DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 414

Zanga-zanga: Ku dan ba mu lokaci, gwamnatin tarayya ta roki ‘yan Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin cewa za a warware matsalolin da zasu sa a gudanar da zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.

Wasu kungiyoyi da daidaikun jama’a ne zasu gudanar da zanga-zangar a fadin kasar a ranar 1 ga watan Agusta domin kawo karshen tsadar rayuwa a kasar.

Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume a ranar Laraba ya yi wata ganawar sirri da ministoci kan baton.

Da yake jawabi bayan taron, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce babu wanda zai bacci a tsakaninsu har sai an warware matsalolin.

Idris ya ce gwamnati ta kasance tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki da sauran masu shirya zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar.

Gwamna Yusuf yayi kira da a daina sare itatuwa barkatai a Kano

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bukaci shugabannin gargajiya da su dasa akalla bishiya daya a yankinsu domin dakile kalubalen sauyin yanayi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani taron wayar da kan jama’a na kwanaki 2 wanda Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACRESAL), karkashin ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar ta shirya. 

Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta ya yi kira ga al’ummar jihar da su daina sare itatuwa ba tare da maye gurbinsu da wasu ba.

KASSROTA ta gargadi masu sana’o’i a gefen titunan jihar Katsina

Hukumar kiyaye haɗurra ta jihar Katsina KASSROTA ta gargadi masu sana’oin gefen tituna da masu wankin mashina da suke tare ma masu wucewa a ƙasa hanya.

Wannan gargadin ya fitone ta bakin shugaban hukumar, Manjo Garba Yahaya Rimi Rtd, a hedikwatar hukumar dake Katsina.

Garba Yahaya ya kara da cewa “Hukumar tayi kiraye-kiraye a kafafen yada labarai daban-daban na jan hankali ga masu wannan dabi’ar.

“Mukan kama masu kunnen kashi muyi masu tara daidai da yadda dokokin mu su ka tanada”.

Kungiyar daliban Najeriya ta yi kashedin karin kudin makaranta a Ƙasar

Kungiyar daliban Najeriya ta gargadi shugabannin makarantun kasar kan karin kudin makaranta sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na baiwa dalibai rancen kudi.

Wannan gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro na da kungiyar ta fitar a Kano, ranar Laraba wanda Kwamared Okunomo Adewumi ya sakama hannun.

“Duk wata cibiya da aka samu ta kara kudi ba gaira ba dalili, za ta fuskanci fushin Kungiyar dalibai, za mu hada kan mambobinmu tare da daukar kwakkwaran mataki”.

An bukaci kwamitin binciken Hisba a Katsina ya bada rahoto cikin kwana goma

 

Sakataren gwamnatin jihar Katsina Abdullahi Faskari ne ya kaddamar da kwamitin a ranar Talata a madadin mataimakin gwamnan jihar Faruq Jobe a ofishinsa dake cikin sakatariyar jihar Katsina.

Ya ci gaba da cewa ana sa ran kwamitin zai binciki wasu zarge-zargen cin zarafi da azabtarwa da jami’an hukumar ke yi.

Sauran sharuddan kwamitin a cewar Faskari sun hada da: nazarin dokar kafa hukumar da wasu kura-kurai da ake zargin ta da take hakkin dan Adam.

Kwamitin dai zai kasance karkashin jagorancin kwamishinan matasa da wasanni Aliyu Lawal Zakari yayin da babban sakataren ma’aikatar harkokin addini zai kasance mamba.

NLC ta musanta janyewa daga zanga-zangar tsadar rayuwa

Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ta janye daga zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar domin nuna adawa da tsadarrayuwa, wacce aka shirya yi a ranar 1 ga watan Agusta.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero, ya ce kungiyar ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar ba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Ajaero ya sanyawa hannu a ranar Talata mai taken, ‘Kungiyar Kwadago ta Najeriya ba za ta iya janyewa daga zanga-zangar tsadar rayuwaba.

Gwamnatin Bauchi za ta rufe cibiyoyin kiwon lafiya yayin zanga-zangar gama gari

Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana aniyarta na rufe dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a ranar da za a gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a fadin kasarnan.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko na Jihar, Dokta Rilwanu Mohammed yace, an yanke wannan shawarar ne domin barazanar tsaro, kare rayukan ma’aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya.

Ya bayyana hakan ne a wajen bude taron manema labarai na shekara biyu kan dabarun bayar da rahoton hidimomin kula da lafiya a matakin farko da aka gudanar a Bauchi ranar Talata.

Kashim Shettima ya kaddamar da wasu ayyuka a jigawa, ya kuma bukaci matasa su gujewa shiga zanga-zanga

Kashim Shettima ya kaddamar da wasu ayyuka a jigawa, ya kuma bukaci matasa su gujewa shiga zanga-zanga

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ziyarci jihar Jigawa a ranar Talata domin kaddamar da wasu ayyuka da ofishin sa ya jagoranta. A yayin ziyarar tasa, Shettima ya bukaci matasan da su kaurace wa shiga zanga-zanga, inda ya bayyana cewa, ba za ta haifar da ci gaba mai kyau ba, kuma za ta iya haifar da tashin hankali da asarar dukiyoyin jama’a.

