DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 407

Kamala Harris ta zabi Tim Walz a matsayin mataimakin ta

Kamala Harris ta zabi Tim Walz a matsayin mataimakin ta

‘Yar takarar shugabar kasar Amurka ta jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta zabi gwamnan jihar Minnesota Tim Walz a matsayin abokin takararta a zaben shugaban kasa 

Harris ta sanar da hakan a ranar Talata, 6 ga Agusta, 2024.

Walz, mai shekaru 60, tsohon sojan Amurka ne kuma tsohon malami, an zabe shi a gunduma mai ra’ayin Republican a majalisar wakilai ta Amurka a 2006 kuma ya yi shekaru 12 kafin a zabe shi gwamnan Minnesota a 2018.

Ana ganin Walz a matsayin gwani wajen iya alaka da fararen fata, masu jefa kuri’a na yankunan karkara wadanda a shekarun baya-bayan nan suka kada kuri’a ga dan takarar Republican Donald Trump, abokin hamayyar Kamala.

Iyayen matashi dan shekara 25 da aka harbe yayin zanga-zanga a Kano sun nemi a yi musu adalci

Iyayen matashi dan shekara 25 da aka harbe yayin zanga-zanga a Kano sun nemi a yi musu adalci

Daya daga cikin iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a zanga-zangar da aka yi a Kano a makon jiya ta bukaci a yi musu adalci.

Akalla mutane takwas ne aka ruwaito an sun rasa rayukansu a rikicin da ya barke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a yankin Rijiyar Lemo da Kurna Asabe da ke karamar hukumar Fagge a ranar Asabar.

Bashir Muhammad Lawan mai shekaru 25 yana daga cikin wadanda aka kashe a lokacin da masu zanga-zanga a Rijiyar Lemo da ke kan titin Katsina suka yi artabu da ‘yan sanda.

Iyalan marigayi Bashir, suna alhinin rasuwarsa, sun shaida wa Daily Trust cewa an kashe dansu ne a lokacin da yake fafutukar kwato hakkinsa a matsayinsa na dan Najeriya.

Malam Muhammad Lawal, mahaifin Bashir, ya ba da labarin cewa an kashe dansa mintuna sha biyar kacal da barin gida don shiga zanga-zanga.

Ya kara da cewa wasu matasa da dama da suka hada da mata da kananan yara ne ake zargin ‘yan sanda sun harbe su a ranar.

A cewar wasu ‘yan uwan mamacin, ‘yan sandan sun fara harbin harsashi ne a lokacin da gungun masu zanga-zangar suka fara yi musu ihu suna cewa bamayi.

Khadija Bala, kanwar Bashir, ta ce yana gudu ne domin ya fake da harbin bindiga ya same shi.

Khadeejah tace sun yi zanga-zangar ne kawai amma an ce musu ‘yan daba,don haka muna son a yi masa adalci.

Duk da cewa gwamnatin jihar Kano ta sassauta dokar hana zirga-zirga amma a ranar Litininin an samu wasu matasa na zanga -zangar dauke da tutar kasar Russia.

Sai dai gwamnatin jihar ta sanar da cewa an kama wasu mutane 632 da ake zargi da wawure dukiyar jama’a a yayin zanga-zangar.

Kotu ta tsare wasu masu zanga-zanga 632 a Kano

Kotu ta tsare wasu masu zanga-zanga 632 a Kano

Wata kotu a Kano ta bayar da umarnin tsare wasu masu zanga-zanga 632 bisa zargin lalata kadarorin gwamnati da na al’umma a yayin zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.

Ana tuhumar su da laifin hada baki, sata, yin taro ba bisa ka’ida ba,tare da tada tarzoma, da kuma lalata ta abubuwa da dama.

Manyan masu shari’a uku ne suka jagoranci kotun,wadanda suka hada da babban alkali, Ibrahim Mansur-Yola, babbar mai shari’a Hadiza Rabiu-Bello, da alkali, Abba Muttaka-Dandago.

Kotun ta dage zaman har sai ranar 19 ga watan Agusta domin cigaba da sauraran shariar.

Tun da farko, Daraktan shigar da kara na Jiha (DPP), Salisu Tahir, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin da ake tuhumarsu ne a ranar 1 ga watan Agusta.

Ya yi zargin cewa a daidai wannan ranar ne wadanda ake kara a lokacin zanga-zanga, sun barnata dukiyoyin gwamnati da na al’ummar jihar.

“Wadanda ake tuhumar sun shiga cikin shagunan mutane sun yi awon gaba da kayayyakinsu, da dukiyoyi da dama kamar yadda ya shaida

Mai gabatar da kara ya ce laifukan sun ci karo da sashe na 97, 287, 229, 336, 349 da 247 na kundin laifuffuka.

