DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 409

Shurun da shugaba Tinubu ya yi ne ya ƙara fusata ‘yan Najeriya – zargin da jami’yar PDP ta yi

Babbar jami’ar adawa a Najeriya PDP ta ce rashin fitar shugaba Tinubu ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya ya yi matuƙar baiyanawa cewa gwamnatin jam’iyar APC ba mai tausayin talakawan Najeriya ba ce, duk da yanayi na tausayawa da ‘yan ƙasar suka shiga.

A wata sanarwa da mamakin PDP na ƙasa Debo Ologunaba ya fitar jam’iyar ta caccaki shugaba Tinubu tare da nuna buƙatar ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya yadda za’a fitar da ‘yan ƙasa daga ƙangi da suka shiga.

Jam’iyar PDP ta ce saboda yanayi na ƙangi da ‘yan ƙasar ke ciki ya sanya suka fara zanga-zanga ranar Alhamis ɗaya ga wannan wata na Augusta amma shugaba Tinubu bai ce uffan ba duk da irin hatsaniya da ake samu a sanadin wannan zanga-zanga.

PDP ta ce Duniya na gani yadda gwamnatin APC ke amfani da jami’an tsaro wurin cin zarafin masu zanga-zanga, tana zargin har ma da kisan wasu daga cikin ‘yan zanga-zangar Najeriya.

Kwamitin zaman lafiya a Kano yayi Allah Wadai da abinda ya faru lokacin zanga-zanga.

Kwamitin ya bayyana hakan ne ta wani saƙon murya da shugaban sakatariyar Ambasada Ibrahim Waiya ya fitar ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Bashir A Bashir. 

Kwamitin zaman lafiyar ya bayyana takaicin sa da irin yadda matasa ke bada dãma wasu na amfani dasu wajen lalata kadarorin gwamnati da na ƴan kasuwa da sunan siyasa. 

Shugaban kamirin Ambasada Waiya ya cigaba da cewa tun farko shugabannin zanga-zangar suna da laifi la’akari da yadda aka bayyana musu Abunda ka iya faruwa idan suka ce sai sun gabatar da wannan zanga-zanga amma sukai burus da kiraye-kiraye suka fita, sai kuma gashi abunda suke hange ya afku.

Ambasada Waiya ya kuma nuna takaicin kwamitin bisa kwashe kayan ofishin hukumar Sadarwa ta ƙasa dake hanyar zuwa gidan gwamnati inda yace ba iya kanawa ne sukai asara ba har da jihohin arewa maso gabas, domin shine guri ɗaya tilo da Najeriya ta samar domin koyar da al’ummar arewa harkokin sadarwa.

A ƙarshe kwamitin na zaman lafiya na jihar Kano yaja hankalin masu tada wannan husuma tare da tunatar dasu gobe ƙiyama domin rai zai girbi duk abinda ya shuka.

Kada a yi amfani da ku wajen lalata Kano, Sarki Sanusi ya fadawa masu zanga-zanga

Kada a yi amfani da ku wajen lalata Kano, Sarki Sanusi ya fadawa masu zanga-zanga

Mai martaba Sarkin Kano na 16,Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga al’umma da kada su bari a yi amfani da su a yi barna a Kano da Arewa da ma kasa baki daya.

Sarkin ya yi wannan kirane lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadarsa dake gidan sarki na cikin garin kano.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu masu zanga-zangar suka sake haduwa a Tudun Wada da ke karamar hukumar Nassarawa a Kano, a yammacin ranar Juma’a.

Sun sake haduwa bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sassauta dokar hana fita domin ba musulmi damar gudanar da Juma’a.

Da yawa daga cikinsu na rike da alluna yayin da wasu ke rera waka da tafawa yayin da suke tafiya bayan wani matashi ya yi musu jawabi.

A lokacin da yake tattaunawa da manema labaran a yammacin Juma’a, sarkin ya nuna matukar damuwarsa kan yadda aka wawure dukiyoyin jama’a da na wayanda basuji ba basu gani ba, sakamakon zanga-zangar da aka ce za’a da gudanar cikin lumana don nuna adawa da yunwa da kuncin rayuwa a kasar.

Sarkin ya ce abin da ya faru koma baya ne ga jihar da yankin arewa da ma kasa baki daya.

Ya ce, “Yau rana ce ta bakin ciki ga al’ummar Kano yayin da muke tunani kan abubuwan da suka faru a jiya. Rikicin na jiya shi ne abin da masana da shugabanni suka yi ta gargadi kan yiwuwar zanga-zangar  lumana tare da yin amfani da wannan damar wajen haifar da tarzoma wanda ya kai ga hasarar rayuka da lalata dukiyoyi da jikkata mutane da dama.

Kamar yadda muka fada yayin taron masu ruwa da tsaki, duk wani tashin hankali a Kano yana cutar da mutane wanda basu da laifi. Matasan da suka mutu ‘ya’yanmu ne, dukiyar da aka kona aka sace ta mutanen Kano ce.An lalata kayan gwamnati kuma kudin al’umma za a dauka domin siyan wasu kayayyakin don haka babu wani abu da wannan abu ya haifar in ba koma baya ba.

