Sojoji sun karbe mulki a kasar Bangladesh
Tirela 20 ta shinkafar da gwamnatin tarayya ta ce ta ba jihohi, ba ta iso hannunmu ba – Gwamnan Gombe
Gwamnatin tarayya ta sa kafa ta shure abin da ta kira ikirarin da Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya yi, na cewa har yanzu jiharsa ba ta karbi tirela 20 ta tallafin shunkafar da gwamnatin tarayyar ta ce ta rarraba wa jihohi ba.
An garzaya da wasu iyalai asibiti bayan sun sha wani kunu
Masu zanga-zanga zasu sauya akãla zuwa birnin taraiya Abuja daga ranar Litini
Da alama masu zanga-zangar adawa da tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu basu gamsu da jawaban da yayi ga ‘yan ƙasa ba, a maimakon kawo karshen gangamin, yanzu haka shirin shiga Abuja masu zanga-zangar suke.
Rahotanni sun nuna cewa masu gangamin suna wallafawa a shafin nan mai taken #OccupyAbuja cewa zasu dunguma kuma zuwa birnin taraiyar ƙasar domin cigaba daga inda suka tsaya.
Sauran wallafe-wallafe da aka yi ta yi a shafin na twitter ciki har da na tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyar African Action Congress Omoyele Sowore da sauran su, na nuna alamun zanga zanga zata yi zafi a Abuja.
Wasu mabiya addinin Kirista sun gudanar ibadar Lahadi a filin zanga-zanga a jihar Plateau
Ɗaruruwan masu zanga-zanga mabiya addinin kirista da suka saba Ibadar Lahadi a Coci, a wannan karon sun gudanar da wadannan addu’o’in nasu a matattarar zanga-zanga da ake a jihar Plateau.
Wannan ibada ta nuna hadin kai a fili, saboda a lokacin da suke wannan ibada mabiya addinin Musulunci ne ke kewaye da su suna basu kariya.
Ɗaya daga cikin limaman Cocin dake jagorantar majami’ar El-Buba Outreach Ministries da ke Jos, Pastor Isa El-Buba ya jaddada bukatar gwamnatin Najeriya ta kawo ƙarshen yunwa da rashin tsaro da suka addabi ‘yan ƙasar.
A ranar Juma’a ma anga yadda mabiya addinin kiristan suka bada tsaro ga Musulumai da ke Sallar Juma’a a lokacin zanga-zanga, wacce aka fara ta ranar Alhamis ɗaya ga watan Agustan nan da muke ciki
Amnesty International ta bukaci gwamnan Kano ya kafa kwamitin gano yadda zanga-zanga ta kazance a jihar
Mun sayo kayayyakin noma na zamani, don kawo ƙarshen yunwa a Nijeriya – Shugaba Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya sanar cewa gwamnati ta sayo kayan noma na biliyoyin Naira dan kawo ƙarshen yunwa a ƙasar.
Tinubu a jawabin da yayi ga ‘yan Najeriya Lahadinnan ya ce wannan mataki zai taimaka gãya wurin samar da wadataccen abinci mai rahusa a ƙasar.
Ya kuma ce yana ganawa da gwamnoni da wasu ministoci dan ganin an cimma hakan, sa’annan gwamnati ta raba taki ga manoma inji shugaba Tinubu dan cika wannan buri na gwamnati.
Tinubu ya ce ya fahimci tsanani da ya ingiza jama’a yin zanga-zanga amma duk da haka bai kamata a bari tashin hankali ya daidaita ƙasar ba.
Bama cikin wadanda suka yi ƙone ƙone a zanga-zangar Kano-Ƙungiyar Kano Peace Ambassadors
Ƙungiyarnan ta Kano state Peace Ambassadors mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya ta nisanta kanta daga ƙone-ƙone da aka yi lokacin zanga-zanga da aka yi ranar Alhamis a Kanon.
Shugaban ƙungiyar Nasiru Usman Na’ibawa ya ce sun gudanar da zanga-zanga mai tsafta daga ofishin su da ke titin Aufu Baƙo zuwa fadar Sarki Sunusi, suka miƙa masa takardar koken jama’a.
Ya baiyana cewa sun so su mika wata wasikar kuma ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf amma shawarar da jami’an tsaro suka basu ya sa suka fasa.
Ya ce shugaba Tinubu yana bukatar ƙarin lokaci dan magance matsalolin ƙasar, yana kuma shawartar ‘yan Najeriya suka tsãme kansu daga zanga zangar da ake domin ta fara haifar da ɗa mara ido.
Shugaba Tinubu na bibiyar abubuwan da ke wakana game da zanga-zanga a Nijeriya – Bagudu
Ministan Kasafi da kula da lamurran tattalin arzikin Najeriya Atiku Bagudu ya ce shugaba Tinubu na nan yana bibiya tare da nazarin abubuwa da ke faruwa a zanga-zangar da ake yi wa gwamnatin sa.
An samu ƙiraye-kiraye kan shugaba Tinubu ya ce wani game da wannan zanga-zanga a yayin da ta shiga rana ta uku, abinda Bagudu ke cewa ai yana sane sarai da abubuwan da ke wakana.
Ministan ya amince cewa ‘yan Najeriya suka cikin mayuyacin hali, amma yana bada tabbacen shugaba Tinubu yana aiki tukuru da zummar ganin an sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya.



.png)



