DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 412

Wike ya ba da sharudda ga masu shirin yin zanga-zanga a Abuja

Wike ya ba da sharudda ga masu shirin yin zanga-zanga a Abuja

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana sharudda ga wasu ‘yan Nijeriya da ke son yin amfani da dandalin Eagle Square domin gudanar da zanga-zanga a ranar 1 ga watan Agusta a fadin kasar.

Wike ya bayar da sharuddan ne yayin wani taro na masu ruwa da tsaki da aka yi a Abuja ranar Asabar, domin hana mazauna babban birnin tarayya shiga zanga-zangar da za’ayi a fadin kasar.

Ya bayyana cewa taron ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki a babban birnin tarayya Abuja su amince da bukatar zaman lafiya, wanda ba za a iya tabbatar da shi ba, idan mazauna yankin suka shiga zanga-zangar.

Yace wadanda suke son yin zanga-zangar, sun nemi ya basu filin Eagle Square domin su gudanar a wajen.

Wike ya ce dole ne sai sun rubuta wasika gareshi,kuma yasan su wanene zasu yi sannan kwana nawa zasu dauka kafin su gama.

“Amma ba’asan ko su wanene ba sedai kawai a jisu a kafafen yada labarai suna bayyana zasu yi zanga-zanga,”ba kawai mun hana su bane   dole ne su cika sharuddan”

Ya kara da cewa “ba ina cewa kada mutane su yi zanga-zanga ba,babban birnin tarayya Abuja wuri ne na zaman lafiya da ya hada al’umomi da dama,don haka baza mu bari a yi tashe-tashen hankula a cikin rigar zanga-zanga ba.

Hukumar NDLEA ta kama wata mata dake kai wa ‘yan bindiga alburusai

Hukumar NDLEA ta kama wata mata dake kai wa ‘yan bindiga alburusai

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da ke sintiri a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya sun cafke wata mata mai suna Ubaida Aliyu mai shekaru 32 dauke da harsashi 573 .

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labaran hukumar Femi Babafemi, da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta ce ta bisa bincike da akayi matar ta bayyana cewa tana kai alburusan ne  ga ‘yan bindiga a jihar Sakkwato.

A cewar sanarwar, an hukumar ta kuma kama wani mutum mai suna Godwin Udochukwu, mai shekaru 35, da laifin shigo da wasu allurai masu illa ga rayuwar al’umma a kan hanyar ta Kaduna zuwa Zariya.

Hakazalika, an kama wani wanda ake zargi mai suna Alkasim Mikailu, mai shekaru 35 a Kano, a wani samame da aka kai masa biyo bayan kama wani ampoules na allurar Diazepam guda 37,880 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Hukumar ta yi kira ga sauran al’umma da su cigaba da sanya ido tare da sanar da hukumar bayanai da zarar sunga wani abu da yayi kama da wannan

An kama ma’auratan da suka sayi jariri, har sun shirya bikin rada masa suna

An kama ma’auratan da suka sayi jariri, har sun shirya bikin rada masa suna

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ceto wani jariri dan watanni biyu daga hannun wasu ma’aurata, Mista James da Uwam, a yayin bikin radin sunan yaron a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin,ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce ma’auratan sun biya Naira miliyan 2,350,000 don siyan jaririn daga hannun wani da ake zargin mai fataucin yara mai suna Loretta Nelson, wanda ya sayi jaririn a hannun wani Fasto mai suna Peter Udoh a kan N1. 450,000.

Hundeyin ya ce Udoh ya sayi jaririn ne a kan Naira 500,000 daga hannun wata mai suna Gloria Sunday da ake zargi da satar jaririn a ranar 11 ga watan Yulin 2024, lamarin da ya sa mahaifiyar jaririn ta kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.

Bayan rahoton, Hundeyin ya ce ‘yan sandan sun yi bincike, wanda ya kai su ga cafke wasu da ake zargi da aikata laifin da jami’an ‘yan sanda da ke sashin Oko Oba suka kama.

