DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 411

Kananan hukumomi 8 na jihar Yobe na fuskantar barazanar ambaliya ruwa – NEMA

Kananan hukumomi 8 na jihar Yobe na fuskantar barazanar ambaliya ruwa – NEMA

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta ce rahoton ambaliyar ruwa na shekara ta 2024, AFO, ya bayyana Yobe a matsayin daya daga cikin jihohi 31 da ke da hadarin ambaliya ruwa.

Zubaida Umar, Darakta janar ta NEMA, ta bayyana haka ne a wajen bikin kaddamar da ingantacciyar hanyar kawar da ambaliya na shekarar 2024 a ranar Talatar nan a Damaturu, Yobe.

Zubaida Umar wanda mataimakin daraktan kudi na hukumar ta NEMA, Aminu Ringim ya wakilta, ta kara da cewa hukumar kula da ruwan ta Nijeriya, NIHSA, ta yi hasashen cewa kananan hukumomi takwas a jihar na fuskantar hadarin ambaliya ruwa.

Ta lissafa kananan hukumomin da suka hada da Bade, Jakusko, Yunusari, Gulani, Geidam, Potiskum, Borsari da Karasuwa.

Yace”mun yaba da matakan da gwamnatin jihar Yobe take dauka dan kaucewa ambaliyar ruwa musamman a wannan lokaci”.

A nasa bangaren ko’odinetan hukumar a shiyyar arewa maso gabas, Garba Sirajo, ya yi kira ga jama’a da su guji dabi’ar zubar da shara, musamman yadda ake zubar da shara a magudanar ruwa bar kata hakan na kara toshe hanyoyin da ruwa ke bi.

Gwamnan Kano ya mika sunan karin kwamishina ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa

Gwamnan Kano ya mika sunan karin kwamishina ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya mika karin mukamin kwamishina ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

kakakin majalisar, Alhaji Jibrin Falgore, ya karanta wasikar da gwamnan ya aike wa majalisar yayin zaman ta a talatar nan.

Ya ce wanda aka nada shi ne Muhammad Inuwa-Idris, Manjo-janar mai ritaya.Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce tantancewa tare da tabbatar da wanda aka mika sunan nasa zai kawo ci gaban jihar baki daya.

Yace wanda aka nada zai taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da wasu manufofi da shirye-shiryenta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Daga nan sai shugaban majalisar ya bukaci wanda aka zaba ya bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba domin tantancewa.

Kamfanin MTN ya sanar da rufe Ofisoshin shi a fadin Nijeriya

Kamfanin MTN ya sanar da rufe Ofisoshin shi a fadin Nijeriya 

Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da rufe dukkan ofisoshi da cibiyoyin da yake da su a fadin kasar nan na tsawon sa’o’i 24, daga ranar 30 ga Yuli, 2024.

Wannan yazo ne daidai lokacin da kamfanin yace wasu fusatattu sun fasa musu kayan amfani a Ofishin su sakamakon rufe musu layuka da aka yi saboda rashin rashin cike tsarin NIN.

Sa’o’i kadan bayan faruwar lamarin, kamfanin na MTN ya ce ya rufe ofisoshinsa a fadin kasar a ranar Talatar nan.

MTN, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na X, ya bukaci abokan hulda da abin ya shafa da su yi amfani da tashoshin su na kafofin sadarwa na zamani don nemam taimako.

Kamfanin ya tabbatar wa abokan huldar sa cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan yau da kullum bayan awa 24.

An kama wasu malaman bogi a jami’ar Bayero dake Kano

An kama wasu malaman bogi a jami’ar Bayero dake Kano

Jami’an tsaro na jami’ar Bayero Kano (BUK) sun kama wasu mutane biyu da suke bayyana a matsayin malamai da kuma sayar da littattafai ga daliban a makarantar.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin magatakardan makarantar Bala G. Abdullahi ya fitar ya rabawa manema labarai tace wadanda ake zargin, Mista David Iluebe da Mista Chike E. Eke daga jihohin Edo da Delta, sun shiga wani dakin karatu a Kwalejin Injiniyan ci jami’ar.

Suka gabatar da kansu a matsayin malamai kuma sun gabatar da jerin litattafai guda huɗu da suka shafi batutuwa kamar Ingilishi, Ƙididdiga, Jama’ar Nijeriya da Al’adu-a matsayin wajibi ga dalibai’ wanda zasu zaman musu Continuous Assessment (C.A.).