Peter Obi ya musanta jagorantar zanga-zangar Abuja da akace ya yi

Peter Obi ya musanta jagorantar zanga-zangar Abuja da akace ya yi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben shekarar da ta gabata, Peter Obi, ya musanta cewa ya jagoranci zanga-zangar adawa da yunwa da tsadar rayuwa a babban birnin tarayya Abuja ranar 1 ga watan Agusta.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne matasan kasar nan suka gudanar da zanga-zangar kira ga shugaba Bola Tinubu da ya duba halin da suke ciki.

A cewar masu shirya taron, ya kamata a yi zanga-zangar lumana sai dai zanga-zangar ta yi sanadin asarar rayuka da barnata dukiyoyi da kimarsu ta kai na daruruwan miliyoyin naira.

Akalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu a manyan biranen wasu jihohin kasar yayin da ake gudanar da zanga-zangar.

Bayan haka, wasu bata gari sun yi amfani da wannan zanga-zangar sun wawure kayayyaki masu mahimmanci na jama’a da sauran mutane.

A cikin sakon da ya fitar ta hanyar X ranar Juma’a, Obi ya ce bidiyon da aka ce an ganshi yana jagorantar zanga-zanga a abuja wani yunkuri ne na bata masa suna.

A cewarsa, an dauki hoton bidiyon ne a ziyarar da ya kai hedikwatar jam’iyyar Labour, inda ya sasanta rikicin da ya barke tsakanin jam’iyyar LP da kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC.

“Wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, wanda ake zaton yana nuna ina jagorantar zanga-zanga a Abuja, shi ma karya ne. A gaskiya an dauki hoton bidiyon ne a ziyarar da na kai Hedikwatar Jam’iyyar Labour, inda na sasanta rikicin da ya barke tsakanin Labour Party da NLC.

Tsohon gwamnan na Anambra ya ce an hada wannan bidiyon ne kawai don bata masa suna,amma bashi da wani sahihancin abin da ake fada akai.

Kaduna Electric ta ya yanke wutar lantarkin gidan gwamnatin jihar

Kaduna Electric ta ya yanke wutar lantarkin gidan gwamnatin jihar

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KEDCO) ya yanke lantarkin gidan gwamnatin Kaduna saboda bashin sama da Naira biliyan 2.9 da yake bi.

Kamfanin a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashen sadarwa na kamfanin Abdulazeez Abdullahi, ya ce gidan gwamnati bai biya kudin wutar da aka ci ba cikin watanni bakwai.

Idan ba a manta ba a safiyar ranar Juma’a ne gwamnatin jihar ta hannun hukumarta ta haraji, hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS) ta rufe kanfanin wutar lantarkin dake bin sama da naira miliyan 600 na haraji.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A wani gagarumin yunkuri da ke nuna yadda ake samun takun saka tsakanin masu samar da wutar lantarki da gwamnatocin Jihohi, kamfanin Kaduna Electric ya yanke wutar lantarki a gidan gwamnatin jihar Kaduna da sauran asusun gwamnatin jihar saboda rashin biyansu kudi.

Kamfanin na Kaduna Electric ya sanar da katse huldar ne bayan kokarin da aka yi na magance matsalar ta hanyar tuntubar juna da sulhu a tsakanin su.

Ya ce duk da biyan Naira miliyan 256 da aka yi a kwanakin baya na wutar lantarki da ake amfani da su a tsakanin Satumba 2023 zuwa Disamba 2023, bashin da gwamnatin Jihar Kaduna ta biya ya ci gaba da yawa, wannan bai kai a cire ba.

Matakin da kamfanin Kaduna Electric ya dauka na yanke wutar lantarkin ya biyo bayan kokarin da aka yi na shawo kan matsalar biyan kudin, ciki har da tuntubar jami’an jihar da dama. Sabanin haka, sauran jihohin da ke karkashin kamfanin Kaduna Electric, wato Sokoto, Kebbi, da Zamfara, sun ci gaba da kula da asusunsu yadda ya kamata, tare da biyan bukatunsu na biyan kudin wutar lantarki da sauran hakkokinsu na biyan wutar lantarki da Kaduna Electric.

Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya kuma nemi Tinubu da ya saurari al’umma

Atiku ya jinjinawa masu zanga-zanga, ya kuma nemi Tinubu da ya saurari al’umma 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jinjinawa ‘yan Najeriya da suka fito kan tituna domin nuna adawa da gwamnatin babban abokin hamayyarsa a zaben da ya gabata.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Atiku ya yabawa ‘yan Najeriya bisa jajircewar da suka nuna yayin da ya yi Allah wadai da wayan da  suka yi sace sace a yayin zanga-zanga a wasu jihohin.

Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su lura da yadda suke gudanar da ayyukan su,su kuma daina muzgunawa ‘yan jarida da masu zanga-zanga da harbe harbe.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta saurari mutane tayi abin da al’umma suke so

Yace fara zanga-zangar da jama’a suka yi a fadin Nijeriya ya nuna rashin amincewa da manufofin gwamnati, tare da ci gaba da tattaunawa mai mahimmanci game da shugabanci nagari a cikin al’ummarmu.

