DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 406

Talauci zai karu idan aka dawo da tallafin mai a Nijeriya – Shugaban NOA

Shugaban Hukumar wayar da kan al’umma ta Nijeriya (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya yi tir da batun dawo da tallafin man fetur, wanda a cewarsa zai kara jefa kasar cikın matsanancin talauci.
Daya daga cikin bukatun masu zanga-zangar kasa dai a yanzu shi ne dawo da tallafin man fetur. 
Amma a jawabin da ya yi wa kasa baki daya ranar Lahadi, Shugaba Bola Tinubu ya kore dawo da tallafin, inda ya bayyana cire shi matsayin abu mara dadi amma ya zama dole.
Ya kuma kara da cewa tallafin man fetur ya zama kamar wani makamin kashe tattalin arzikin kasar nan kuma abin da ya hana shi cigaba.
Da ya ke magana a wani shirin Gidan Talabijin na Channels Issa-Onilu ya shawarci ‘yan Nijeriya kan su tanadi dabarun yadda za su rayu bayan cire tallafin man fetur.
Onilu ya kuma kara da cewa duk wanda ke neman a mayar da tallafin man fetur yana fadin son zuciyarsa ne, ba wani abin da zai taimakawa tattalin arziki ba saboda dole ne a tabbatar da cewa idan an mayar da shi, zai magance matsalar talauci wanda ba zai yi hakan ba sai dai ma ya kara tsananin talauci.

Dokar shigo da kayan abinci ba tare da biyan haraji ba, za ta fara aiki mako mai kamawa – FG

A watan Yuli, Gwamnatin Tarayya ta amince da wani tagomashin kwanaki 150 da ba za a caji haraji ba wurin shigo da masara, shinkafa, da alkama a matsayin wani mataki na yaki da hauhawar farashin abinci a fadin kasar.
Wannan doka dai kamar yadda shugaban hukumar ta Kwastam ya sanar, za ta fara aiki a mako mai kamawa.
Da ya ke magana a taron shugabannin hukumomin tsaro a Abuja, Shugaban Hukumar Kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce za a fara aiwatar da wannan dokar ta shigo da wadannan kayan abinci da zarar an gama shirye-shiryen da suka dace.
Bashir ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dan kara hakuri inda yace wasu daga cikin wadannan kayayyaki da za a shigo da su yanzu haka za su wuce ba tare da haraji ba.

APC ta karbi tubar Ali Ndume ta kuma yafe masa

Sanata Ali Ndume ya fito ya ba  jam’iyyar APC mai mulki hakuri  bayan wata daya da sauke shi daga mukamin shi na mai tsawatarwa. 
Ali Ndume dai ya yi kalaman  da suka bayyana a matsayin suka ga jam’iyyar APC da ke karkashin mulkin Bola Ahmad Tinubu.
Ndume shi ne Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu. Kafin wannan tataburzar yana rike da mukamin mai tsawatarwa a majalisa  wanda bayan wadannan kalaman,shugaban majalisar ya sanar da sauke shi daga mukamin, tare da maye gurbinshi nan take da Sanata Tahir Mongunu a watan Yulin da ya gabata.
A wancan lokacin, jam’iyyar APC tayi barazanar korarsa.Amma dai a farkon makon nan aka jiyo Ali Ndume na cewa ya nemi yafiya wurin uwar jam’iyyar APC ta kasa ta kuma yafe masa.

Babban bankin kasar Kenya ya rage kudin ruwa

A Talatar nan makon nan ne babban bankin kasar Kenya ya sanar da rage kudin ruwa na farko cikin shekaru huɗu.
Wannan na zaman wani yunkurin kawo saukin matsi da hauhawar farashi, yayin da ita kuma gwamnatin kasar ke gwagwarmaya don tara kudaden shiga da biyan bashin jama’a bayan zanga-zangar da aka gudanar kan karin haraji.
Kwamitin kula da harkokin kudi na kasar (MPC) ya bayyana rage kashi daya bisa hudu na kudin ruwan zuwa 12.75 cikin dari.
A cikin wata sanarwa da gwamnan babban bankin kasar kuma shugaban kwamitin (MPC)ya fitar ta ce wannan mataki da aka dauka a baya ya rage hauhawar farashi gaba ɗaya, ya kuma daga darajar kudin kasar sannan ya shawo kan matsalar hauhawar farashin kayan abinci.
Kazalika, jimillar hauhawar farashin kasar na shekara zuwa shekara ya ragu daga 4.6 zuwa 4.3.

‘Yan siyasar da suka sha kaye a zaben 2023 ne ke ruruta zanga-zanga a Nijeriya – Zargin matasan APC

Kungiyar matasan jam’iyyar APC ta zargi wadanda suka fadi zaben 2023 da hannu cikin shirya zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.
Zanga-zangar tsadar rayuwar da aka fara ta ranar 1 ga Agusta ta dakile harkokin tattalin arziki, musamman a Arewa.
Da ya ke karin bayani akan lamarin Shugaban kungiyar matasan jam’iyyar APC mai mulki Comr Olamide Lawal, ya zargi tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, da wasu ma da ya boye sunan su a matsayin wadanda ya zarga da shirya zanga-zangar.
A bangare guda kuma Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Ogun kan Harkokin Matasa, ya nuna rashin jin dadinsa na yadda wasu matasa suka toshe kunnuwansu daga kiran da shugaban kasa ya yi cikin jawabinshi ga kasa baki daya na dakatar da gudanar da zanga zangar.

