DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 410

Yan yankin Neja Delta basu da dalilin yin zanga-zanga ga Tinubu inji ministan harkokin yankin

 

Ministan harkokin Neja Delta Injiniya Abubakar Momoh yace, al’ummar yankin Kudu maso Kudu ba su da dalilin yin zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu.

Mininstan ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati a yau ranar Laraba, Ministan ya ce hakan ya faru ne saboda shugaban kasar ya gudanar da ayyuka da dama da nufin bunkasa yankin ba kawai ba, har ma da karfafa matasa.

Ya kara da cewa, a yankin na Neja Delta, Shugaban kasa ya yi abubuwa da yawa kuma ba ya tunanin duk wani dan yankin Neja Delta zai ga ya dace ya fito ya ce yana zanga-zangar adawa da rashin shugabanci.

Daga karshe yayi kira ga matasan da su ci moriyar ayyukan da gwamnati tay, kada su lalata komai don su ne manyan gobe kuma su zasu ci moriyar su.

Naja’atu Mohd, Usman Yusuf, Umar Ardo, Salihu Lukman sun goyi bayan matasa kan zanga-zanga

 

MUNA TARE DA MATASAN MU

Wannan
sanarwar ce ga manema labaru a kan zanga-zangar da ake shirin yi, da aka fitar
da ita a ranar 31 ga watan Yuli wadda dattajan arewacin Najeriya da suka hada
da Professor Usman Yusuf da Naja’atu Muhammad da Malam Salihu Lukman da Dr.
Ardo Umar suka fitar a birnin Abuja. 
 

——-

Mu dattawan Arewa kuma ginshikai da ke
da ruwa da tsaki a ƙasar nan muka yi wannan rubutu domin tsayar da matsaya a
kan babban lamari da ya shafe mu duka.

 

Kamar yadda kuka sani, ƙasarmu ta dade
tana fama da matsaloli ba ‘yan kaɗan ba ɓangaren rashin tsaro, da tsananin
talauci, da tsananin yunwa da jahilci  da
rashin aikin yi, da cututtuka da tsananin tsadar rayuwa, da duk rashin
shugabanci na gari da rashawa a ofisoshi ne gwamnati suka haddasa su.

 

Muna sane cewa babbar manufar dukkan
wata gwamnati ita ce kare rayuka da dukiyar jama’a da kyautata jin dadin
al’ummar kasa. Duk  gwamnatin da ba ta
iya samar wa al’ummarta wadannan muhimman haƙƙoƙi nasu to ta rasa huruminta na
ci gaba da kasancewa a madafun iko, kuma ko shakka babu za ta gamu da fushin
‘yan ƙasa. Saboda haka za ta iya ci gaba da kasancewa a kan mulki ne ba da fatan
alheri daga jama’a ba.

 

Da alama yanayin da ake ciki ke nan a
Najeriya, inda ƙasarmu, abar ƙaunarmu Nijeriya, ta dosa ke nan.

Shekaru da dama gwamnatocin da suka
gabata a dukkan matakai, ciki har da gwamnatoci da ke ci a yanzu, sun gaza
samar da shugabancin da ake buƙata.

 

Saboda haka aka jefa ‘yan Nijeriya cikin
mawuyacin hali, na rashin sanin inda rayuwarsu ta dosa, ga ƙunci da sauransu
musamman matasa.

 

Domin matasa su bayyana buƙatunsu kan
tsadar rayuwa, da matsalar tsaro, da lalacewar lamura, suka sa matasan Nijeriya
suka yanke shawarar gudanar da zanga-zanga ta ƙasa baki-ɗaya daga 1 zuwa 10 ga
watan Agusta.

 

Saboda
haka muka rubuta wannan sanarwa ta musamman domin bayyana matsayinmu a game da
wannan zanga-zanga da matasa suka tsara da kuma halin da gwamnati take nunawa a
kan zanga-zangar.