Ya jaddada cewa gwamnatin su karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tana aiki tukuru wajen aiwatar da manufofi da shirye-shirye da nufin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma yabawa gwamna Malam Umar Namadi bisa bullo da tsare-tsare masu da zasu inganta rayuwar al’ummar Jigawa.

Gwamna Namadi ya bayyan ziyarar mataimakin shugaban kasar a matsayin wadda tazo da alheri da amfani mai tarin yawa ga al’ummar jihar Jigawa.

Yace mataimakin Shugaban kasa ya kaddamar da asibitocin MSME don inganta harkokin lafiya, kasuwanci da bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu. Ya kuma kaddamar da shirin noman rani mai amfani da hasken rana mai fadin hekta 20,000.

Sauran ayyukan sun hada da kaddamar da samar da wutar lantarki mai ta hasken rana mai karfin KVA 100 domin samar da tsayayyar wutar lantarki ga masu kananan sana’o’i a kasuwannin Dutse, da kaddamar da shirin horas da matasa 1,000 daga jihar Jigawa kan sabuwar fasahar zamani ta Artificial intelligence (AI).

Gwamna Namadi ya ce mun yi farin ciki da cewa wannan ya yi daidai da ajandarmu ta inganta rayuwar al’ummar Jigawa, inda muke shirin aiwatar da tsare-tsare masu inganci don tallafawa da inganta harkokin kasuwanci, sana’o’i, da bunkasa kananan ‘yan kasuwa.

Zanga-zanga ba zata magance kalubalen dake Nijeriya ba– Gwamna Namadi

Zanga-zanga ba zata magance kalubalen dake Nijeriya ba– Gwamna Namadi

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi ranar ya ce zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar a ranar 1 ga watan Agusta, ba ita ce mafita ga kalubalen da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu ba.

Gwamnan ya bayyana hakanne a wani taro da aka yi da kungiyoyi 27 da ya gudana ranar litinin a birnin Dutse.

Namadi yace tabbas Nijeriya na fama da tabarbarewar tattalin arziki da rashin tabbas

Amma, zanga-zangar ba ita ce mafita ba. Akwai hanyoyi da dama da mutane za su iya bayyana kokensu, mutane suna da ‘yancin nuna korafe-korafensu ta hanyar zanga-zangar karkashin mulkin dimokradiyya, amma wannan ba ita ce hanya mafi inganci don magance matsalolin ba.

Yace zanga-zanga kadai ba za ta samar da mafita ba, jama’a su koma ga Allah, su tuba, su nemi gafara da sa hannun Ubangiji kan kalubalen da kasa ke ciki.

Namadi ya ce gwamnati ta yi iyakacin kokarinta ta fuskar samar da kayan abinci da sauran kayayyaki da suka hada da raba kudade domin rage wahalhalun da jama’a suke fuskanta a dukkan matakan gwamnati.

Gwamnan ya kuma tunatar da jama’a cewa a kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta amince da shigo da kayan abinci cikin kasar na tsawon watanni biyar ba tare da harajin shigo da kaya daga kasashen waje ba.

Namadi ya shawarci ‘yan Nijeriya da su yarda da wahalhalu a matsayin jarabawa daga Allah, ya kara da cewa kowane musulmi yasan kaddara ko mai kyau ko mara kyau don haka al’umma su cigaba da addu’ar samun sauki ga kasa.

APC na zawarcin Gwamnan jihar Plateau

Gamayyar kungiyoyin jam’iyyar APC na Arewa ta tsakiyar Nijeriya na zawarcin Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang da ya ajiye jam’iyyarsa ta PDP ya koma jam’iyyar APC.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Saleh Mandung Abdullahi a cikin wata sanarwa da ya aike wa DCL Hausa, ya ce kiran ya zamo wajibi domim burinsu shi ne jam’iyyar APC ta kara bunkasa, amonta ya kai ko’ina.
A cikin wasikar mai taken “gayyatar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa jam’iyyar APC” ta ce a ‘yan kwanakin nan sun gana da masu ruwa da tsaki da jigogin jam’iyyar APC na arewa ta tsakiyar Nijeriya, inda suka bukaci da a sada gwamnan da takardar gayyata, ta ya koma APC.
Hon Saleh Zazzaga ya ce tuni sun fara isar da sakon ga Gwamnan ta hanyar kafafen sadarwa, yanzu kuma sun mika masa wasika a hukumance.
Kungiyar ta ce kiran nasu ga Gwamnan jihar zai ba APC damar sake karbar jihar Plateau bayan da ta rasa ta a zaben shekarar 2023.
Wasikar ta yi nuni da cewa Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwangne tilo daga yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya da ba dan jam’iyyar APC ba, don haka ne suke bukatarsa da ya saje da sauran ‘yan’uwansa.