Ya ce, Jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin kama Gloria Sunday wadda a lokacin da ake yi mata tambayoyi ta ce ta sayar da jaririn a kan N500,000 ga wani Fasto Peter Udoh.

Fasto Udoh, wanda daga baya aka kama shi a garin Ikene, jihar Ogun, ya amince ya sayar da jaririn kan kudi N1,450,000 ga wata Loretta Nelson da aka kama a Festac Town, Legas.

Hundeyin ya ce, Nelson ya amsa cewa ya sayar da jaririn ne a kan Naira 2,350,000 ga wani Mista da Mrs. James Uwam da aka kama yayin bikin nadin yaron da aka sace.

Wani gini ya rufta da wasu leburori a jihar Jigawa

Wani gini ya rufta da wasu leburori a jihar Jigawa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu leburori uku a wani gini da ya rufta a karamar hukumar Taura ta jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse.

Yace ‘yan sanda sun samu labarin lamarin da misalin karfe 10 na safe lokacin da abin ya faru a ranar Asabar a garin Gujungu da ke karamar hukumar Taura.

Ya bayyana cewa da samun rahoton, tawagar ‘yan sanda ta garzaya wurin da lamarin ya faru,da isar tawagar ta gano cewa wani gini ne mai hawa biyu da ake ginawa ya ruguje.

Ya kara da cewa, a sakamakon lamarin, mutane uku ne suka mutu a nan take, yayin da wasu hudu suka samu raunuka daban-daban.

A cewarsa wadanda suka rasa rayukansu a lamarin sun hada da,Nafi’u Mohd mai shekaru 28, mazaunin unguwar Rijiyar Zaki a karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano, Abdurrahman Ibrahim mai shekaru 60 da Usaman Lawan Muhammad mai shekaru 62, dukkansu mazauna kauyen Danmadai da ke karamar hukumar Gagarawa ta Jigawa.

Ya kara da cewa duka gawarwakin da wadanda suka jikkata an garzaya da su babban asibitin Jahun domin duba lafiyarsu da kuma duba lafiyarsu, yayin da bincike na farko ya nuna cewa wadanda abin ya shafa leburori ne da ke aikin ginin.

Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin tsaurara matakan tsaro a iyakoki kasar kan zanga-zangar da aka shirya

Gwamnatin Nijeriya ta ba da umarnin tsaurara matakan tsaro a iyakoki kasar kan zanga-zangar da aka shirya

Gwamnatin tarayya ta bayar da umurnin tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar sakamakon zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki a da tsadar rayuwa a Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar shige da fice ta kasa (NIS) KT Udo ya fitar, ya ce kwanturola janar na hukumar ya bayar da wannan umurnin.

Yace shugaban hukumar shige da fice ta kasa, KN Nandap pcc, mms, fsm, ya umurci shugabannin hukumar na Shiyyoyi da Kwanturololi na Jihohi da sauran jami’an na hukumar kula da shige da fice ta kasa da ke fadin kasar nan da su yi taka-tsan-tsan tare da kara sanya ido sossai a ayyukan su. 

Shugaban ya kuma umurci dukkan jami’an kan iyaka da su tabbatar da cewa dukkan su sun yi aiki tukuru don hana wasu ‘yan kasashen waje shigowa kasar saboda wata muguwar manufa.

Ya ce yakamata jami’ansu suyi aiki cikin gogewa da kwarewa a yayin wannan aikin domin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ba.

Jigawa ta yi hadin gwiwa da gidauniyar Alfurqan dake Saudi Arabiya don bunkasa tsarin ilimin tsangaya da Alkur’ani

 Jigawa ta yi hadin gwiwa da gidauniyar Alfurqan dake Saudi Arabiya don bunkasa tsarin ilimin tsangaya da Alkur’ani

An bayyana hakan ne a lokacin da tawagar gidauniyar karkashin jagorancin shugabanta Sheikh Abdalla Ibn Nasir Al-Utaibiy ta kai ziyara ga gwamna Umar Namadi a ranar juma’a a gidan gwamnati dake Dutse.

