atu Sani Barda sakamakon kammala digirinsu.
Kazalika, kotun ta umurci hukumar gudanarwar jami’ar da ta lamunce wa wadannan dalibai zuwa shirin yi wa kasa hidima biyo bayan kammala karatun digiri da suka yi a jami’ar.
Bugu da kari, kotun ta umurci hukumar gudanarwar jami’ar da ta biya tsoffin daliban tarar kudi Naira milyan daya saboda bata musu lokaci da ta yi wajen sanya su cikin shirin yi wa kasa hidima na NYSC bisa zargin da jami’ar ta yi musu cewa ba su biya kudin rajista ba na zangunan karatu hudu.
Daliban, ‘yan’uwan juna, sun maka jami’ar Al-Qalam Katsina kotu, inda suke kararta kan hana su sakamakon kammala digiri da kuma kin sanya su cikin shirin yi wa kasa hidima na NYSC.
Jami’ar Al-Qalam Katsina, jami’ar mai zaman kanta ya zargi daliban, Hawwa’u Sani Barda da Rabi’atu Sani Barda da Hafsat Sani Barda da cewa ba su biya kudin rajista na jami’ar ba na tsawon zangunan karatu hudu, zargin da daliban suka musanta.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Abbas Bawale, ya ce bayan sauraren hujjojin da lauya ya gabatar, kotu ta gano cewa Hafsat Sani Barda da Rabi’atu Sani Barda sun biya kudin rajistar karatunsu na tsawon zangunan karatu hudu.
Alkalin ya ce hukumar gudanarwar jami’ar Al-Qalam Katsina ta gaza gamsar da kotu cewa wadannan dalibai ba su biya kudin rajista ba.

Masara ta ƙara kuɗi a wasu kasuwannin sassan Nijeriya

Masara ta sake tashi a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas, an sayi buhunta N103,000 a makonnan, bayan da a satin da shuɗe aka saye ta N100,000 daidai a kasuwar.

Sai Mai’adua jihar Katsina ana sayar da ita N90,000 daidai a makon nan, amma a makon daya gabata N88,000 aka sai da buhun.

Ita ma kasuwar Giwa jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya buhun masara ya ƙara N5000, inda aka sai da buhun N88,000 a makon nan, amma a makon jiya N83,000 ne kuɗin buhunta.

Sai kasuwar Dawanau jihar Kano ana sayar da ita N87,000 a wannan satin, yayinda a makon daya gabata aka saya N80-85,000.

A Dandume jihar Katsina N82-85,000 aka sayi buhun a wannan makon, haka nan aka sai da a makon daya gabata.

N85000 aka sai da buhun masara a kasuwannin jihar Adamawa a satin nan,yayin da a satin daya wuce aka saya N80-85000.

Ita kuwa Shinkafar Hausa tafi tsada a wasu daga cikin kasuwannin jihohin Kano da Kaduna da ke Arewacin Nijeriya,wanda ake saidawa N160,000 cif a makon nan,amma dai farashin ya sha banban a kasuwannin a makon daya gabata,inda a kasuwar Dawanau jihar Kano ka sayar kan kuɗi N157,000,yayin kasuwar Giwa jihar Kaduna aka saya N155,000.

Suma dai kasuwannin jihohin Adamawa da Legas farashin buhun Shinkafa ‘yar gida N150,000 ne a wannan mako.bayanda a makon jiya aka saya N148,000 a kasuwannin jihar Adamawa,amma dai a jihar Lagos farashin daya ne dana makon nan.

Haka zalika farashin shinkafa bai sauya tufafi ba a kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya N138-155,000.

N145,000 aka sai da buhun shinkafar Hausa a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan mako da muke shirin fita,amma a makon jiya an sayi buhun N147,000.

To a bangaren Shinkafar waje kuwa tafi tsada a kasuwar Dawanau da ke jihar Kano da aka saya N98,000 a satin nan,haka kuma aka sai da a makon jiya.

Sai dai,shinkafa ‘Yar Gwamnati tafi sauki a kasuwar Dandume jihar Katsina a wannan mako,wanda aka sai da N69,000,bayan da a makon daya wuce aka saya N70,000 daidai.

A Mai’adua jihar Katsinan kuma aka saya N88000-90,000 a wannan satin,amma a satin daya shuɗe N88,000 ne kuɗin buhun.

A kasuwar Giwa jihar Kaduna kuma farashin Shinkafar ta sake tashi a makon nan da aka saya N85,000,bayan da makon daya kare ak sai da N80,000 cif-cif.

To a jihar Adamawa an sai da buhun ta N87000-88000 a makon nan, amma a makon jiya an sayi buhun N75,000,a satin na an samu karin sama N10,000 kenan.

An samu karin N1000 guda kan farashin shinkafar waje a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a satin nan da aka saya N76000 ,yayinda a makon jiya aka sai da N75,000.

Da alamu sai farashin wake ya sake komawa gidansa na jiya, musamman a kasuwar Mile 12 International Market jihar da ke jihar a kudancin Nijeriya,an sayi buhun N220,000 a wannan mako,bayan da a makon jiya aka saya N200,000 daidai,tashin farko an samu karin N20,000.

Sai Adamawa aka saya N176,000-180,000 a satin nan,amma a makon jiya N170-175,000 aka sai da buhunsa.

A kasuwar Giwa jihar Kaduna N170,000 ake sayar da buhun farin wake a satin da ke dab da ƙarewa, bayan da a makon daya shude aka saya N150,000,hakan na nuna cewar farashin waken yayi tashi zabi a kasuwar Giwa jihar Kaduna.

N140,000-160,000 ne aka sai da buhun wake a kasuwar Dandume jihar Katsina a satin nan,amma a makon jiya N140,000-145,000 aka sai da buhunsa.