Rahotanni sun ce sun yi barazanar cewa rashin sayen littattafan zai sa su kasa cin kwasa kwasan da malaman zasu dauke su.

Mukaddashin magatakardar ya bayyana cewa dalibai, sun damu da biyan sossai kuma sun sayi littattafan. Sai dai abin nasu ya janyo surutu, wanda ya kai ga cafke su da jami’an tsaron jami’ar suka yi bayan wani korafi da suka samu. Yanzu haka dai mutanen biyu suna fuskantar tuhuma kan aikata laifuka, damfara, da kuma zamba.

Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun yi ikirarin su ne suka wallafa littattafan da suke sayarwa.

Sun amince da zargin kuma sun bayyana cewa suna yin wannan makirci ne saboda rashin aikin yi, wadanda ake zargin sun kuma bayyana cewa wannan shi ne yunkurinsu na biyu a jihar Kano, inda a baya suka yi aiki a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kano a farkon wannan shekarar.

Gwamnatin tarayya za ta fara sayar da shinkafa 50kg akan kudi N40,000

Gwamnatin tarayya za ta fara sayar da shinkafa  50kg akan kudi N40,000

A ranar Litininin ne gwamnatin tarayya ta sanar da raba karin motoci 10 cike da buhunan shinkafa 50kg ga kowace jiha. Wadannan buhuhuna za a siye su ne a wasu wurare na usamman akan Naira 40,000 kowanne.

A yayin taron majalisar, Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma na kasa Mohammed Idris, ya yi wa manema labarai karin haske kan shirin gwamnatin na rage radadin talauci da kuma yaki da tsadar rayuwa a kasar.

Majalisar zartaswa ta tarayya ta bayyana cewa, mafi yawan bukatun da masu zanga-zangar suka gabatar, tuni gwamnati ta biya su.

Don haka,yin zanga-zangar ba lallai ba ne, saboda gwamnati na aiki tuƙuru kan magance kalubalen da ake fuskanta.

Yace shugaban kasa ya ji damuwar wadanda ke shirya zanga-zangar kuma tuni ya fara daukar matakai a, domin  gwamnati na kokarin tabbatar da wadatar abinci.

“A taron majalisar da ya gabata mun sanar da raba tireloli 20 na shinkafa ga gwamnonin jihohi ga masu bukata musamman marasa galihu a cikin al’umma”.

Idris ya bayyana cewa an kai shinkafar cibiyoyi daban-daban a fadin jihohin kasar nan, inda za a iya siyan ta kan Naira 40,000 kan kowacce buhu.

Wasu daga cikin Ministocin Bazoum Mohammed sun samu ‘yanci daga gwamnatin Tiani

Kotu a birnin Yamai ta saki hudu daga cikin ministocin gwamnatin hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum

Ministocin da aka sakin sun hada tsohon ministan makamashi malan Ibrahim Yacouba, sai tsohon ministan kudi Mohamed Djidoud, sai kuma tsohon ministan fasali Dr Rabiou Abdou sai a karshe tsohon ministan cikin gida Hama Adamou Souley.

Daman dai an kama wadannan ministoci ne da sauren wasu mukarabban tsohuwar gwamnatin ta hambararren shugaban kasar tun washe garin juyin mulkin sakamakon zargin su da furta kalaman cin amanar kasa da yi mata zagon kasa

A yanzu dai ko baya ga hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, sauren manya manyan mukarabban nashi da ake cigaba da rike wa sun hada da tsohon ministan man fetur wato Mahaman Sani Mahadou da aka fi sani da suna Abba, da shugaban jam’iyyar PNDS Tarayya na kasa Malan Foumakoye Gado, akwai kuma tsohon dan majalisar dokoki kuma tsohon ministan tsaro a tsohuwar gwamnatin shugaba Issoufou Mahamadou wato malan Kalla Moutari da kuma tsohon ministan ilimi shi ma a lokacin gwamnatin Issoufo Daouda Mamadou Martai da sauran su.

Sakin wadannan tsoffin ministoci na hambararriyar gwamnatin ta Bazoum na zuwa ne kwanaki uku da cikar sojoji shekara guda akan karagar mulkin kasar.

Sojojin Najeriya sun kafa wani shinge da ya haifar da dogon layin motoci kafin shiga Abuja

Sojojin Najeriya sun kafa wani katafaren shigen binciken ababen hawa da ya haifar da dogon layi na wajen kilomita 12 kafin shiga Abuja babban birnin Nijeriya.