Yayin da wasu daga cikin wadanda ake tuhumar suka amsa laifinsu, wasu kuma sun musanta aikata laifin.

Da yake zantawa da manema labarai, bayan zaman kotun, babban lauyan gwamnatin jihar, Haruna Isa-Dederi, ya ce gwamnatin jihar ta kafa kotunan tafi da gidanka guda uku domin gurfanar da wadanda ake tuhuma.

Isa-Dederi ya bayyana cewa za a yi nazari kan kundin da ma’aikatar shari’a ta bayar da shawarwarin da suka dace kafin ranar da za a dage cigaba da sauraren karar.

APC ta yi tir da harin da aka kai sakatariyar jam’iyyar a Zamfara

APC ta yi tir da harin da aka kai sakatariyar jam’iyyar a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da masu zanga-zanga suka kai sakatariyar jam’iyyar ta jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Litinin.

Sanarwar tace jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da wasu bata-gari da suka kai hari a yayin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa.

“Ko a ranar juma’ar da ta gabata, jam’iyyar APC ta gargadi gwamnatin jihar kan yadda ta bar wasu bata gari suna huce haushin su kan APC da shugabannin ta.

Yace a kwanakin nan wasu bata gari sun yi amfani da zanga-zanga wajen kai hari gidan Sen. Sahabi Ya’u a Kauran Namoda da kuma yunkurin rusa gidan tsohon Gwamna Bello Matawalle da ke Gusau.

Ya kuma ce jam’iyyar ta kuma roki jami’an tsaro da su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

“Babban abin bakin ciki ya faru ne a Litinin, yadda bata gari da sunan zanga-zanga suka mamaye Sakatariyar jam’iyyar APC da ke kan titin Sokoto Bye Pass Road, Gusau, tare da lalata wuraren da suka hada da gilasai da kofofi da kayan ofisoshi tare da kwamfutoci da aka kwashe a ofisoshin.

Yayi kira mambobi da magoya bayan jam’iyyar da masu fatan alheri da su ci gaba da kasancewa cikin masu bin doka da oda dan samun zaman lafiyar jihar

Gwamnatin tarayya ta bayyana hanyoyin da ma’aikata za su sayi shinkafa 50kg akan kudi 40,000

Gwamnatin tarayya tayi kira ga ma’aikata da su yi rijistar sayen shinkafar da za ta sayar mai nauyin 50kg akan kudi dubu 40,000

Gwamnatin tarayya tace ta kammala shirin sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 a kan Naira 40,000 ga ma’aikatan gwamnati da nufin magance matsalar karancin abinci da ke addabar al’ummar kasar.

A wata wasika daga ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatin tarayya mai dauke da sa hannun daraktan ma’aikatar, Jaiyesimi Abimbola, ta sanar da hakan.

An bayyana cewa za a gudanar da biyan kudin da kuma rabon shinkafar ne ta ofisoshin da aka kebe yayin da shugaban kungiyar hadin gwiwa na ma’aikatar zai kasance mai sa ido kan yadda ayyukan zasu kasance

Sanarwar tace a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin an shawo kan matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar nan, an umurce ni da in sanar da ku cewa, za a sayar da buhunan shinkafa 50kg a kan kudi naira 40,000 kacal a kan kowane buhu ga ma’aikatan gwamnati masu bukata.

An sanar da cewa, ana buƙatar duk ma’aikatan da ke da sha’awar su cika fom na Google akan gidan yanar gizon OHCSF, https://www.ohcsf.gov.ng, buga, kuma a mika su ga Darakta, HR, don amincewa.

A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta ce ta samar da cibiyoyi a fadin kasar nan inda ‘yan Nijeriya za su iya siyan buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan Naira 40,000.

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma na kasa, Muhammed Idris, ya ce shirin na daya daga cikin wasu tsare-tsare da gwamnatin Tinubu ta yi na saukaka yanayin rayuwa ga ‘yan kasa.

Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olushegun Obasanjo ya ce rashin samar da aiki yi ga matasan kasar na iya zama wani abin far fargaba

 Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olushegun Obasanjo ya ce rashin samar da aiki yi ga matasan kasar na iya zama wani abin far fargaba

Tsohon shugaban Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda matasa ke tashe-tashen hankula sakamakon rashin aikin yi.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels.

Yace yana fargabar matasa na cikin tarin matsaloli na rashin ilimi tare da rashin aikin yi,kuma dole sai an tashi tsaye dan gudun kada abin yafi karfin mu indai hakan ta kasance toh addu’a itace kawai magani.