Sai kasuwar Mai’adua jihar Katsinan aka saya N160,000-170,000 a wannan makon,amma a makon jiya N180,000 cif aka sai da buhunsa.

Farashin waken yayi tashin gwouron zabi a kasuwar Dawanau jihar Kano wanda aka sayar da Buhun N155,000,yayinda a makon jiya aka sai da N135,000

Ga ma’abota cin taliya kuwa, farashin kwalin bai sauya zani dana makon Jiya da aka saya N18,500 a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas.

Sai farashin ya ƙara a kasuwar Giwa jihar Kaduna wanda aka sai da kwalinta N19,500 a satin nan, yayinda a makon daya gabata aka saya N17500,an samu karin N2000 kenan a makon nan.

N17700 ake sayar da kwalin taliya a kasuwar Zamani da ke jihar Adamawa a mako nan,bayan da a makon daya wuce aka saya N17,500.

An samu sauƙin N500 kan farashin taliya na makon daya gabata a kasuwar Dandume jihar Katsina da aka saya N18,500,amma a makon nan an saya N18,000 cif.

A kasuwar Mai’adua jihar Katsinan N17600 ake sai da kwalin taliya a satin nan,haka batun yake a satin daya gabata.

Ita kuwa kasuwar Dawanau jihar Kano kari aka samu a makon nan da aka saya N18,000, bayan da a makon jiya aka saya N16500.

DCL Hausa A’isha Usman Gebi.

An dakatar da sayar da shinkafa mai rangwamen kudi ga ma’aikatan gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin tarayyar Nijeriya dai ta ce a dakata da batun sayar da wannan shinkafa mai rangwamen kudi ta N40,000 ga ma’aikatan gwamnatin kasar.
Kazalika, gwamnatin ta kuma sanar da janye duk wata takarda wato circular da ta aike wa ma’aikatun gwamnati kan wannan batu na sayar da shinkafar a farashi mai rahusa ga ma’aikatan gwamnatin kasar da ke cewa duk maaikacin da ke bukata, ya nema a tsarin da aka ayyana.
Bayanin hakan na a wata sabuwar takardar da aka fitar daga ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati da jaridar Punch ta samu kwafi a Abuja.
Sanarwar mai dauke da kwanan watan 2 ga Agusta 2024, da Daraktan Ma’aikata na ma’aikatar, Aderonke Jaiyesimi ya sanya wa hannu, ba ta bayar da dalilin janye takardar farko ba.
Kazalika, ba a nuna ko an dakatar da shirin ne ko kuma an fasa kwata-kwata.
Tun da farko, ma’aikatar ta ce duk ma’aikatan da ke da sha’awa, su cika fom akan gidan yanar gizo kuma su mika shi ga daraktan kula da ma’aikatan gwamnati na ofishin shugabar ma’aikatan tarayya, don amincewa.

Zanga-zanga ta sa ba ma samun kwastomomi, in ji karuwai a Kano

Mata masu zaman kansu wato karuwai a Kano sun yi kira ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin Nijeriya da su shiga tattaunawa da gwamnati domin samun mafita.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya rawaito karuwan na kokawa kan zanga-zangar da ta kawo masu cikas a harkokinsu da hakan ya sa ake samun karancin kwastomomi a harkarsu.
Monica James, wata karuwa da NAN ta zanta da ita da ke a kan titin France, ta ce tattaunawar ita ce hanya daya tilo ta magance korafe-korafen masu zanga-zangar.

Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta sauya manufofin da suka sanya ‘yan Nijeriya cikin wahalhalu

Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta sauya manufofin da suka sanya ‘yan Nijeriya cikin wahalhalu

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya NLC, ta yi kira da a sauya manufofin da suka jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki, lamarin da ya janyo zanga-zanga a fadin kasar.

A cewar wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da babban sakataren kungiyar Emmanuel Ugboaja suka sanyawa hannu a wani taron gaggawa da suka gudanar. 

Sanarwar tace tun bayan da ya hau mulki a shekarar 2023, Tinubu ya cire tallafin man fetur da kudin wutar lantarki, sakamakon faduwar darajar Naira. Duk da gwamnati ta ce yin gyare-gyaren manufofin ya zama dole domin sake farfado da tattalin arzikin Nijeriya, sai dai da dama daga cikin ‘yan Nijeriya sun fuskanci yunwa da hauhawar farashin kayayyaki saka makon manufofin.

PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa tun bayan zanga-zangar,Tinubu ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi game da zanga-zangar da aka yi ranar Lahadin da ta gabata amma bai yi wani magana akan abubuwan da mutane sukai zanga-zangar akai ba.

Zan bayyana gaskiya idan lokaci ya yi -Mele Kyari

Zan bayyana gaskiya idan lokaci ya yi -Mele Kyari

Shugaban kamfanin samar da man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya ce zai bayyana gaskiya game da ayyukan kamfanin a bangaren mai da iskar gas a lokacin da ya dace.

Kyari ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake ba da shaida a gaban kwamitin rikon kwarya na majalisar dattawa da ke binciken zagon kasa a harkar man fetur.

Kwamitin wanda Sanata Opeyemi Bamidele ke jagoranta, yana binciken ayyukan kamfanin mai na NNPL, ne a daidai lokacin da jama’a ke kiraye-kiraye kan yadda ayyukan ma’aikatar ke gudana.

Kyari ya bayyana cewa, NNPCL ba ta da hannu wajen shigo da abubuwan da ba su dace ba, ta himmatu ne wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Ya koka da rahotannin da ake yadawa a kafafen sadarwa, inda ya bayyana cewa ana yi ne don bata sunan NNPCL, da kuma zagon kasa ga tattalin arziki.