 

Da farko muna so mu jaddada kariyar da
tsarin mulki ya ba kowanne ɗan ƙasa a ‘yancin da yake da shi na yin taro da
kuma yin zanga-zanga.

 

Har ila yau muna jaddada cewa dalilan da
suka haddasa zanga-zangar dalilai ne masu ƙwari.

Saboda haka muke bayyanawa ɓaro-ɓaro
cewa muna tare da matasanmu a wannan gwagwarmaya tasu ta aiki da ‘yancin da
suke da shi na gudanar da zanga-zanga.

Na biyu muna kira ga gwamnatin tarayya
ta zama mai sanin ya kamata wajen warware wannan matsala idan har tana so ta
warware cikin ruwan sanyi da kauce wa dukkan wata matsala da ke tattare da
gagarumar zanga-zanga. Saboda haka muke ba gwamnati shawarar ta hanzarta ɗaukar
waɗannan matakan:

 

 1. Tattaunawa: Gano shugabannin matasan da
masu zanga-zangar tare da ganawa da su kai tsaye domin fahimtar
ƙorafe-ƙorafensu da kuma magance musu su. Ɗora wa wasu wannan aiki kamar irin
su sarakuna, da shugabannin addini, da shugabannin kwadago da na farar hula ba
zai yi aiki ba.

 

Amfani da ƙarfin tuwo wajen tursasa wa
masu zanga-zangar zai ƙara sa yanayin da ake ciki ya ƙara ta’azzara ne. Mun dai
ga yadda zanga-zangar EndSARS ta wanye.

 

2. Aiwatar da sauye-sauye: A duba
buƙatun masu zanga-zangar tsakani da Allah ta hanyar aiwatar da sauye-sauye
masu ma’ana, da nuna fata ta gari da dukufa ga canji.

 

3. Ba da goyon baya ga karfafa matasa: A
zuba jari ga tsare-tsare na ci gaban matasa, da iliminsu da dabaru na bunƙasa
kasuwancinsu.

 

4. Bunƙasa ci gaban tattalin arziki:
Aiwatar da tsare-tsare da za su kyautata ilahirin ci-gaban tattalin arzikin
ƙasa.

 

5. Kyautata shugabanci: Gaskiya da riƙon
amana da damawa da kowa a sha’anin shugabanci, maimakon shugabanci na son- kai
da-baba-kere, da magance rashawa da tabbatar da dama iri guda ga dukkan ‘yan
ƙasa.

 

6. Tabbatar da tsaro: A tabbatar da
jami’an tsaro na ƙasa sun mutunta ‘yancin da masu zanga-zangar suke da shi ta
hanyar ƙyale su, su gudanar da taronsu cikin ruwan sanyi ba tare da musu
katsalandan ba, ko tursasa musu ko cin zarafinsu ba, tare da kare su daga
dukkan wata illa ko rauni.

 

7. Shugabanci abin koyi: Ya kamata
gwamnati da shugabanninta su nuna shugabanci abin koyi, nuna sadaukar da kai,
da kima, da martaba domin cusa ƙauna da amincewa.

 

A
matsayinsa na wanda shi da kansa ya jagoranci zanga-zanga daban-daban daga
lokacin kungiyar NADECO zuwa shekara ta 2014, Shugaba Tinubu ya fi kowa sanin
darajar zanga-zanga.

 

Ga
su kuma matasa masu zanga-zanga, muna so mu tabbatar muku cewa mun fahimta tare
da ba da goyon bayan wannan shawara da kuka yanke ta aiki da ‘yancin da kundin
tsarin mulki ya ba ku ta gudanar da zanga-zanga ta lumana domin neman
shugabanci na gari da gaskiya daga shugabanku.

 

Mun yi imanin cewa wannan mataki ne
halastacce kuma matakin da ya wajaba domin kyautata alƙiblarku da tabbatar da
Nijeriya ta mana daɗi gaba ɗayanmu.