“Ina kira ga masu zanga-zangar da su yi cikin lumana tare da yin kira ga ‘yan Najeriya da su kara nuna goyon baya da goyon bayan zanga-zangar lumana ta #EndBadGovernance. Wannan wani muhimmin lokaci ne da za a ji muryarmu ta gama gari, kuma dole ne a yi shi cikin mutunci da mutunta doka.

“Ina kuma kira ga ‘yan sanda da su kara kaimi wajen tafiyar da wadannan masu zanga-zangar. Kisan gillar da jami’an tsaro ke yi wa ‘yan kasa ba gaira ba dalili abu ne da ba za a amince da shi ba. Dole ne ‘yan sanda su guji cin zarafin ‘yan jarida da ke ba da rahoton zanga-zanga. Ya zama wajibi hukumomin tsaro su yi taka-tsantsan wajen tabbatar da doka da oda.

An sassauta dokar hana fita a jihar Borno don gudanar da sallar Juma’a

 An sassauta dokar hana fita a jihar Borno don gudanar da sallar Juma’a

Gwamnatin jihar Borno da hukumomin tsaro na jihar sun sassauta dokar hana fita da aka kafa a jihar daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3,domin ba da damar musulmai suje sallar Juma’a.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno ASP Nahum Kenneth Daso ANIPR, ya rabawa manema labarai , sanarwar tayi kira ga jama’a da su yi sallar Juma’a a masallatai dake kusa da su.

Sanarwar ta cigaba da cewa dokar zata ci gata daga karfe 3 na yammacin Juma’a zuwa karfe shida na safiyar  ranar Asabar, bayan haka ana sa ran mutane za su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Tace hukumomin tsaro na jihar na neman hadin kan al’ummar don tabbatar da tsaron rayukan al’ummar jihar baki daya.

Jam’iyyar PDP ta nemi Tinubu ya sake duba manufofi gwamnatin sa

Jam’iyyar PDP ta nemi Tinubu ya sake duba manufofi gwamnatin sa

Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da ta gaggauta sake duba duk wasu manufofinta da tsare-tsare daya dagula rayuwar kasar nan.

Jam’iyyar ta ce jam’iyyar APC ta jefa Nijeriya cikin mawuyacin hali, ta kuma bukaci shugaba Tinubu ya yi wa al’ummar kasar jawabi kan hanyar da za a bi wajen shawo kan lamarin.

Jam’iyyar adawar ta yi nuni da cewa zanga-zangar da ‘yan Nijeriya suka yi a fadin kasar ba za ta faru ba idan da a ce gwamnatin APC ta nuna gaskiya da jajircewa wajen magance wahalhalun da ke faruwa a halin yanzu sakamakon rashin aiwatar da ingantattun manufofi.

Sakataren yada labaran PDP na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya bayyana cewa, “Yan Nijeriya za su iya tunawa cewa jam’iyyar PDP a lokuta da dama ta ba gwamnati shawarwari kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Abin baƙin ciki, waɗannan shawarwari ba su samu karbuwa ba,wanda hakan yasa ake halin da ake ciki yanzu

Hadin kai tsakanin hukumonin tsaro tare da masu ruwa da tsaki nada matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro-Christoper Musa

Hadin kai tsakanin hukumonin tsaro tare da masu ruwa da tsaki nada matukar muhimmanci wajen tabbatar da tsaro-Christoper Musa

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya ce rundunar soji na ci gaba da wayar da kan sojoji kan hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin kare makarantu daga hare-hare.

Ya bayyana haka ne a yayin bude taron kwana biyu kan makarantun tsaro a hedikwatar runduna ta daya ta sojojin Nijeriya dake Kaduna, CDS ya jaddada muhimmancin samar da muhimman abubuwa kamar babura da na’urorin sadarwa domin isa makarantu cikin hanzari a lokacin da ake bukata.

Wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Emeka Onumajuru, ya ce, “Rundunar Sojin Nijeriya ta ‘yan Nijeriya ce kuma za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kare al’umma, tare da yin aiki da dukkanin hukumomin tsaro.

Babban kwamandan rundunar soji ta daya (GOC), Manjo Janar Mayirenso Saraso, ya kuma yi kira da a hada kai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaro a makarantun jihar.

Kwamishinan tsaro na harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce tsakanin watan Yulin 2021 zuwa Maris 2024, jihar Kaduna ta fuskanci sace yara ‘yan makaranta da dama.

Irin illar da masu zanga-zanga suka yi wa ‘yan sandan Nijeriya, IGP ya magantu

Babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya IGP Kayode Egbetokun ya ce zanga-zanga da aka gudanar a ranar Alhamis, ta yi sanadiyyar mutuwar dan sanda da raunata da dama.
Kazalika, IGP Egbetokun ya ce zanga-zangar ta kuma yi sanadiyyar lalata ofisoshin ‘yan sanda a sassan kasar.
A taron manema labarai a daren Alhamis a Abuja, IGP Kayode Egbetokun bai ce uffan ba game da zargin kisan fararen hula a yayin zanga-zangar ba a fadin kasar.