Mai magana da yawun gwamnan, Hamisu Mohammad Gumel ne ya  bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Ya ce Sheikh Al-Utaibiy ya nuna jin dadinsa ga kokarin Gwamna Namadi na bunkasa ilimin kur’ani a jihar Jigawa, yana mai jaddada cewa gidauniyar Alfurqan mai hedikwatarta da ke Ta’if kasar Saudiyya ta sadaukar da kanta wajen tallafa wa alkur’ani, karatu da haddar annic sama da shekaru 50.

Ziyarar a cewar Sheikh Al-Utaibiy da nufin kulla alaka da gwamnatin jihar Jigawa domin inganta hanyoyin koyar da kur’ani ta hanyar samar da dabaru na zamani domin saukaka fahimta da haddace cikin gaggawa, tare da jaddada kwarewar gidauniyar kan hanyoyin koyarwa, wanda ke taimaka wa kurame da yara kanana wajen haddar Alkur’ani.

Gwamna Namadi ya bayyana jin dadinsa da wannan ziyara da kuma alakar da ake kullawa,yace “muna farin ciki da wannan ziyara da kuma kokarin da kuke yi na tallafa mana wajen bunkasa ilimin Alkur’ani, kasancewar ku a nan yana nuna cewa manufarmu daya itace Alkur’ani.

Gwamnan ya godewa gidauniyar bisa kyakkyawar kulawar da tawagar jihar Jigawa ta yi a ziyarar da suka kai garin Ta’if a shekarar da ta gabata.

“Muna matukar godiya da irin karamcin da aka nuna wa tawagarmu a ziyarar da suka kai Ta’if a bara. Irin wannan karamci yana karfafa dankon zumuncin mu da share fagen samun hadin kai mai amfani,”

Daga nan sai gwamnan ya jaddada mahimmancin Alkur’ani a rayuwar al’ummar Jihar Jigawa,yace idan aka yi la’akari da cewa kusan kashi 99% na al’ummarmu musulmi ne, koyarwa da yada koyarwar Alkur’ani mai girma na da matukar muhimmanci, domin ta hanyar wannan littafi ne mutanenmu suke samun shiriya da karfi.

Yace don haka gwamnatin jihar jigawa a shirye take da tayi duk mai yuwuwa wajen kyautata alakar dake tsakani.

Kungiyar ‘yan kasuwar kano ta kafa kwamitoci domin samar da tsaro ga kasuwanni a yayin gudanar da zanga-zanga

Kungiyar ‘yan kasuwar kano ta kafa kwamitoci domin samar da tsaro ga kasuwanni a yayin gudanar da zanga-zanga

Kungiyar ‘yan kasuwar Kano ta kafa rundunoni domin samar da tsaro a fadin kasuwanni da wuraren kasuwanci a yayin zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar nan.

Shugaban ‘yan kasuwar Kanon Alhaji Sabi’u Bako,ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani taron gaggawa da wakilan manyan kasuwanni da manyan kantuna na jihar suka gudanar, ya bayyana bukatar daukar kwararan matakai na dakile satar dukiyar jama’a a yayin zanga-zangar.

A yayin taron, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa, Alhaji Bature Abdul Aziz ya kaddamar da kwamitin mutane 20 domin daidaita ayyukan kungiyar ‘yan kasuwar

A nasa bangaren, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Balarabe Tatari, ya bukaci matasa da su daina yin ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Balarabe Tatari ya ce rahotannin da ke yawo na nuni da cewa za a gudanar da zanga-zangar cikin lumana, duk da cewa ya zama wajibi su samar da isassun matakan kare Kano a matsayin cibiyar kasuwanci.

Shugaban ya yi ga matasa da su sanya a ransu cewa Kano ce gidansu kuma kar suyi duk wani yunkuri na tada tarzoma.

SolaceBase ta ruwaito cewa Kano cibiyar kasuwanci ce a yankin arewacin Nijeriya, kuma a halin yanzu tana da manyan kasuwanni 8, da kuma shaguna da ke a wurare masu mahimmanci a cikin birni mai kusan mutane miliyan 20.

Ba zan iya kwatanta farin cikin da nake ciki ba-dan wasa Endrick

Ba zan iya kwatanta farin cikin da nake ciki ba-dan wasa Endrick

Sabon dan wasan kungiyar kwallon kafa na Real Madrid Endrick ya bayyana cewa yana cike da farin ciki tin bayan da kungiyar ta gabatar dashi a gaban magoya bayan ta.

Yace dama “koyaushe ina son kasancewa a nan kuma in buga wa Real Madrid wasa,wannan mafarki ne tun ina yaro”.

Yau burina ya cika dan haka ina farin cikin,kuma ina tabbatar da cewa zan buga wasa don samun nassarar kungiyata ta Real Madrid.

Majalisar wakilai za tai binciken kan abinda ke tsakanin matatar man Dangote da hukuma kula da man fetur ta Nijeriya

Majalisar wakilai za tai binciken kan abinda ke tsakanin matatar man Dangote da hukuma kula da man fetur ta Nijeriya

Majalisar takilai ta ce za ta binciki cece-ku-cen da ke faruwa tsakanin matatar mai ta Dangote da hukumar hula da man fetur ta Nijeriya (NMDPRA).

Haka kuma binciken zai hada da hukumar kula da man fetur ta Nijeriya (NUPRC) da Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL).

Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilai, Philip Agbese ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa binciken na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar karancin mai a fadin kasar da kuma zargin cewa man Dangote ba shi da inganci.

Agbese ya ce binciken ya yi daidai da kudurin majalisar na kare dukkan kadarorin kasa da muhimman ababen more rayuwa na tattalin arziki kamar matatar man Dangote.

Ya ce: “Mun dade muna gani ta hanyar yin kamfen don bata sunan matatar man Dangote da kuma la’akari da mummunan tasirin da hakan ya haifar da firgici a kasar.

Yace abin takaici, abin da muka gani shi ne, NNPC da NMDPRA na taka rawar gani sosai a cikin wadannan makirce-makircen don bata sunan matatar, wanda kuma ba za a amince da shi ba.

Ta akwatin zabe ya kamata ‘yan Nijeriya su nuna fushinsu ba ta hanyar zanga-zanga ba – Kwankwaso

 Ta akwatin zabe ya kamata ‘yan Nijeriya su nuna fushinsu ba ta hanyar zanga-zanga ba – Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar (NNPP) na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su nemi sauyi ta hanyar dimokradiyya maimakon zanga-zanga.

A wata sanarwa da ya sanyawa hannu,Sanata Kwankwaso ya jaddada cewa za a iya samun sauyi mai inganci kuma mai dorewa ta hanyar karfin yin zabe.

Yace mun tsinci kanmu cikin wahalhalun da ba za a iya misaltawa ba saboda shugabanninmu sun rasa wasu abubuwa.

“Duk da haka, a ko da yaushe akwai damar yin gyara da dora kasar nan kan turba mai kyau don bunkasar tattalin arziki, wadata, da kyautata jin dadin ‘yan kasa.

Kwankwaso ya bayyana wasu rigingimu da suka samo asali daga rashin shugabanci na gari, kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi katsalandan a harkokin masarautun jihar Kano, da tsige mataimakin gwamnan jihar Edo, da rudanin siyasa a jihar Ribas, da rashin tsaro.

Ya kara da cewa wadannan al’amura alamu ne na rashin bin ka’ida da kuma nuna gaskiya ga Shugabanin a Nijeriya.

Ya yi kira ga shugabannin Nijeriya a dukkan matakai da su gaggauta magance wadannan kalubale ta hanyar tabbatar da kyakkyawan shugabanci da bin doka da oda.