 

A matsayinmu na dattawa, a lokacin da
muke tafiya kafaɗa-da-kafada da ku a kan wannan, muna kira a gare ku, ku ci
gaba da kasancewa masu zaman lafiya da kiyaye doka a lokacin wannan
zanga-zanga, da kauce wa dukkan wani abu da zai iya zamewa tashin hankali, ko
illa, ko ɓarna ko barazana ga zaman lafiya.

 

Har ila yau muna kira gare ku, ku amince
da tattaunawa idan gwamnati ta nemi yin haka da ku wajen magance ainihin
musabbabin ɓacin ranku.

 

Ta hanyar ɗaukar waɗannan matakai,
gwamnati tana iya magance waɗannan matsaloli da suka yi sanadiyyar
zanga-zangar, da rage zaman ɗar-ɗar da samar da kyakkyawar makoma da kauce wa
dukkan wata tashin-tashina.

 

Muna kira ga shugabanninmu da gwamnatoci
a kowanne mataki su zama masu sauraren koke-koken jama’a, su kuma  mutunta ‘yancin kowanne ɗan ƙasa na bayyana
ra’ayinsa ba tare da wata tsangwama ba, kamar yadda kundin tsarin mulki na
shekarar 1999 ya tanadar.

 

Mun yi imanin cewa idan muka hada ƙarfi,
za mu iya samar da ƙasa da za ta yi wa kowa daɗi, ba tare da wani bambanci na
shekara, ko ƙabila, ko matsayi na zamantakewa da tattalin arziki ba.

 

Muna
godiya.
Sakonmu
ke nan a yau, mune naku

 

 Farfesa Usman Yusuf da  Hajiya Naja’atu Muhammad

Da
Malam Salihu Lukman da kuma Dakta Umar Ardo

 

 

Gwamnan Kano ya gayyaci masu shirya zanga-zanga zuwa gidan gwamnatin jihar

 

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati baza ta lamunta da tashin hankali ba yayin zanga-zangar da ake shirin yi.

Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi ga yan kasuwa, sarakunan gargajiya, da malaman addini a gidan gwamnati da ke Kano a yau ranar Laraba.

Gwamnan dai ya jaddada cewa, zanga-zanga ba ta da wani alfanu . Yayi kira ga masu son yin amfani da yancinsu na yin zanga-zangar da su guji yin barna don kaucewa bata gari da za su yi amfani da su.

Gwamnatin Tinubu ta roki ‘yan Nijeriya da su hakura da zanga-zangar

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, maimakon haka su nemi zama na tattaunawa.

Sakataren ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugabannin kafafen yada labarai a Abuja ranar Laraba.

Akume ya amince da ‘yancin yin zanga-zanga amma ya nuna damuwarsa game da shirin yin zanga-zangar, inda yace batagari zasu iya yin amfani da wannan damar su cimma gurinsu.

Zanga-zanga: Tinubu ya amince da biyan N50,000 duk wata ga matasan yankin Neja Delta

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da biyan N50,000 duk wata ga matasan yankin Neja Delta su 10,000 domin rage wahalhalun da kasar ke ciki.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan kabilu da matasa da mata na yankin Neja Delta a Fatakwal a ranar Talata.

Ya ce za a biya kudin ne a karkashin shirin NDDC Youth Intensive Scheme kuma zai dauki tsawon watanni 12 na farko tare da yiwuwar tsawaitawa.

MTN ya koma aiki bayan ya rufe ofisoshin sa a Nijeriya

Kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya ya koma aiki a duka fadin kasar bayan rufe Ofisoshin sa da yayi a ranar Talata.

Kullewar Ofisoshin nasu na zuwa ne bayan da kwastomomin su sukai masu barna, sakamakon katsewar masu layukan wasu wayoyi na rashin saka Lambobin Shaida na dan kasa.

A ranar Laraba ne kamfanin na MTN ya sanar da komawarsa aiki a shafin sa na X, inda ya tabbatar da cewa shagunan sa za su kasance a bude ga kwastomomi daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana.