Da ba a shafa wa Yahaya Bello da El-rufa’i kashin kaji ba, da sun tausashi zukatan masu zanga-zanga a arewa – Jigon APC

Wani mamba na kwamitin yakin neman zabe na shugaba Tinubu a jam’iyyar APC a zaben da ya gabata, Jesutega Onokpasa ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai a matsayin wandanda tuni za su tausashi zukatan masu zanga-zanga a yankin Arewa, ba domin an sha masu kai da tuhume-tuhume marasa tushe ba.
Jesutega ya kuma kara da cewa tsofaffin gwamnonin za su ɗauki gabarar magana a madadin shugaban kasa Bola Tinubu cikin wani salo domin su kwantar da hankulan mutane tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Onokpasa ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo wanda ya ke sukar masu mukamai da ‘yan arewa a gwamnatin shugaba saboda zarginsu da rashin ɗaukar wani mataki don kare gwamnatin Tinubu tare da tabbatar da kwanciyar hankali a tsakanin masu zanga-zangar ƙasa baki ɗaya.

Akwai bukatar Sanata Akpabio ya sauka daga mukaminsa – Jigon APC

Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sauka daga kujerar sa saboda zargin yi wa masu zanga-zangar yunwa habaici da ya ce masu zanga zangar na yi su kuma lokacin suna gidajensu suna cin abinci.
Duk da Akpabio ya musanta furta kalaman, a cikin wata sanarwa da ya fitar, Vatsa ya bayyana furucin a matsayin abin kunya ga jam’iyyar mai mulki, inda ya ce Akpabio yana nuna halin kyama irin na jam’iyyar daya fito ta PDP.
Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja ya bukaci Shugaban Majalisar Dattawa da ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri.
Kazalika Vatsa ya bayyana bawa Akbaio matsayin shugaban majisar dattawa da jam’iyayyar APC mai mulki ta yi a matsayin babban kuskure kuma abin cutarwa ga kasa ya kuma dangantaka hakan da dalilin rashin samun nasarar gwamnatin .

Jami’anmu ba su yi harbi da harsashi mai rai ba a lokacin zanga-zanga – IGP

 Jami’anmu ba su yi harbi a lokacin zanga-zanga ba – IGP

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ya ce babu jami’insu da ya yi harbi a lokacin zanga-zanga.

Sufeton ya bayyana haka ne a lokacin ya ke jawabi a taron shugabanin tsaro a ranar Talatar,a Abuja lokacin da yake kare zargin da aka yi wa jami’ansu na yin harbi a yayin zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi a Nijeriya.

Ya ce duk jami’in da aka gani da bakin kaya a ranar zanga-zanga ba jami’insu ba ne saboda ba kayan da suka saba sanyawa suka sa ba a ranar.

Sannan ya ce,sun kama masu dinka tutocin kasashen waje don su kai su wajen masu daukar nauyinsu.

Ko a jihar Kano ‘yan sanda sun fara gurfanar da wa’yanda ake zargi da tayar da tarzoma tare da bannata dukiyoyin al’umma a yayin zanga -zangar.

Mun shirya biyan N70,000 mafi karancin albashi – Gwamnatin jihar Nasarawa

Mun shirya biyan N70,000 mafi karancin albashi – Gwamnatin jihar Nasarawa

Gwamnatin Nasarawa ta ce a shirye take ta biya sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan jihar.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan harkokin al’umma Peter Ahemba ne ya bayyana haka a ranar Talatar a Lafia, babban birnin jihar a lokacin da ya ziyarci ofishin kungiyar ‘yan jarida da ke jihar.
Ya ce biyan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati ba wai kawai zai inganta jin dadin su ba ne har ma zai kara musu kwarin gwiwar gudanar da ayyuka.
A kan zanga-zangar da aka yi a fadin kasar, mai taimaka wa gwamnan ya yi kira ga al’ummar kasar da su kawo karshen zanga-zangar da kuma bin tafarkin zaman lafiya ganin cewa tuni gwamnati ta dauki matakin magance wasu korafe-korafensu.
Yace tsarin mulki ya tanadi ‘yan kasa su yi amfani da ra’ayoyinsu ta hanyar zanga-zangar lumana.
Ahemba ya bayyana cewa babu wata gagarumar zanga-zanga a jihar Nasarawa sakamakon kyawawan manufofi da tsare-tsare da Gwamna Abdullahi Sule ya yi na magance wahalhalun da al’ummar jihar ke fuskanta.

Dakatar da biyan harajin kayan abincin da ake shigowa da su daga waje zai rage farashin kayayyaki a Nijeriya – Shugaban Kwastam

Dakatar da biyan harajin kayan abincin da ake shigowa da su daga waje zai rage farashin kayayyaki a Nijeriya – Shugaban Kwastam 

Shugaban hukumar hana fasa kwauri a Nijeriya Kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce dakatar da haraji kan kayan abinci da magunguna da ake shigowa da su daga kasashen waje zai rage farashin kayan abinci.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin wani taron ganawa da shugabannin tsaro a Abuja kan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka na rage farashin kayan abinci.

Yace an shirya zanga-zanga ne akan abubuwa da dama, daya daga cikinsu shine kawo karshen hauhawar farashin kayayyaki”,Mun gano cewa ana shigo da abinci mai tarin yawa da ake amfani da shi a Najeriya. Don haka daya daga cikin abubuwan da shugaban kasa ya yi na rage tasirin farashin shigo da kaya shi ne dakatar da harajin kwastam da haraji kan kayan abinci da ake shigowa da su na wani lokaci.

“Mun yi imanin cewa idan aka aiwatar da hakan, zai taimaka wajen rage farashin kayayyakin abinci a kasuwanni.