A daidai barikin soja na Marigayi janar Sani Abacha sojojin suka kafa wannan shinge suna binciken ababen hawa da ke ƙoƙarin shiga Abuja.

Ma’aikata da ‘yan kasuwa da ke rayuwa a wajen birnin na Abuja bayan share awanni suna tsaye wuri guda kan hanyar suka hakura suka koma gidajen su.

Lamarin na faruwa ne kwanaki uku kafin ranar da aka sanya za’a yi zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya.

Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa ta barke a jihar Neja

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa wasu matasa sun bazama kan titunan jihar Neja domin nuna adawa da matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya.

Matasan dai suna ɗauke ne da kwalaye da aka rubuta sakonni daban-daban wadanda ke cewa ” ya isa haka, dole a dakatar da tsare-tsare masu musguna wa talakawa, ba za mu zama bayi a ƙasar mu ba, dole a mayar da tallafin man fetur”

Bayan kasancewar su ɗauke kwalayen masu rubuce-rubuce, matasan suna kuma wake-wake da ke nuna adawa da gwamnati.

Wannan na zuwa ne mako guda bayan da gwamnan jihar ta Niger Mohammed Bago ya yi alkawarin baiwa ma’aikata ƙarin Naira dubu 20 baya ga albsahin su dan rage radadain tsadar rayuwa, ya kuma bayar da umurnin a fitar da tan 500,000 na abinci domin saida shi ga jama’a a farashi mai rabuwa a jihar.

Ku ankare, kada ku kusanci wuraren zanga-zanga a Najeriya – saƙon Amurka da Birtaniya da Canada ga ‘yan ƙasashen su

Gwamnatocin Amurka, Birtaniya da Canada suna ankarar da ‘yan kasashen da su yi taka tsantsan kan zanga-zangar da ake shirin yi ranar ɗaya ga watan Agusta a Najeriya.

Gwamnatocin kasashen uku a wasiku da suka aike ga ‘yan ƙasashe masu da ke nan Najeriya sun shawarce su da kada su bari yamutsi ya ritsa da su a yayin da wataƙila rikici zai barke tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga kamar yadda ya faru a baya.
Wannan gargadi na zuwa ne a daidai lokacin da yan kasuwa a manyan biranen Nijeriya ciki har da Abuja suka bukaci tsaurara tsaro a kan dukiyoyin su a yayin wannan zanga-zanga da ya rage ƙasa da awanni 72 ake tunanin za a fara ta.

Gwamna Kano ya nada Sabbinn shugabanin hukumar gudanarwa na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars

Gwamna Kano ya nada Sabbinn shugabanin hukumar gudanarwa na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars

Gwamnan jihar Kano,Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada sabuwar hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars.

Nadin na zuwa ne bayan rusa kwamitin gudanarwa na kungiyar kwallon kafar a kwanakin  baya.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa,da ya rabawa manema labarai a ranar lahadi.

A cewar sanarwar an zabo sabbin mambobin hukumar cikin tsanaki don kwarewa da gogewar su kuma za su yi aiki na wucin gadi na shekara guda, tare da yuwuwar sabunta su bisa la’akari da kwazon kungiyar a kaka mai zuwa.

SolaceBase ta ruwaito cewa sabuwar hukumar ta kunshi Ali Muhammad Umar (Nayara Mai Samba) – Shugaban, Salisu Kosawa – Honorary Member, Yusuf Danladi (Andy Cole) – Member, Nasiru Bello – Member, Muhammad Ibrahim (Hassan West) – Member, Muhammad Usman – Member, Muhammad Danjuma Gwarzo – Member, Mustapha Usman Darma – Member, Umar Dankura – Member

Sanarwar ta ce sauran sun hada da Ahmad Musbahu – Memba, Rabiu Abdullahi – Memba, Abubakar Isah Dandago Yamalash – Daraktan yada labarai, Ismail Abba Tangalash – mataimakin daraktan yada labarai da Engr. Usman Kofar Naisa as Member.

Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwar cewa wadannan mutane za su yi aiki tare da gogewa da za ta taimaka wajen tafiyar da harkokin kungiyar ta Kano Pillars FC.

Ana sa ran sabuwar hukumar gudanarwar za ta yi aiki kafada da kafada da ma’aikatar matasa da wasanni ta jiha da sauran masu ruwa da tsaki a harkar wasanni domin bunkasa kungiyar Kano Pillars.