Bayanin nashi ya zo ne biyo bayan zanga-zangar da matasa keyi a fadin kasar kan tsadar rayuwa a fadin kasar.

Tun a ranar 1 ga watan Agusta ne dai matasa a fadin Nijeriya suka fara zanga-zanga, lamarin da tun a ranar 1 ga watan Agusta ke kara ta’azzara inda aka rika samun rahotanni da tashe-tashen hankula da sace-sace a fadin kasar.

Mazauna garin Kano na fuskantar karancin kayan masarufi tun bayan da aka rufe Kasuwanni

Mazauna garin Kano na fuskantar karancin kayan masarufi tun bayan da aka rufe Kasuwanni

Mazauna garin Kano sun ce suna fuskantar karancin kayan masarufi kamar sukari, gari da sauran kayayyaki yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a wasu sassan jihar, wanda hakan yasa kasuwanni da manyan shaguna ke rufe.

Daily Trust ta rawaito cewa bincike ya nuna yadda yawancin shagunan dake unguwanni a Kano kayan su sun kare saboda har yanzu manyan kasuwannin a rufe suke.

Duk da cewa gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita na tsawon sa’o’i shida, amma har yanzu yankuna da dama a cikin babban birnin jihar na fama da karancin kayayyakin masarufi.

Malam Bello Bashir, wani mazaunin Unguwar Sharada da ke karamar hukumar Birni, ya ce a halin yanzu gari da sikari da sauran kayayyaki sun yi karanci a cikin al’umma,kuma hakan yasamo asaline kan rashin bude kasuwanni da ake yi.

Binciken ya kuma nuna cewa farashin kayayyakin da ake da su ya karu sossai domin karancin su da ake samu.

Asusun NELFUND na gwamnatin Tinubu ya bai wa daliban jami’o’i 6 tallafin N20,000 ga kowane dalibi 20,000

Asusun ba da bashin karatu na Nijeriya NELFUND ya sanar da ba da wani hasahin N20,000 ga dalibai 20,371 a jami’o’i na kasar nan na watan Juli, 2024.
Daraktan kudi na asusum Mr Ibom Uche ya sanar da hakan a ranar Litinin a wata sanarwa da ya fitar.
Ibom Uche ya lissafto jami’o’in da suka hada da jami’ar Bayero, Kano, jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, jihar Katsina, Jami’ar Ilori, jihar Kwara, Jami’ar Benin jihar Edo, jami’ar Ibadan jihar Oyo da jami’ar Maiduguri a jihar Borno.
Daraktan ya ce wannan ya nuna karara irin zuar Shugaba Tinubu na ganin ya tallafi dalibai domin su cika burikan da suka sa a gaba a fadin kasar nan.
Ya ce wannan asusu na aiki domin ganin ya raba wa dalibai wannan hasahi daga karin jami’o’i 55 na kasar nan domin su ma su amfana.

‘Yan sanda sun kama mutane masu yawa da ke yawo da tutar kasar Russia

‘Yan sanda a Nijeriya sun sanar da kama mutane 30 da ake zargi da daga tutar kasar Russia a yayin da suke gudanar da zanga-zanga a kasar.
Kazalika, rundunar ‘yan sandan ta sanar da kama wani mutum mai suna Ahmad Taylor da ake zargi da samar da wannan tuta a Kano da wasu sassan kasar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Nijeriya ACP Olumuyiwa Adejobi ya sanar da hakan a hedikwatar rundunar tsaron DSS a wani taron manema labarai na hadin guiwa da suka kira a Abuja.
Bayanai dai sun ce an samu karuwar masu daga tutar kasar Russia a wasu jihohin Nijeriya irinsu Kano, Kaduna da Katsina a lokacin gudanar da zanga-zangar da ke gudana a kasar.

An saki Bobrisky daga gidan gyaran hali na Kiri-kiri

Sannannen mai sha’awar shiga irin ta mata din nan Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya shaki iskar ‘yanci bayan da ya fita daga gidan gyaran hali na Kiri-kiri a Litinin din nan.
Bobrisky dai ya kwashe watanni 6 tsare a gidan yari bayan da kotu ta kama shi da laifin ‘likin’ kudi na irin na gadara a wajen wata walima.
A ranar 12 ga Afrilun, 2024 ne dai aka yanke wa Idris hukuncin daurin watanni 6 bayan da kotu ta same shi da wannan laifi na cin zarafin takardar Naira.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati, EFCC dai ce ta maka Idris Okuneye kotu bayan da ta zarge shi da wulakanta Naira, kotun kuma ta same shi da laifin, ta yanke masa hukunci.