Za ayi zabukan kananan hukumomi nan da watanni hudu masu zuwa – Hukumar zaben Kano

 

Hukumar zabe ta jihar Kano tace za ta gudanar da zaben kananan hukumomin jihar ranar  30,ga watan Nuwambar shekarar 2024.

Shugaban hukumar zaben na jihar Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau laraba.

Yace hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zabukan kananan hukumomi da kansiloli,kuma tuni shirye shirye sunyi nisa domin kuma tuni suka aikawa jam’iyyu da ranar da zasu fara sayar da fama famai domin da kuma ranar da zasu maidoshi domin cigaba da tantance ‘yan takarkaru.

Gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamitin aiwatar da mafi karancin albashi

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin ba da shawara kan sabon mafi karancin albashi, biyo bayan amincewar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na sabon mafi karancin albashi na N70,000.

Kaddamarwar ta gudana ne a gidan gwamnatin jihar, wanda mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranta a madadin gwamnan.  

Kafa kwamitin ya zo ne sa’o’i 48 kacal bayan amincewar shugaban kasa. Jihar Kano dai ta zama jiha ta farko a Nijeriya da ta kafa irin wannan kwamiti.

Gwamnatin jihar Yobe ta rufe makarantun Firamare da Sakadiren jihar

Gwamnatin jihar Yobe ta rufe makarantun Firamare da Sakadiren jihar

Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da rufe dukkan makarantun Firamare da Sakandare a jihar gabanin zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan ranar 1 ga watan Agustan 2024.

Ma’aikatar ilimi ta jihar ce ta bayyana hakan a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun daraktan kula da makarantu, na jihar Bukar M Modu.

Daily Trust ta ruwaito cewa za a rufe makarantu a jihar a ranar Laraba 31 ga watan Yuli, 2024 dama ranar juma’a 2 ga watan Agusta 2024 za a kammala zangon karatu a makarantun  gwamnati da masu zaman kansu.

Takardar ta ce matakin ya zama dole bisa la’akari da shirin gudanar da zanga-zangar a fadin kasar, inda ta kara da cewa makarantun za su koma harkokin su a ranar 15 ga Satumba, 2024.

Da aka tuntubi kwamishinan ma’aikatar ilimi na jihar Farfesa Abba Idriss Adam, ya tabbatar wa Daily Trust faruwar lamarin.

Ya ce, ‘’mun san za ai zanga-zanga amma bamu san me zatazo dashi ba,dama anzo karshen zangon karatu wanda za’a gama a ranar juma’a, 2 ga Agusta, 2024, don haka mun yanke shawarar rufe makarantun daga ranar Laraba, 31 ga Yuli, 2024 don kare dalibai

“Ko da yake muna da kyakkyawan fata, za mu sami kwanciyar hankali kuma za mu ji daɗi idan waɗannan zanga-zangar ta faru lokacin da waɗannan ɗaliban suke tare da iyayensu a gida.

Ndume ya ki amincewa da sabon ofishin da aka bashi a majalisar dattawa

Ndume ya ki amincewa da sabon ofishin da aka bashi a majalisar dattawa

Sanata mai wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattawan Nijeriya, Mohammed Ali Ndume, ya yi watsi da sabon ofishin da kwamitin ayyuka na majalisar dattawa ya bashi.

Ndume, a wata wasika da ya aike wa shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa a ranar Talatar nan, ya ce ofishin da aka ba shi bai nuna girmansa da matsayinsa a majalisar dattawa ba.

Wasikar mai dauke da sa hannun babban sakataren sa,Yati Shuaibu Gawu, ta ce: “An umurce ni da in sanar da ku cewa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ki amincewa da ofishin da aka bashi mai lamba 3.10 da kwamitin ayyuka ya yi.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne aka tube Ndume daga mukaminsa na babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, biyo bayan sukar da ya yi wa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu.