DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 413

Shinkafar da gwamnatin tarayya ta ba Minista Dangiwa na nan, babu wanda ya karkatar da ita – Makusancinsa

Wani makusancin ministan gidaje a Nijeriya Arch Ahmad Musa Dangiwa ya sanar cewa babu kanshin gaskiya a zargin da ake yi cewa shinkafar da jami’an DSS suka sanar da kamawa a Katsina, ta ministan ce da gwamnatin tarayya ta bashi a rarraba a jihar Katsina.
Salisu Hamza Rimaye a cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina ya ce an jawo hankalinsu akan wani rahoto da ake zargin karkatar da kayan abinci da Gwamnatin tarayya ta bayar da nufin rabawa a jihar Katsina daga wajen Minista Dangiwa.
Rahoton ya yi ikirari cewa wani na kusa da ministan gidaje da raya birane Arc. Ahmed Musa Dangiwa ne ya karkatar da wannan kayan abinci.
Salisu Hamza ya sanar cewa babu kamshin gaskiya a kan wadannan zarge-zargen. Wannan ikirari rashin fahimta ne kawai daga wadanda su ka bayar da rahoton. 
Ya kara da cewa Minista, Dangiwa wanda ya yi fice wajen taimakon jama’a, yana da tarihin rikon amana da karimci. 
“Sama da shekaru goma yana raba wa al’umma daruruwan ton-ton na kayan abinci musamman a lokutan azumin Ramadan da sauran lokutan bukukuwan sallah da makamantansu”. In ji shi.
Ya ci gaba yana cewa malaman addini, shugabannin jam’iyya, da marasa galihu da sauran al’umma duk sun kasance masu amfana da ire, iren wadannan kayakin abinci da Ministan yake rabawa duk shekara.
Makusancin ministan ya ce wadannan zarge-zargen da ba su da tushe balle makama. Ya kara da cewa illa ce ga kokarin da Ministan ke yi na tallafa ma al’umma.
 
Ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan ikirari maras tushe.
Sannan ya sanar da Jama’a cewa kayaki na nan, nan gaba kadan bayan an gama tsare-tsaren da shirye, shiryen raba su za a kira taro a raba.

Yanzu lokaci ne da zamu magance matsaloli bawai zanga-zanga ba -Kashim Shettima

Yanzu lokaci ne da zamu magance matsaloli bawai zanga-zanga ba -Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima,yanzu lokaci ne da za a magance matsaloli ba wai zanga-zanga ba,ya bayyana hakan ne a yayin wani babban taro a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shettima ya jaddada bukatar daukar kwararan matakai kan zanga-zangar duk da cewa ya amince da wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da aka yi a baya-bayan nan, musamman cire tallafin man fetur.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasar kan kafafen yada labarai Stanley Nkwocha ya fitar.

Yace wannan lokaci ne da ya kamata mu magance matsalolinmu, ba wai yin zanga-zanga ba. Kowa nada ‘yancin gudanar da zanga-zanga a yawan kasashen dimokuradiyya da ake a duniya,amma wasu na kokarin tada zaune tsaye da ba a san inda za a kawo karshensa ba.

“Ina so in yi kira gare ku da ku ba da shawarwari irin na diflomasiyya, haɗin da karin karfin gwiwa, da haƙuri,shugaban mu ya na aiki sossai wajen inganta abubuwa a Nijeriya”

A sanya ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Jigawa

A sanya ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Jigawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Jigawa (JISIEC), ta sanya ranar 5 ga watan Oktoba domin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.

Shugaban hukumar Alhaji Awwal Muhammad ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki, a Dutse babban birnin jihar a ranar Juma’a.

Muhammad ya tabbatar da shirin hukumar na gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomi 27 na jihar.

Yace a baya hukumar ta sanar da dage zaben, daga watan Yunin 2024, zuwa watan Yunin 2025, bayan da aka yi wa dokar zaben jihar kwaskwarima.

Yace duk da haka, suna sane da hukuncin da Kotun Koli ta yanke na baya-bayan nan ta umurci dukkan gwamnatocin jihohi, da su yi zababbun kananan hukumomi a jihohinsu, da gaggawa.

A bisa bin hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, hukumar zaben ta ga ya zama dole ta koma ga hukuncin da ta kotu ta yanke a baya kan zabukan kananan hukumomi, sannan ta bukaci baki daya da a sake gyara dokar zaben jihar, domin ta bi hukuncin kotun koli. , saboda haka ya sanya ranar Asabar 5 ga Oktoba, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gudanar da zaben a jihar Jigawa.

Don haka ya bukaci hukumomin tsaro, shugabannin gargajiya da na addini, jam’iyyun siyasa, kungiyoyi, kungiyoyin mata, shugabannin matasa, kafafen yada labarai da kungiyoyin al’umma da su marawa hukumar baya, domin cimma burin da ake so.

Muhammad, wanda ya jaddada kudirin hukumar na gudanar da sahihin zabe, ya yabawa masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar, a kokarinta na gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci a jihar.

Shugaban hukumar zabe ta kasa INEC yace yanzu zasu iya gudanar da zabukan kananan hukumomi

 Shugaban hukumar zabe ta kasa INEC yace yanzu zasu iya gudanar da zabukan kananan hukumomi

Makonni biyu bayan da kotun koli ta bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu a Nijeriya, Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar zaben na iya samun nasarar gudanar da zabukan kananan hukumomi,idan har aka yi la’akari da yadda doka ta ce.

Shugaban na INEC ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a gaban kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dokoki kan harkokin zabe domin gabatar da kasafin kudin zaben jihar Ondo da Edo a ranar Alhamis.

Yace a halin yanzu dai gwamnatocin jihohi suna shirya zaben kananan hukumomi a yankunansu inda jam’iyyun da ke mulki a jihohin ke samun kujerun shugabannin kananan hukumomi, lamarin da yasa jam’iyyun adawa suka fara kaucewa shiga zabe.

Mahmood ya bayyana cewa, hukumar da a halin yanzu take gudanar da zabukan na kananan hukumomi 62 da ke babban birnin tarayya Abuja,za ta iya gudanar da zaben cikin sauki a fadin kananan hukumomi 774 da aka yi wa kwaskwarima, na wasu tanade-tanaden dokokin zabe.

A ranar 21 ga Satumba, 2024, zaben gwamnan Edo da kuma ranar 16 ga Nuwamba, 2024, zaben gwamnan Ondo, shugaban INEC ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yaba da gagarumin ci gaban da hukumar ta samu.

Ya kuma kara da cewa hukumar ba ta da wata fargaba dangane da kudaden gudanar da zabukan.

Tinubu ya shiga ganawar sirri da gwamnonin APC kan batun zanga-zanga

Tinubu ya shiga ganawar sirri da gwamnonin APC kan batun zanga-zanga 

Shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnonin jam’iyyar APC karkashin kungiyar gwamnonin Progressives Forum a fadar sa da ke Abuja.

Taron wanda aka fara da misalin karfe 1, ya biyo bayan kiraye-kirayen da ake yi na zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki a fadin Nijeriya.

Ko da yake ba a san ajandar taron ba, amma ana iya danganta shi da zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a ranar 1 – 10 ga Agusta.

Zanga-zangar wacce aka shirya a karkashin taken ‘EndBadGovernance’ ta samu karbuwa sosai a shafukan sada zumunta duk da cewa wadanda suka shirya zanga-zangar ba a bayyana sunansu ba,kuma ba babu sunan wata kungiya da ta dauki nauyi a hukumance ba.

Wannan taron ya biyo bayan kammala taron kungiyar gwamnonin Nijeriya da aka yi a daren Larabar da ta gabata, kuma ya biyo bayan soke taron Majalisar Tattalin Arzikin kasa da aka shirya gudanarwa a yammacin ranar Alhamis dinnan.

Wadanda suka hallarci taron sun hada da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, Wale Edun da Abubakar Bagudu.

Gwamnatin tarayya ta kashe dala biliyan $1.5 wajen dakile satar danyen mai – George Akume

 Gwamnatin tarayya ta kashe dala biliyan $1.5 wajen dakile satar danyen mai – George Akume

Gwamnatin tarayya ta kashe sama da dala biliyan 1.5 daga shekarar 2020 zuwa yau domin kare gidajen man kasar da kuma dakile satar danyen mai.

Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), George Akume ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wajen wani taron jin ra’ayin jama’a na majalisar wakilai kan satar danyen mai.

Yace gwamnatin tarayya ta damu da rahoton hukumar kula da masana’antu ta Nijeriya (NEITI) wanda ya nuna sama da dala biliyan 46 da aka sace tsakanin shekarar 2009 zuwa 2020.

Majalisar dai ta kafa wani kwamiti na musamman karkashin jagorancin shugaban kwamitin kula da harkokin man fetur na majalisar, Alhassan Ado Doguwa, domin ya binciki asarar da aka yi a bangaren mai da iskar gas.

Har ila yau, kakakin majalisar Tajudeen Abbas, wanda mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya wakilta, ya ce an yi asarar dala biliyan 10 a cikin watanni bakwai na satar danyen mai, kuma babu wani sihiri da gwamnati za ta iya yi da irin wannan asara.

Matatar man Dangote ba zata fasa aiki ba- Kwankwaso ya fadawa gwamnatin Nijeriya

Matatar man Dangote ba zata fasa aiki ba- Kwankwaso ya fadawa gwamnatin Nijeriya

Dan takarar shugaban kasa a (NNPP) a zaben 2023 kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, ya mayar da martani kan takaddamar da ke tsakanin matatar man Dangote, da masu kula da bangaren mai a Nijeriya.

A makonnin da suka gabata ne dai Dangote da hukumomin a Nijeriya ke takun-saka game da matatar mai da ke yankin Ibeju-Lekki a jihar Legas.

Ya kai wani sabon mataki a lokacin da hukumar kula da man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce har yanzu gwamnati ba ta ba da lasisin fara aiki ba ga matatar man Dangote.

Sai dai a wani mataki na warware matsalolin, karamin ministan albarkatun man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren mai da iskar gas sun gana da Dangote a ranar litinin.

A wani sako ta hanyar X a ranar Laraba, Kwankwaso ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta tabbatar da nasarar aikin matatar man ta Dangote.

Yayin da yake bayyana ra’ayinshi Kwankwaso ya ce dole ne gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta nuna adalci ga irin wannan gagarumin aiki da Dangote ya dauko domin samun nasarar sa.

Yace na yi farin ciki da ziyartar matatar mai ta Dangote, kuma na yi mamakin irin jajircewar da aka yi wajen ganin an kafa ta.

Lokaci ya yi da za mu hada kan wannan kadarorin kasa don ganin cewa babban aikin ba’a samu matsala ba, kuma dole ne gwamnatin Nijeriya ta fahimci hakan ta hanyar nuna gaskiya da kuma amincewa da kudurin Dangote na habbaka tattalin arziki.

Na janye daga takarar shugaban kasa don bawa masu tasowa dama-Jeo Biden

Na janye daga takarar shugaban kasa don bawa masu tasowa dama-Jeo Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana dalilin da ya sa ya ki tsayawa takara a babban zaben kasar dake tafe a watan Nuwamba.

Biden, mai shekaru 81, ya yi aiki a matsayin mataimakin Barack Obama, a lokacin da ya yi wa’adi biyu a matsayin shugaban kasad Amurka.

Kamar Obama da sauran ‘yan jam’iyyar Democrat, Biden ya bi sahun Hillary Clinton a zaben shugaban kasa na 2016 da Shugaba Donald Trump ya lashe.

Shekaru hudu bayan haka, Biden ya doke Trump wanda ke neman sake tsayawa takara. Sannan ya yi shekaru 77,inda ya kafa tarihi a matsayin mutum mafi tsufa da aka zaba.

Duk da haka, shugabancinsa ya yi ta fama da cece-kuce, musamman saboda rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Yayin da yake bayyana matakinsa na yin murabus, Biden ya ce zai ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban kasa da kuma babban kwamandan rundunar har sai wa’adinsa ya kare a watan Janairun 2025.

Da yake magana a wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin a daren Laraba, Biden ya ce ya kawo karshen yakin neman zabensa na sake tsayawa takara a wani yunkuri na ceto demokradiyyar Amurka.

A cewarsa, ya amince da mataimakiyarsa, Kamala Harris, don hada kan ‘yan uwansu na Democrat da kuma kasar baki daya.

Ya ce ina girmama wannan ofishin, amma ina son kasata,shiyasa na yanke shawarar hanya mafi dacewa domin samun nasara.

Gargadin sojojin Nijeriya ga masu zanga-zanga

 

Jan kunne ne mai karfi daga sojojin ga masu yunkurin shirya zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya, inda suka ce duk da dokar kasa ta aminta da a yi zanga-zangar lumana, to amma fa, inda ‘yancin wani ya kare, a nan na wani ya soma, domin kuwa sojojin sun ce ba za su lamunci a tayar da hatsaniya ba.

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta hannun daraktan yada labaranta Maj Gen Edward Buba ce dai ta fitar da wannan gargadi ga masu yunkurin shirya wannan zanga-zangar a wani taron manema labarai a Alhamis din nan a  Abuja.

Maj Gen Edward Buba ya ce sojoji ba za su zura idanu su ga ana neman barnata dukiyar kasa ba da sunan zanga-zanga.


Ya ce wannan gargadi ya zama wajibi saboda  sojojin sun kwakwulo wani shiri daga wadansu bata-gari da ke shirin yin uwa-ma-karbiya ga zanga-zangar, su mayar da ita wani abu daban su je suna farmakar wuraren kasuwancin mutane


Maj Gen Edward Buba ya ce wadansu na son a yi koyi da zanga-zangar da ke faruwa a kasar Kenya, wadda kowa ya gani a kasa cewa ta kazance kuma ta haifar da tashin hankali, a sabili da haka hedikwatar tsraon Nijeriya ba za ta zura ido ta amince wani abu makamancin abin da ke faruwa a Kenya ya zo Nijeriya ba


Jaridar Daily Trust wacce ta ruwaito babban sojan na fadin hakan ta ce ta wasu ‘yan Nijeriya da tsadar rayuwa ta jijjiga sun shirya fantsama kan titi daga ranar daya ga wata mai kamawa na Agusta zuwa 10 ga wata.

Ba mu san me ‘yan Nijeriya zasu yiwa zanga -zanga ba-gwamnonin APC

 Ba mu san me ‘yan Nijeriya zasu yiwa zanga -zanga ba-gwamnonin APC

Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun ce basu san dalilin da yasa ake shirin,shirya zanga-zanga ba a kasar.

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi bayan wani taron na kungiyar gwamnoni Progressives’  Governors Forum (PGF) da aka gudanar a Abuja,in da yace ba mu san masu shirya zanga-zangar me suke shirin yi ba,muna kira da su zo muzauna a tattauna domin samun mafita.

Yace mu a matsayinmu mun himmatu wajen tabbatar da hadin kan kasar nan, mun himmatu ga duk wani abu da zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, ya kawo wadata, samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata wadanda suka kammala karatunsu domin a samar  musu aiki yi.

Gwamnan Uzodimma ya ci gaba da cewa bai dace a halin yanzu kasar nan ta yi wata zanga-zangar da wata kungiya za ta yi ba, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wannan zanga-zangar.

Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi hakuri da gwamnati, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin ganin an daidaita matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a kasar.

 ya kara da cewa: “Muna ganin ba hikima ba ne a halin yanzu duk wata zanga-zangar da wata kungiya ta mutane za ta yi ta kowace irin salo.

Muna amfani da wannan dama don mu shawarci matasan mu maza da mata da su daina tunzura su su haddasa rikici ko hargitsi a kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mutane na yin gangamin shirya zanga-zangar da za a yi a fadin kasar daga ranar 1 ga Agusta zuwa 10 ga Agusta, 2024.